Ɗan Afirka na farko da ya fara samun lambar zinare a gasar Olympics, ba tare da takalmi a kafarsa ba

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Marta Pausilli & Priya Sippy
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 5
A 1960 da dare a Rome, jikan makiyayi ba takalmi a ƙafarsa ya ja hankalin duniya tare da kafa tarihi a Afirka.
A wannan yammacin, titunan birnin ya cika makil da baƙi suna ta karfafawa 'yan wasan gudu na gasar Olympic.
A gefen titi, sojojin Italiya ne rike da tocila su na haska hanya a daidai lokacin dan dan wasan gudu na kasar Habasha Abebe Bikila ya tasamma isa layin karshe na tseren.
Ga mutane da dama, su na kallon Bikila wanda ke sanye da gajeren wando na yadin siliki da bakar singileti ta 'yan tsere, su na masa kallon zakaran gudun yada kanin wani dan Morocco Rhadi Ben Abdesselem.
kasa da mil daya ya kai karshe, Bikila ya fara yi wa sauran abokan wasansa nisa. Sannu a hankali ya fara dosar layin karshe, ya na daga hannu sama alamar nasara a daidai lokacin da ya karshe.
Ba wai Bikila ya zama na farko a tseren ba, ya kasance na farko a babake 'yan Afirka kuma dan kasar Habasha na farko da ya fara cin kyautar zinare a gasar ta Olympics.
Wannan ce nasarar ce ta sanya ya kasance wanda ya kafa tarihi a duniya na yin gudun yada kanin wani na tsahon sa'a biyu da mintina 15.
Nasara ce da ta girgiza kowa, ba wai kawai dan babu wanda ya san da zaman Bikila ba, a'a saboda ya yi duk wannan tseren ba tare da takalmi a kafarsa ba.
Bikila ya yanke shawarar yin tseren ba tare da takalmi ba, saboda takalmin shi ya lalace, kuma ya na tsoron sabon takalmi ka iya janyo masa ciwon kafa.
“Yawancin zakarun gasa irin wannan kan yi fice da daukaka saboda wata bajinta, amma ga Bikila, ba haka lamarin ya ke ba saboda shi ba kowa ba ne,“ in ji Tim Judah, wani kwararren marubuci da ya wallafa littafi akan Bikila.
“Wannan ne dalilin da ya girgiza mutane da kuma ban mamaki, dan Afirka ya yi nasara a gudun yada kanin wani kuma babu takalmi a kafarsa.”

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dubban mutane ne sukai wa Bikila tarbar ban girma, a lokacin da ya koma gida cike da nasara.
Harwayau, a shekarar 1960 nasarar da ya yi ta yi fice a duniya.
“Wannan ne lokacin da turawa suka fara janyewa daga mulkin mallaka, lokacin da Afirka ta hau matakin fice a duniya,” in ji Judah.
“Abin da hakan ke nufi shi ne, Bikila ya zama tauraro kuma fitilar da ake da kyakkyawan fatan za ta dasa dan ba na alkhairai ga nahiyar.”
Wannan nasara ta Bikila ce ake kan turbarta har kawo yau din nan.
“Idan ka yi nazari za ka lura abubuwan da suka faru na alkhairi ga Afirka na 'yancin kai, sun soma ne bayan nasarar da Abebe Bikila ya yi na zama gwarzon duniya a wasan da Italiya ta karbi bakunci,” in ji tsohon zakaran gudun yada kanin wani shi ma dan kasar Habasha wato, Haile Gebrselassie.
Lokacin da Bikila ya koma kasarsa, wata jaridar kasar Kenya mai suna Nation ta rawaito Sarki Haile Selassie ya bashi kyautar Tauraron kasar Habasha. Ya kuma kara masa girma inda ya zama Kofur, ya bashi rantsattsen gida da sabuwar mota kirar kirar Beetle.
Mafarin daukaka
Tarbiyyar da aka dora Bikila akai, ba wai ta tsaya kan nasarar gasar Olympic ba ne kadai.
A shekarar 1932 aka haife shi a kauyen Jato, mahaifinsa makiyayi ne. A lokacin da ya na matashi ya koma birnin Addis Ababa inda ya shiga aikin dan doka har ta kai shiga nausawa fadar masu mulkin kasa, da tafiya ta mika ya samu damar zama mai kula da lafiyar sarki Haile Selassie.
Anan ne mai horas da 'yan wasan tsere dan kasar Sweden Onni Niskanen, wanda gwamnatin Habasha ta dauko domin horas da sojinta ya yi tozali da Bikila.
Niskanen bai bata lokaci ba, ya fara bai wa Bikila horo na musamman domin ya yi nasara a gasar.
Ko da ya ke, Bikila ba shi ake yi wa kallon zakakurin dan wasan tsere ba, sakamakon a lokacin akwai wani mai suna Wami Biratu da ya yi farin jini a wasannin da aka yi a kasar Italiya, kwanaki kalilan gabannin tafiya gasar ta Olympics Biratu ya wayi gari ba shi da lafiya, dole aka cire shi daga jerin masu tafiya Roma.

Asalin hoton, Getty Images
Lambar zinare ta biyu a gasar Olympic
An sake ganin hazakar Bikila a shekarar 1964, lokacin da birnin Tokyo ya karbi bakuncin gasar Olympic,inda ya kare kambinsa ya zama wanda ya kare lambar zinarensa a karo na biyu a jere.
Har kawo yau Bikila ne daya daga cikin 'yan wasan gudu su uku da sukai fice, wato
Waldemar Cierpinski da Eliud Kipchoge. Amma a wannan karon Bikila sanye da takalmi ya kai banten shi.
Kwanaki 40 gabannin gasar aka yi wa Bkila tiyatar gaggawa aka cire masa kabar ciki.
Duk da hakan, Bikila ya shayar da mutane mamaki a titin Tokyon Japan, yadda ya falfala gudu, da wuce tsararrakinsa tamkar walkiya, sai da ya sake kafa tarihin tseren sa'a 2 da minti 12.

Asalin hoton, Getty Images
Kalubalen da ya Fuskanta
A watan Maris din1969, rahotanni sun bayyana cewa Bikila ya yi hatsari a cikin motarsa Bettle, wanda hakan ya janyo masa shanyewar barin jiki tun daga wuyansa har kafafu.
An garzaya da shi wani asibiti mai suna Stoke Mandeville da ke Birtaniya, sai dai abu mafi tashin hankali shi ne ba zai kara tsayawa da kafafunsa bare ya yi wasan gudu ba.
Amma duk da hakan, Bikila bai karaya ba sakamakon samun nasarar amfani da hannayensa, daga nan ya koma wasan kwallon tebur da na harbi.

Asalin hoton, Getty Images
Kafa tarihi har abada
A shekarar 1973, Allah ya yi wa Bikila rasuwa ya na da shekara 41, sakamakon matsalolin da ya samu lokacin da ya yi hatsarin mota.
Sarki Haile Selassie ya ayyana makokin kwana guda, an kuma yi wa Bikila jana'izar ban girma ta kasa.
Duk da mutuwar kuruciyar da ya yi, tarihin da ya kafa a gudun yada kanin wani ya ci gaba da zama abin ba da labari ga 'yan baya.
Bikila ya zama abin kwaikwayo a kasar Habasha. An gina katafaren filin wasa mai suna Abebe Bikila a birnin Addis Ababa, makarantu da dama sun gudanar da gasa da lambobin yabo domin tunawa da shi.
Ywancin 'yan wasan gudu na Habasha da Kenya sun zama abin kwatance saboda kwaikwayon salo da jajircewar Bikila da suka samu labari, irin su Haile Gebrselassie da Eliud Kipchoge.
“Mu 'yan tseren Afirka, mun kawo wannan matakin ne albarkacin Abebe Bikila, Saboda shi na kawo matakin da na ke kai ahalin yanzu,” in ji Gebrselassie.
Getnet Wale, kuwa da zai wakilci 'yan wasan gudu na Habasha a gasar wasannin Olympic da ke gudana a birnin Paris na kasar Faransa ajin mita 3000, ya bayyana Bikili a matsayin wani dan tsere mai kama da walkiya.
“Ba za a taba mantawa da shi bam har abada. Saboda shi ne mafari.”










