Munanan abubuwan da BBC ta gani a Sudan

Asalin hoton, Lyse Doucet / BBC
- Marubuci, Lyse Doucet
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Chief international correspondent
- Lokacin karatu: Minti 6
Babu wanda ke zaune a wannan gari na El Geneina, da ke yammacin Darfur wanda ya zama tamkar kufai a yanzu.
To amma har yanzu gine-ginensa na nan sai dai a yanayin da duk wanda ya gansu zai san irin mummunan labarin abubuwan da suka faru a garin.
Ba abin da ake iya gani a jikin gine-ginen nan sai ramukan harsashi ta ko'ina. An kakkarya kofofi.
Ga manyan motocin yaƙi na sojin Sudan na sintiri a titunan birnin. Har yanzu ana iya jin warin irin wutar da ta yi wa birnin illa a shekarar da ta gabata.
“Abin tashin hankali ne da tausayi ka bi cikin garin nan da ya zama kufai,” in ji sabon babban jami'in jin-kai na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda ziyararsa ita ce ta wani babban jami'in majalisar ta farko tun bayan da ƙasar ta Sudan ta faɗa yaƙin basasa watanni 19 da suka wuce.
“Darfur ce ta fi ganin illar wannan yaƙi na basasa,” in ji Fletcher, babban jami'in jinkan na Majalisar ta Ɗinkin Duniya.
Birnin na fama da matsalar kariya da annobar cin zarafi ta lalata da kuma ƙamfar abinci.
Wannan ziyara ta jami'in ta tabbata ne kawai bayan amincewar manya abokan faɗan - wato rundunar sojin Sudan ƙarƙashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta amince da shi a matsayin shugaban ƙasar da kuma dakarun RSF, ƙarƙashin jagorancin Janar Mohamed Hamdan Dagalo, wanda ake kira Hemedti, wanda dakarunsa ne ke iko da yawancin Darfur.
Waɗannan dakaru ne na RSF, tare da mayaƙa Larabawa suka ƙaddamar da yaƙi a kan yawanci ƙabilun da ba Larabawa ba a El Geneina a bara, a abin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana a matsayin ƙoƙarin share wata al'umma daga doron ƙasa, da aikata laifukan yaƙi - har ma ƙungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta ayyana abin da ya faru da kisan kiyashi.
Ita ma rundunar sojin Sudan ɗin ta fuskanci suka kan irin rawar da ta taka a wannan balahira a birnin.
Dukkanin ɓangarorin biyu na ƙungiyar ta RSF da kuma rundunar sojin ta Sudan sun musanta zargin aikata laifukan yaƙi -maimakon haka sai suke zargin junansa da laifin.

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
'Yanjarida kaɗan ne suka samu damar zuwa birnin na El Geneina suka ga halin da yake ciki bayan wata da watanni da kisan mutanen da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sun kai 15,000.
Tashin hankalin da fyaɗe da satar kaya da aka yi a wannan birni sun kasance ɗaya daga cikin abubuwa mafiya muni da aka gani a yaƙin basasar Sudan, lamarin da ya haifar da bala'i mafi muni da jama'a suka samu kansu a ciki a duniya.
Mun yi tafiya daga garin Adre na Chadi da ke kan iyaka tare da jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya inda muka ga garuruwa da suka zama kufai.
Kana iya ganin manyan motoci 'yan kaɗan ɗauke da kayan tallafi na Majalisar. Sai kuma amalanke da za ka iya gani da jakuna ko dawakai ke ja suna kai komo a kan iyakar.
To amma a ɗaya ɓangaren kuma na ƙasar Sudan kana iya ganin mayaƙan RSF, sanye da kayan soji riƙe da bindiga wasu ma yara ne.
To amma kafin mu bar Adre, sanin yadda yake da wahala mu samu bayanai a ciki, mun ɗauki lokaci a cikin sansanin da Majalisar Ɗinkin Duniya ke sojojin Sudan ke tafiyarwa a kusa da iyakar.
A wannan sansani da yawanci mata ne yara da manya wasu ma na ɗauke da jarirai su ne suka cika sansanin.
Duk waɗanda muka tattauna da su daga El Geneina suka fito. Kowa zai faɗa maka irin labarinsa daban - kan yadda ya tsira daga garin a yanayi na yunwa da hare-haren da aka afka musu a gidajensu.
Wata yarinya mai shekara 14 ta faɗa mana irin azabar da suka gamu da ita - ta shaida mana yadda aka kashe 'yan'uwansu maza, waɗanda suke gudun hijira tare.
“Wasu daga cikinsu ma yara ne na goye, masu san nono, sun yi ƙananan da ba za su iya tafiya ba. Manyanmu da ke tafiya tare da mu su ma ana kashe su.” In ji ta.
Na tambaye ta yadda har ta iya ta tsira.
Ta ce suna ɓuya ne da rana sai da tsakar dare su kama hanya. Saboda idan ka tafi da rana mayaƙan suka gan ka za su kashe ka. ''Ko da daren ma akwai haɗari'' ta ce.
Yarinyar tana tare da mahaifiyarta amma ba ta san inda mahaifinta yake ba.
Wata dattijuwa cikin ɓacin rai ta ce, an raba 'ya'ya da iyayensu maza, mata an raba su da mazansu.
Ta ce, suna kashe kowa -kisan kan-mai-uwa-da-wabi, suna kisan mata da maza da yara da kowa ma.

Asalin hoton, Lyse Doucet / BBC
Lokacin da muka je El Geneina, inda muka fara yada zango shi ne wani asibiti da ke sansanin 'yan gudun hijira na Al-Riyadh, inda yawanci maza ne dattijai, wasunsu da sanduna na tafiyar guragu suna zazzaune.
Wani dattijo ya yi jawabi ga tawagar ta Majaliar Ɗinkin Duniya inda ya bayyana irin azabar da ya ce sun sha.
Ya ce a lokacin da yaƙin ya fara wasunsu sun goyi bayan rundunar sojin ƙasar wasu kuma sun mara baya ga ƙungiyar RSF. To amma yanzu a matsayinsu na 'yan gudun hijira ba sa goyon bayan kowa kuma suna buƙatar duk wani taimako da za su samu.
Bayan da suka gabatar da irin bayanansu babban jami'in jinkan na majalisar Fletcher, ya yi musu jawabi kai tsaye.
Jami'in ya tausaya musu tare da nuna takaicin irin halin da suka shiga.
Bayan tawagar ta Majalisar Ɗinkin Duniya akwai wasu ƙungiyoyi na sa-kai na Sudan da kuma na duniya masu agaji wajen ashirin da ke taimakawa.
Suna wannan aiki ne a yanayi na wahala domin babu wadatacciyar wutar lantarki ko waya ko kuma intanet.

Asalin hoton, Joyce Liu / BBC
Tariq Riebl, wanda ke jagorantar aikin na Sudan a ƙuniyar bayar da agaji ta ƙasar Norway, ya ce, “Akwai buƙatar ƙara tashi tsaye,”
Ya ce babban abin da ya dame shi shi ne babu wanda ya damu, duniya ta mayar da hankalinta ne kan wasu yaƙe-yaƙen, kamar na Ukraine da Gaza.
Ya ƙara da cewa wannan yana ɗaya daga cikin rikice-rikice mafiya muni da aka sani a kan ta'addancin da aka aikata da kuma mutanen da ke gudu.
Yanzu dai babban jami'in na Majalisar Ɗinkin Duniya a yayin wannan ziyara ta mako ɗaya ya gana da wakilan sojin Sudan da ƙungiyar RSF, domin samun damar kai kayan agaji a wurare da buɗe wasu cibiyoyin.
Ya nuna takaicinsa a kan yadda ƙasashen da ke gaba da juna ke mara baya tare da samar da kayan yaƙi ga ɓangarorin da ke rikicin.
To amma ya yi alƙawarin ɗaukar mataki.
Ana zargin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da mara baya ga ƙungiyar RSF yayin da ƙasashe irin su Masar da Iran da Rasha su kuma daman an san suna bayan rundunar sojin Sudan ne.
Su kuwa irin su Saudiyya suna aunawa ne su gani, inda ƙungiyoyi kamar su ƙungiyar ƙasashen Larabawa ta Arab Union, suke cewa su suna ƙoƙarin samar da zaman lafiya ne.
Yanzu dai al'ummar Sudan da dama da ma ma'aikatan agaji sun zuba ido da fatan ziyarar ta Mista Fletcher za ta kawo sauyi a wannan rikici mafi wahala a duniya.











