Argentina ta ci Bolivia 6, Messi ya ci uku

Messi

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Lionel Messi ya ci kwallo uku a wasan neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026, wanda Argentina ta doke Bolivia 6-0.

Wannan ne karo na 10 da Messi ke ci wa Argentina kwallo uku a wasa guda a tarihi.

Dan wasan gaban Iter Miami mai shekara 37, wanda ya bayar da kwallo biyu aka ci a filin wasan na Monumental da ke birnin Buenos Aires, ya kamo takwaransa na Portugal Cristiano Ronaldo a yawan cin kwallo uku a kasarsu.

Argentina da ke saman teburi ta bai wa Colombia maki uku a wasannin neman gurbin gasar kofin duniya ta 2026, duk da cewa ta yi rashin nasara a watan Satumba ta kuma canjaras da Venezuela a makon jiya.

"Abin farin ciki ne samun wannan nasara, domin na sanya mutane da dama farin ciki. Yadda suka rika kiran sunana kuma ya samin farin ciki," in ji Messi.

"Wannan na ƙaran farin ciki a inda nake. Duk da cewa ina da shekaru, amma duk sanda na zo nan sai na ji na dawo tamkar ɗan yaro, saboda yadda hankalina ke kwanciya da tawagar. Matukar ina jin dadin jikina zan ci gaba da wasa yadda ya kamata".

Wannan ne wasa na biyu da Messi ya buga wa Argrntina tun bayan raunin da ya ji a watan Yuli a gasar Copa America, kuskuren da 'yan bayan Bolivia suka yi ya sa suka jefa musu kwallo a minti na 19.

Ya bai wa Lautaro Martinez da Julian Alvarez kwallo sunci kafin daga bisani Thiago Almada da ya shigo a canji ya ci ta hudu .

Messi ya ci kwallo 112 a wasa 189 da ya buga wa Argentina - wanda shi ke biye wa Ronaldo da ya ci wa Portugal 133 a ɓangaren maza.