Dabbobin da suka ɓace a doron duniya saboda shuɗewar zamani

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dabbobi masu yawa sun ɓace shekaru da dama da suka shuɗe.
Lokacin karatu: Minti 5

Ra'ayinmu game da ɓacewar abubuwa na iya zama abin tsoro, wanda ke shafe tsoffin halittu kamar dabbar dinosaurs da sauran misalan. Amma gaskiyar ita ce ɓacewar na faruwa ta wata hanya mai an tsoro.

Asusun kula da dabbobi na duniya ya yi ƙiyasin cewa akwai aƙalla nau'ikan dabbobi 10,000 da ke ɓacewa a kowace shekara, kuma ɓacewa na har abada.

Asusun ya ce abu ne mawuyaci a iya tantance haƙiƙanin adadin dabbobin da suka ɓace, saboda a cewarsa yana da wahala a san haƙaƙin dabbobin da ke rayuwa a gandun daji.

Asusun ya ware ranar 30 ga watan kowace Nuwamba domin tunawa da dabbobin da suka ɓace.

A wannan maƙala mun yi ƙoƙarin tattaro wasu daga cikin dabbobin da suka taɓa rayuwa a doron ƙasa amma yanzu babu labarinsu.

Jajayen birrai - Ghana da Ivory Coast

Wani jan biri mai launin fari a ƙiji da zikinsa riƙe da ɗansa mai irin wannan launin a kan wata bishiya.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jajayen birran ƴan asalin Zanzibar na daga cikin dabobin da suke ɓace a ban ƙasa, wanda rabon da a gansu tun 1978. A baya akwai nau'ikan waɗannan birran aƙalla 1,500 a Afirka.

Suna cikin na'ikan birran da aka daina jin ɗuriyarsu a baya-bayan nan. Birrai ne masu matsakaicin girma da jajayen tabo a jikinsu.

An yi imanin cewa birran sun ɓace tun a farkon shekarun 2000.

A baya sun yi rayuwa tsakanin ƙasashen Ghana, nau'i ne da ya fita daban a cikin birrai saboda ba su da babban ɗan yatsa.

Dabbobi ne masu kyawun halitta, da ke rayuwa a cikin garke da galibi suka fi rayuwa kan bishiyoyi, amma yadda mutane ke ywan sare bishiyoyi ya tilasta musu sauya wurin zama.

Yayin da dazuka ke ci gaba da zama gonaki a wasu wuraren , jajaye birran sun ci gaba da raguwa, lamarin da ya sa ba sa iya kare kansu daga masu kai musu hari.

Kifin Dolphin - China

Kifin dolphin cikin kogi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kifin dolphin da aka fi sani da baidji ya kasance cikin tsoffin halittun da suka jima a gansu ba.

A shekarar 2016 ne aka bayyana kifina hukumance. Nau'in kifi ne mai aukar hankali da ke rayuwa a cikin teku.

Kifi ne mai ƙarfin gaske, wanda a wasu lokuta ke yi wa ƙananan jiragen kamun kifi barazana a cikin teku.

haka a wasu lokuta waɗannan kifaye kan yi bazarana har da manyan jragen dakon kaya a ciin teku.

Amma sannu a hankali yanzu wannan nau'i na kifi ya zama tarihi, domin an jima a ji ɗuriyarsa ba.

Ƙafar alade - Alabama, Amurka

..

Asalin hoton, Getty Images

Wannan wasu na'ikan dƙwarin da ke rayuwa a ciin ruwa ne a kogin jihar Alabama da ke Amurka.

A shekarar 2006 ne aka bayyana ɓacewar ƙwarin daga kogin a hukumance.

Ana kiransu da ƙafar-alade, saboda yadda suke kamanceceniya da siffar ƙafar aladu.

kwarin kan taimaka wajen tsaftace ruwan da ya gurɓace, musamman idan gurbacewar ba ta kai wani mataki ba.

A baya akwai irin waɗannan ƙwarin masu yawan gaske a ruwan yankin Alabama, amma yanzu babu su.

Tsuntun dodo - Mauritius

Dodo tare da ɗansa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dodo ya kasnce cikin tsuntsayen da suka ɓace sakamakon ayyukan ɗan'adam.

Wannan tsuntsu mai suna dodo ya kasance cikin tsuntsayen da suka yi ɓatan dabo.

Tsuntsu ne a baya ya fice tsakanin takwarorinsa tsuntsayen dawa.

A baya an fi sanin tsuntsun a tsibiri Mauritius, wani yanki da bai son maharba ba.

Tsuntsu ne da baya iya tashi da fuka-fukansa.

Bayan ɗan'adam ya isa Mauritius, sun riƙa kamo dabbobi da nufin kiwatawa da kuma samun nama, kuma tsuntsun dodo ya kasance cikin dabbobin da wannan sauyi ya kawo ƙarshensu.

Rabon da a ga nau'in wannan tsuntsu tun ƙarni na 18.

Kifin Steller - Tsakanin Alaska da Russia

Kifin Steller

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana tunanin ya ɓace ne sakamakon yawan kama shi da ake yi

Kifin ne da idan ya gifta zai yi wahala a kasa iya ganinsa saboda girmansa.

Yana cikin dangin kifayen manatee, kifi ne mai girma da tsayin jiki da zai iya kai mita tara.

Yana da kariya a jikinta ta yadda ba komai ne ke iya ji masa ciwo ba. Masu kamun kifi na son kama shi saboda wadatar namansa, kuma an yi imanin cewa zaƙin namansa ya yi kama da naman shanu.

Ana tunanin ya ɓace ne sakamakon yawan kama shi da ake yi da kuma sauyawar abincinsa da aka samu a duniya.

Qwagga - Afirka ta Kudu

Dabbar Quagga
Bayanan hoto, Dabbar Quagga ta ƙarshe ta mutu a gidan namun dawa na Amsterdam a 1883.

Kyawun haitar jikin dabbar ne ya fi ɗaukar hankali mutane game da ita.,

Daga kanta zuwa wuya ta yi kama da raƙumin dawa, yayain da gashin gadon bayansa ya ke kama da na dok.

A baya wannan dabba ta yi rayuwa Afirka da wasu ƙasashen Turai.

Yawaita farautarta ne ya haifar da ɓacewarta a doron ƙasa.

Dabba ta ƙarshe cikin wannan nau'i da ta rage, ta mutu ne a 1880.

Barewar elk - Ireland

barewar elk

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barewar elk na kama da namijin barewa, sai dai ya fi ta faɗi.

Barewar elk na kamanceceniya da namijin barewar da muke gani a yau, amma ya fi na yanzu ɗaukar hankali.

Sai dai shi jikinya cike yake da gasu masu yawa, sannan faɗinsa ya yi kama d ana giwa.

Wannan nau'i na dabbobi ya ɓace kusan shekara 7,700 da suka wuce, saboda yawan farauta da sauyin yanayi.

Shaho mai farar jela - Birtaniya

Shaho mai farin jela na shawagi a kan teku

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shaho mai farin jela

Wannan nau'i na tsuntsaye sun ɓace a Birtaniya tun farkon ƙarni na 20.

Tsuntsun mai kyawun halitta ya riƙa ɗaukar hankali mutane a baya, saboda yadda yake ɗaukar ƙananan yara, lamarin da ya sa aka riƙa bayar da shawarar kashe shi.

Tun gabanin haramta farautar tsuntsaye, wannan nau'i na tsuntsu ya ɓace.