Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ambaliya ta raba kusan mutum miliyan biyu da muhallansu a Maiduguri - Zulum
Gwamnan jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce adadin waɗanda mummunar ambaliyar ruwan da ta ɗaiɗaita birnin Maiduguri ta shafa ba su gaza miliyan biyu ba.
A wata hira ta musamman da BBC a birnin Maiduguri na jihar Bornon, Gwamna Zulum ya ce ba a taɓa tantance ko faɗin adadin ɓarnar da ambaliyar ta yi, ko adadin waɗanda suka mutu ba har sai ruwan ya janye.
Ya ce ana ci gaba da aikin ceto, kwanaki bayan ɓallewar da madatsar ruwa ta Alau ta yi, lamarain da ya janyo mummunar ambaliyar ruwan da ba a taɓa ganin irinta ba cikin shekara 30.
Gwamnati ta tsugunar da waɗanda ambaliyar ruwan ta shafa a sansanoni huɗu a birnin, sai dai ɗaruruwan mutane sun maƙale a wuraren da ambaliyar ta fi ƙamari.
Yawancinsu na zaune a saman rufin gidaje, babu ruwa ba abinci na tsahon kwanaki.
Gwamnati dai na raba abinci ga waɗannan mutanen, sai dai a iya cewa tamkar jefa ƙwayar hatsi a cikin teku ne. ''Sam bai isa ba, babu ta yadda za a yi mu iya ciyar da miliyoyin mutane cikin awoyi kaɗan, sai muka ɗauki matakin tabbatar da cewa mun tsugunar da waɗanda ambaliyar ta shafa a sansanonin da muke da su, sai mu kai abincin wurin in ba haka ba mutane da dama za su mutu a bin layin karɓar abinci,'' in ji Gwamna Zulum.
Gwamna Zulum ya ƙara da cewa rashin kula da madatsar ruwan Alau na daga cikin dalilan da suka haddasa ambaliyar. Ya ce kamata ya yi a ce ma'aikatar ruwa ta Najeriya ta dinga bibiya da kula da ingancin madatsun ruwan da ake da su a ƙasar, amma an ɗauki lokaci mai tsawo ba tare da an yi wannan ba. Sai kuma uwa uba mamakon ruwan da damunar bana ta zo da shi ya ƙara ta'azzara lamarin.
Wata fargaba da ke damun gwamnatin jihar Bornon ita ce tserewar da fursunoni suka yi daga gidajen kaso, ciki har da mayaƙan Boko Haram sakamakon ambaliyar da ta rushe wani sashe na gidajen kason jihar.
Zulum ya ce wannan ambaliyar ruwa ta ƙara jefa jihar Borno cikin halin ni 'ya su, a daidai lokacin da jihar ke ƙoƙarin farfaɗowa daga tada ƙayar bayan da mayaƙan Boko Haram suka kwashe shekara 15 suna yi.
Kama daga kashe dubban mutane, da lalata makarantu da asibitoci da sauransu.