Me ya sa gwamnatin Kano ke son rage cunkoso a birnin?

    • Marubuci, Daga Umar Mikail da Zahradden Lawan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • Lokacin karatu: Minti 3

Duk wanda ya shekara kamar 20 rabonsa da ƙwaryar birnin Kano zai sha mamakin ganin yadda ya cika da gine-gine da kuma abubuwan more rayuwa, amma da wuya a ga irin wannan sauyin a garuruwan da ke gefen birnin.

Abin da zai ƙara tabbatar da haka shi ne tarin sababbin asibitoci, da makarantu masu zaman kansu, da manyan kantuna na zamani, da wuraren yin biki ko dabdala da aka giggina cikin shekara 10 kacal da suka wuce.

Titin Gidan Zoo da na Gwarzo kaɗai sun ishe mu misali.

A cewar shafin World Population Review na Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD), ƙiyasi ya nuna cewa akwai mutum miliyan 4,490,734 da ke zaune a birnin Kano a shekarar 2024. Shekara 10 da suka wuce, mazauna birnin miliyan 3,507,735 ne a 2014.

Kazalika, an samu ƙarin mutum 142,253 cikin shekara ɗaya idan aka kwatanta da 4,348,481 da birnin ke da su a 2023 - kenan al'ummar na ƙaruwa duk shekara da kashi 3.27 cikin 100.

Sai dai hakan ya sa birnin ya cika sosai da al'umma saboda hatta mazauna maƙwabtan garuruwa sai sun yi tattaki zuwa cikinsa kafin su samu wasu abubuwan da rayuwa ke buƙata.

Wannan dalilin ne ya sa gwamnatin Kanon ta ce ta ƙudiri aniyar rage cunkoson ta hanyar gina sabbin birane masu ɗauke da abubuwan more rayuwa a wurare huɗu da ke faɗin jihar.

Kano na da ƙananan hukumomi 44 jimilla, amma takwas daga cikinsu ne suke a ƙwaryar birnin.

Rage cunkoso da raya karkara

Abduljabbar Muhammad Umar, shi ne kwamashinan kasa da tsare-tsare na Kanon kuma ya faɗa wa BBC cewa babbar manufarsu ita ce gina abubuwan more rayuwa a yankunan.

Da yake bayani, kwamashinan ya ce sun zaɓi yankuna huɗu domin gudanar da ayyukan. Su ne: Lambu da Unguwar Rimi a ƙaramar hukumar Tofa, Yar Gaya da Rijiyar Gwangwan a ƙaramar hukumar Dawakin Kudu.

Sai dai ya ce ba gina filayen gwamnati za ta yi ba.

"Duk wanda ya shigo Kano, da mazauninta da baƙo, ya san cewa Kano ta cika. Duk ƙanƙantar fili sai ka ga ana ƙoƙarin tsaga shi domin gina gida," a cewarsa. "Saboda haka gwamnati ta fito da tsarin rage cunkoson."

Ya ƙara da cewa baya ga rage cunkoson suna da burin raya karkara.

"Gwamanti ta kuma duba batun raya karkara kamar yadda muka yi kamfe kafin zaɓe. Da ma Abba Kabir ya yi alƙawarin zai gina karkara.

"Bugu da ƙari, wannan zai taimaka wajen rage yin gine-gine a kan hanyar ruwa, da kuma taimakawa wajen yiwuwar tasirin annoba.

"Abin da muka fi mayar da hankali shi ne gina abubuwa saboda bai kamata a ce idan mutum ya taho daga Lambu sai ya zo Rijiyar Zaki zai samu asibiti mai inganci.

"Mun lura cewa idan muka gina waɗannan abubuwa za su fi jan hankalin mutane su zo su gina nasu."

Fulotai nawa za a yanka?

Duk birnin da za a gina, gwamnati za ta kwashi kasonta kafin ta sayar wa sauran jama'ar gari, kamar yadda Kwamashina Abduljabbar ya yi bayani.

"A garin Yar Gaya da Rijiyar Gwangwan mun bayar da fulotai sama da 2,600. A garin Lambu da Unguwar Rimi kuma mun bayar da sama da 1,500.

"Idan aka yi ƙidaya za a ga cewa fulotan jama'a sun fi na gwamnati yawa. Gwamnati za ta gina abubuwan more rayuwar ne da nata filayen."

Ya ƙara da cewa tuni gwamnati ta fara biyan masu gonakin da aka karɓi filayensu.

"Yanzu muna kan sallamarsu, amma ba mu fara komai ba har sai an sallame su. Abubuwa ne daban-daban. A Lambu mun bai wa gwamantin tarayya fili hekta 50 domin su gina a sayar wa mutane."

Birnin Kano na ɗaya daga cikin wuraren da ake yanka filaye ba bisa tsari ba, abin da aka fi sani da awon igiya.

Kwamashinan ya ce: "Idan ba mu yi abin da yakamata ba, idan ba mu yi irin wannan tsarin ba awon igiya ne za su bazu a Kano."