Matan da ke so a yi watsi da aure da jima'i

Asalin hoton, Getty Images
Bayan nasarar da Shugaba Donald Trump ya samu a zaɓen shugaban ƙasar Amurka da ya gabata, gwagwarmayar 4D, wadda ta faro daga Koriya ta Kudu, ta janyo hankalin duniya.
Me ya sa wasu mata ke son rayuwa tare da guje wa waɗannan abubuwa guda huɗu, wanda ke son yin watsi da jima'i, soyayya, aure da kuma haihuwa?
Min-ju ta tuna wani rubutu da aka wallafa a kafofin sadarwa wanda ya janyo hankalin mata a faɗin duniya:
"Maza na faɗin cewa zubar da ciki haramun ne bayan zaɓen Trump. Sai dai a hakan suna so mata su riƙa yin jima'i da su. Wannan sarkakiyar ba za ta ci gaba da faruwa ba."
Kamar sauran mata da yawa waɗanda muka tattauna da su a wannan labari, ƴar shekara 27 ɗin wadda ta buƙaci mu sakaya sunanta saboda fargabar tsangwama, ta ce tana rayuwa ne kan waɗannan abubuwa huɗu: Watsi da soyayya, babu jima'i, babu aure sannan ba haihuwa.
Wannan tafiya ce da masu rajin kare hakkin mata suka kirkiro a Koriya ta Kudu waɗanda suka zaɓi rayuwa ba tare da miji ba, don martani ga cin zarafin mata a cikin al'umma.
"Muna yawan jin mata da ake azabtarwa a soyayya har ma kashe su idan suka yi yunkurin kawo karshen alaƙar," in ji Min-ju.
Wannan gwagwarmayar, wadda ta kalubalanci rawar da al'ada ke takawa, yanzu ya fara yaɗuwa zuwa Amurka.
A makonnin baya-bayan, tattaunawa da ake yi kan tafiyar ta 4B na janyo hankali a yamma bayan samun nasarar Donald Trump a zaɓen Amurka.
Masu fafutukar kare hakkin mata a Koriya ta Kudu, waɗanda suka kirkiro da kuma rayuwa da waɗannan abubuwa huɗu, sun yi na'am da yadda hankalin duniya ya koma kan gwagwarmayarsu - a ɗaya gefen kuma damuwa.

Asalin hoton, Gong Yeon-hwa
Mece ce gwagwarmayar 4D?

Asalin hoton, B-WAVE
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kalmar "4B" dai ta fito ne daga abubuwa huɗu a Koriya ta Kudu:
Watsi da soyayya, babu jima'i, babu aure sannan ba haihuwa.
"Gwagwarmaya ce ta yau da kullum ga mata," a cewar Ji-sun, wadda ta ki bayyana sunanta na asali.
Ji-sun, tsohuwar jagorar masu neman ƴancin zubar da ciki mai suna B-wave, ta ce ƙungiyoyin mata da dama ne suka haɗu suka haifar da 4B a 2016.
Ta ce batun rashin aure, an kirkiro shi ne don yin watsi da batun da ake cewa aure abu ne na mata.
Sauran abubuwan sun haɗa kin yin jima'i, soyayya da kuma haihuwa - wanda aka ƙara a cikin abubuwan da matan ke fafutuka a kai.
"Zaɓi ne na mutunta kan mu," in ji Ji-sun.
Gare ta, ba a yi 4B ba don guje wa maza, sai dai watsi ko rage ƙarfin ikon maza a cikin al'umma.
"Wannan gwagwarmaya ce ta mata don su yi rayuwa kamar ɗan'adam," a cewarta.
"Soyayya, jima'i, aure da kuma haihuwa abubuwa ne da ke durkusar da mata," kamar yadda ta bayyana.
Gong Yeon-hwa, wadda ta yi rubuce-rubuce kan tafiyar, ta bayyana lokacin da ta yanke shawarar fara amfani da abubuwan da 4D ke fafutuka a kai.
"Lokaci ne na muhimman abubuwa," in ji Yeon-hwa, inda ta faɗi mutuwar wata mata mai shekara 23 wadda aka far wa saboda kawai ita mace ce, da yaɗuwar amfani da kyamarorin ɓoye domin naɗar bidiyon mata da kuma wata ƙungiya da ta wallafa bidiyoyin a yanar gizo.
"Mata da yawa sun fara gane cewa ba aure kaɗai bane, har ma soyayya da jima'i kan iya saka su cikin barazana," in ji ta.
Mata sun fantsama kan tituna a 2016 lokacin da aka kashe wata mai shekara 34 a ɗakin hutu a birnin Seoul.
Yadda matan Koriya ta Kudu suka amshi fafutukar 4B

Asalin hoton, B-WAVE
Ga Min-ju, ta shiga tafiyar 4D ne don kare kanta daga cin zarafin da mata ke fuskanta a soyayya.
"Ba a hukunta masu aikata laifin yadda ya kamata," in ji ta.
"Yin soyayya a Koriya yana kamar ka bai wa namiji damar ya wulakanta ka, har ma da ɗaukar rayuwarka.
Gomsae, wata mata mai shekaru 30 wadda ba ta son ta ambaci sunanta na asali, ta ce aikin da aka yi mata - ya ba ta ƙwarin gwiwar fara amfani da salon rayuwar 4D.
"Likitoci sun mayar da hankali wajen gyara ma'ajiyar kwan mace, sai dai sun fi mayar da hankali kan damar haihuwa," in ji Gomsae.
"Wannan ya sa na gano cewa ana ɗaukar jikin mace a matsayin wata abar samar da abu".
Mata sun bayyana cewa rayuwar tare da koyarwar 4D yana da matukar wahala a Koriya ta Kudu.
Min-ju ta ce ba ta faɗa wa ƴan uwanta maza ko abokai ba kan matakin da ta ɗauka.
Gwagwarmayar ta yaɗu zuwa wasu ƙasashe

Asalin hoton, Getty Images
Matakin shugaban Amurka kan batun zubar da ciki, wanda ya bar batun ga gwamnatocin jihohi don ɗaukar matakin da suka ga ya dace, ya janyo fargaba a tsakanin ƙungiyoyin kare hakkin mata na yiwuwar saka dokar haramta zubar ciki ta tarayya.
Ƙari kan haka, kalaman Trump kan mata, ciki har da batun zargin cin zarafi na lalata da kuma maganganu da ya yi kan Kamala Harris, sun zama sahun gaba.
"A martani ga waɗannan duka, akwai alamu na ƙarin matan Amurkawa da ke da niyyar "ƙauracewa" maza da kuma daɓɓaka ɗabi'un 4D.
Bayanai da aka wallafa a kafofin sada zumunta kan gwagwarmayar ya janyo hankalin ɗimbin mutane, kuma an yi ta neman batutuwa kan gwagwarmayar a cikin watanni da suka gabata.
Yeon-hwa ta ce yaduwar 4D yana da alfanu da kuma rashinsa.
'A ɗaya hannu, ina alfaharin kasancewa a ƙungiyar 4B, gwagwarmayar da ta fara da matan Koriya - inda yanzu ta zama sahun gaba ga masu fafutukar kare hakkin mata a duniya," in ji ta.










