Hikayata: Labarin Naɗin Lauje 02/03/2025

Bayanan sautiTaɓa hoton da ke sama domin sauraron shirin
Lokacin karatu: Minti 1

A labarinmu na Hikayata 2024, a wannan makon mun kawo muku labarin labarin Naɗin Lauje na Fauziyya Sani Jibril da ke gida mai lamba 2313 unguwar Sani Mainagge 'A', a ƙaramar hukumar Gwale da ke birnin Kano wanda Badriyya Tijjani Kalarawiy ta karanta.

Wannan labari na Naɗin Lauje yana jan hankali ne a kan muhimmancin gwajin jini kafin aure.

An gina labarin ne a kan wata mata wadda ta yi aure cikin naɗin lauje, amma daga bisa ta zo tana da-na-sani.