Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Babban asibitin Gaza na cikin mayuwacin hali sakamakon katsewar lantarki
- Marubuci, Adnan Elbush
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Arabic
Asibitin Al-Shifa shi ne babban asibitin birnin Gaza, kuma cike yake da majinyata, waɗanda ke cikin mawuyacin hali.
Duk inda ka duba a farfajiya da harabar asibitin cike suke da ɗaruruwan gawarwaki, yayin da ɗakunan ajiye gawarwakin asibitin ke maƙare da gawarwaki.
A cikin ɗakunan kula da marasa lafiyar kuma, majinyata ne cike a ɗakunan, yayin da ma'aikatan jinya ke fuskantar matsin lamba, sakamakon rashin wutar lantarki a asibitin.
Lamarin da ke barazana ga ayyukan asibitin kasancewar injinan bayar da wutar lantarki ga asibitin na daf da tsayar da aiki.
Mata da ƙananan yara na daga cikin waɗanda suka fi jikkata.
Wannan ka iya haifar da mummunan bala'i.
Wannan ƙaramar yarinya da aka kai asibiti na kukan raɗadin ciwo, yayin da take kiran likitoci da su kawo mata ɗauki don yi mata maganin raunukan da ta ji.
Wani hari ta sama da Isra'ila ta kai ne ya faɗa kan gidansu a Gaza, yayin da 'yan uwanta da dama suka mutu.
To sai dai likitocin asibitin na cikin mayuwacin hali, yayin da suka fi bayar da fifiko ga waɗanda suka fi jikkata.
Wannan matar ta kasance a gaban gawarwakin 'yan uwanta da suka mutu a hare-haren boma-bomai da Isra'ila ta kai unguwarsu da ke kusa da birnin Gaza.
Sauran 'yan uwan da suka tsallake-rijiya-da-baya a hare-haren na dawowa gida ɗaya-bayan-ɗaya.
“Muna tsaka da bacci ne aka far wa ginin gidanmu da hare-hare ta sama kamar kowane gida,” in ji matar.
“Harin ya faɗa kan gidanmu a lokacin da muke tsaka da bacci. Babu mayaƙan Hamas a cikin ginin da muke zaune, duka gidan fararen hula ne, kusan mutum 120 ke zaune a gidan''.
Wata matar kwance a kan gadon marasa lafiya ta ce "likitocin sun dakatar da yi mini aiki, sun fada min cewa akwai waɗanda suka fi ni jikkata, sun ce in ɗan jira. To ya zan yi? Akwai majinyata masu yawa cikin asibitin".
Mun yi magana da wata mata wadda ke kwance a asibitin, ta kuma ce "An zaƙuloni daga ƙarƙashin baraguzai, sai dai ba a samu 'yata ba, amma ina fatan za a same ta".
Shugaban asibitin Dakta Muhammad Abu Salmia, ya shaida wa BBC yadda asibitin ke fuskantar barazanar dakatar da ayyukanta.
“Asibitin ba zai iya ci gaba da aiki ba idan babu wutar lantarki. Fiye da mutum 120 ne aka kwantar a ɗakin bayar da kularwar gaggawa na asibitin da sauran ɗakunan asibitin, idan wutar lantarki ta ɗauke ayyukan za su tsaya cak a ilahirin asibitin, saboda ba za mu iya duba marasa lafiyar ba."
A yayin da BBC ke haɗa wannan rahoto, tawagar ma'aikatan na BBC ta kasance cikin yanayi na kaɗuwa yayin da suka ga makwabtai da 'yan uwa da abokansu a cikin waɗanda suka jikkata da waɗanda aka kashe.
Mun dakatar da aikin yayin da muka ci gaba da fuskantar damuwa da firgici sakamakon halin da jama'a ke ciki.
Ma'aikacin BBC Mahmoud al-Ajrami ya kasance cikin kaɗuwa, inda ya riƙa zubar da hawaye a lokacin da ya ga abokinsa a gadon asibitin ɗauke da munanan raunaka, yayin da 'yan uwansa da dama suka mutu.
Ma'aikatar lafiyar Palasɗinu ta ce tana cikin matsin lamba, kasance babban asibitin Gaza na daf da durƙushewa, sakamakon rashin wutar lantarki.