Yadda ƙungiyar Ansaru ke jan matasa a Birnin Gwari

Asalin hoton, AFP
Mazauna wasu daga cikin yankunan ƙaramar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna, sun koka dangane da yadda ƴan ƙungiyar Ansaru ke ci gaba da jan matasa tare da mamaye garuruwansu.
Jama'ar yankin sun ce ƴan Ansarun sun ɗauki lokaci suna ɗibar matasan da kuma shigar da su ƙungiyar, ko dai ta amfani da dabarun jan hankali ko kuma da ƙarfin tuwo, lamarin da ke ƙara ƙamarin matsalar tsaro a yankin.
Wasu mazauna yankin sun ce yanzu haka garuruwa irin su Ƙauyen Unguwar Gandu da Tsohuwar Kuyello da kuma Unguwar Gajere duk suna ƙarƙashin ikon ƙungiyar Ansaru.
Wani mazaunin Layin Lasan ya ce ''yanzu babban abin da yake tayar da hankalin mutane shi ne ƴan Ansarun sun zo garin Layin Lasan kuma sun nuna cewa suna so su dawo da zama a cikin garin amma mutane sun nuna rashin yarda. A halin yanzu ana zaman ɗar-ɗar ne saboda mutane basu san abin da zai je ya dawo ba tunda dai sun ce ko da ƙarfi sai sun shiga garin''
Ƴan Ansarun sun kuma shiga Unguwar Layin Ɗan-auta dake ƙaramar hukumar ta Birnin Gwari inda can ma suka sanar da aniyar su ta shigar da matasa cikin su da kuma karɓe madafun iko a yankin, kamar yadda wani mazaunin ƙauyen ya shaidawa BBC.
Duk da wannan barazana dai mazauna yankin sun ce a yanzu haka babu wadatattun jami'an tsaro da za su iya hana Ansaru kai masu hari, ko mamaye ƙauyukan nasu.
Sai dai kakakin rundunar ƴansandan Najeriya a jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan ya ce rundunar ta taɓa fatattakar mayaƙan a shekarun baya kuma a wannan karon ma za ta yi duk abin da ya dace don kawar dasu da kuma samar da tsaro ga jama'a.
Ya ce ''mun taɓa zuwa muka yaƙi waɗan nan mutane, shekaru uku zuwa huɗu da suka gabata inda muka kashe aƙalla mutum 200 a cikin su. Ana bakin ƙoƙari amma wannan wani abu ne wanda ba zamu fito kafafen yaɗa labarai muna faɗi ba tunda bayanai ne na sirri''
An dai ɗauki lokaci jama'ar ƙaramar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna, da makwabciyar ta Funtua a jihar Katsina suna kokawa da hare-haren ƴan bindiga masu alaƙa da ƙungiyar Ansaru, kuma kai harin da kuma garkuwa d mutane na ƙara yawaita a yankunan.
Su waye Ansaru?
Ƙungiyar Ansaru ta zama barazana a Najeriya cikin ɗan ƙanƙanin lokacin da ta shafe tana ayyukan ta, inda ta yi amfani da dabaru da ƙarfi wajen shiga muhallan da ke cike da tsaro don sace mutane da yin garkuwa da su, da kuma kashe mutane.
A watan Janairun 2012 ne aka ƙirƙiro ƙungiyar Ansaru, duk da cewa ba a san ta ba sai bayan wata shida da kafuwarta, sakamakon sakin wani bidiyo da ta yi da ya nuna yadda ƴan ƙungiyar suka sha alwashin kai wa Turawa ƴan ƙasashen yamma hari, domin kare Musulmai a duniya.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a watan Janairun 2012, ta ce, "A karon farko muna farin cikin sanar da al'umma kafuwar wannan ƙungiya wacce aka kafa ta kan hujjoji na ƙwarai."
Cikakken sunan kungiyar shi ne, Jama'atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan, wato: "Kungiyar Kare Musulmai baƙaƙe a nahiyar Afirka"











