Abubuwan da ke sa ku ga jini a bahayanku

Mujer preocupada

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Redacción
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo
  • Lokacin karatu: Minti 3

Abu ne shahararre a tsakanin al'umma, amma duk lokacin da ya faru yakan tayar wa mutane hankali.

Da yawan mutane kan shiga fargaba da zarar sun ga jini a bayan gidansu da tunanin cewa sun kamu da wata mummunar cuta, kamar kansar makasaya.

Abin da ba su sani ba shi ne akwai dalilai da dama da ke jawo faruwar hakan, inda wasu suka fi wasu girma.

Fermín Mearín, shugabar sashen kula da narkewar abinci a cibiyar Teknon Medical Center da ke Sifaniya ta lissafa wa BBC Mundo dalilan da suka fi jawo fitar jini ta bahaya.

1. Kumburi ko tsagewar hanyar bayaha: Akasari hakan kan jawo fitar jini mai ɗan haske, wanda za a iya gani bayan hanjin makasaya sun mommotsa.

Hemorroides

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ba lallai a iya ganin kumburin jijiyoyin makasaya (hemorrhoids) da ido ba

"Hakan na nuna cewa jinin na fitowa ne daga ƙarshen makasaya kuma a nan ne matsalar take, ko kuma a ƙarshen hanji," in ji Dr Mearín.

Ba lallai ne a iya ganin kumburin jijiyoyin makasaya (hemorrhoids) da ido ba, amma ana iya ganewa ta hanyar nazartar hoton makasaya a likitance.

Za a iya gane tsagewar makasaya ta hanyar dubawa da ido. Akan samu 'yar ƙaramar tsagewa a wurin musamman ga mutane da ke fama da cushewar ciki, kuma yana kawo raɗaɗi.

2. Cutar makasaya: Mutum kan kamu da ciwonulcerative colitis da ke jawo kumburin babban hanji, ko kuma cutar Crohn's.

Wani zanen kayan cikin mutum da hannun wani mutum yana riƙe da cikinsa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ulcerative colitis ko cutar Crohn's na jawo gudawa da kuma ciwo a mara

"A irin wannan yanayin, baya ga kumburi akwai kuma gudawa da ciwon mara," a cewar Mearin. Suna shafar baban hanji, kodayake dai cutar Crohn's kan shafi ƙaramin hanji.

Hakan kan sa bahaya ya zama ja zuwa baƙi. "Ƙarancin kumburin shi ne ke fayyace kusancinsa da makasaya da kuma launin ja da zai yi."

A gefe guda kuma, idan bahayan ya zama baƙi sosai kuma mai yauƙi, zai iya zama cewa akwai yawan jini a cikin ciki.

Idan haka ta faru, ya zama dole a ɗauki hoton tumbi domin tantance ko gyambon ciki ne ke haddasa hakan.

Akasari, ganin jini a bahaya ba shi nufin lallai akwai wata babbar matsala.

Amma idan jinin ya yi ja sosai kuma gauraye da bahayan, akwai yiwuwar yana fitowa ne daga uwar hanji ko wani wuri. A irin wannan yanayi, likitoci kan bayar da shawarar yin hoton hanji (colonoscopy) domin duba ko akwai kansar hanji.

Zanen babban hanji

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Yin hoton hanji (colonoscopy) zai iya sa a gano ko mutum na ɗauke da kansar hanji da sauran cutuka
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A wasu ƙasashen, akwai tsarin gano kansar hanji ta hanyar yi wa mutane gwaji a wani adadin shekaru.

Wannan tsari kan duba jini a cikin bahayar mutane a matsayin wata alama ta kansar hanji.

Idan aka samu jini a bahayar maras lafiya, sai a saka shi kan layin waɗanda za a sake yi wa gwaji, abin da ke jefa mutane da dama cikin fargaba.

"Mutane kan shigo wajen gwaji a ruɗe, amma akasarinsu sai a ga ba su ɗauke da wata babbar matsala," in ji Dr. Mearin.

Masu shekaru sama da 50 ko kuma samun mai kansar hanji a dangi kan sa likitoci su yi wa mutum hoton kayan ciki (endoscopy) domin tantance lafiyar uwar hanjin.

Duk da cewa launin bahaya na da muhimmanci, ya kamata a sani cewa cin nau'in wasu abinci kan jawo sauyawar launin.

Abincin licorice kan jawo baƙin bahaya. Tumaturi ma zai iya saka bahaya ya zama ja.

Ko ma dai yaya ne, duk lokacin da aka ga jini a bahaya ya kamata a tuntuɓi likita cikin gaggawa domin tabbatar da abin da ke faruwa.

Línea gris