Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waiwaye: Ambaliyar ruwa a Maiduguri da kashe ɗan bindiga Sububu
Wannan maƙale ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi
A ranar Talatar makon da ke ƙarewa ne aka tashi da labarin ambaliyar ruwa da ta tilasta wa dubban mutane barin muhallansu a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau.
Rahotanni sun bayyana cewa mutane da dama sun samu mafaka a waɗansu unguwannin da ambaliyar ba ta kai wurin ba bayan da madatsar ruwa ta Alau ta ɓalle, bayan cikar da ta yi tsawon mako ɗaya.
Wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Farfesa Usman Tar ya fitar a safiyar Talata, ya yi kira ga mutane da su gaggauta tashi daga unguwannin da lamarin ya faru.
Ya ce "Sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu a wannan shekara, muna kira ga mutanen da ke zaune kusa da koguna da su tashi nan take domin kare kansu da kuma dukiyoyinsu".
Kamun da DSS ta yi wa shugaban ƙungiyar ƙwadago Joe Ajaero
A ranar Litinin ne jami’an hukumar tsaron farin kaya ta DSS suka kama shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC, Joe Ajaero.
Kungiyar ta NLC ta bayyana a shafin sada zumuntarta na X ta ce an kama shugaban nata ne da safe a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Ƙungiyar ta NLC ta ce "har yanzu ana ci gaba da cin zarafin ma'aikatan Najeriya yayin da shugabanmu Joe Ajaero ya shiga hannun jami'an DSS da safiyar yau."
"Jami'an sun kama shi ne akan hanyarsa ta zuwa taron ƙungiyar ƙwadago ta TUC a Birtaniya."
A baya dai, shugaban NLC ɗin ya mutunta gayyatar da ƴansanda suka yi masa kan zarginsa da hannu a tallafawa ayyukian ta'addanci, da kuma cin amanar ƙasa.
Daga baya dai DSS ta saki Joe Ajaero a kan beli.
Kotu ta ba da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa kan miliyan 10
A cikin makon ne kuma wata kotu a Abuja babban birnin Najeriya ta bayar da belin mutum 10 da ake tuhuma da cin amanar ƙasa yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.
Mai Shari'a Emeka Nwite ya ce ya ba da belin maza tara da mace ɗaya, waɗanda ba su amsa tuhumar da ake yi musu ba kan naira miliyan 10 kowannensu.
Cikin tuhume-tuhumen da ake yi musu har da haɗa baki wajen tunzira sojoji su kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.
Sai dai tun da farko masu shigar da ƙara sun nemi kotun ta yi watsi da neman belin a makon da ya gabata.
Waɗanda ake zargin na iya fuskantar hukuncin kisa idan aka kama su da aikata laifukan da ake tuhumar su.
Saura kaɗan mu kama Bello Turji - Janar Chris Musa
A cikin makon ne kuma babban hafsan tsaro na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ci alwashin kama ƙasurgumi kuma jagoran 'yan fashin daji Bello Turji "nan ba da jimawa ba".
Da yake magana yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja, janar ɗin ya ce: "Saura kaɗan mu kama Turji."
Game da wa'adin biyan kuɗin haraji da aka ce Turji ya bai wa mazauna yankunan jihar Zamfara, Janar Musa ya ce sojoji na aiki da sauran hukumomin tsaro domin kare mazauna yankunan.
"Game da Turji, mutum ne kawai da ya sauka daga kan layi kuma yake tunanin ya isa, amma ina tabbatar muku za mu kamo shi kuma cikin ƙanƙanin lokaci," in ji shi.
Shugaban sojojin ya kuma nemi mazauna yankunan da su bai wa sojoji haɗin kai.
Sojojin Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Halilu Sububu
Sojojin dai sun samu nasarar kisan ɗan bindiga Sububu ne bayan ɗauki ba ɗaɗi tsakanin su da ƴan bindiga a tsakanin kwanar Dogon Ƙarfe zuwa Mayanki a ƙananan hukumomin Zurmi da Anka.
Gwamnatin Najeriya ta yi gargaɗin sake samun mummunar ambaliya a jihohin ƙasar biyu
A cikin makon ne dai ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhallai na Najeriya, Joseph Utsev ya yi gargaɗin sake samun mummunar ambaliya a kogunan Neja da Benue.
Yayin da yake jawabi ga taron menama labarai a Abuja, babban birnin ƙasar, Ministan ya ce an samu ƙaruwar ruwan da ke ƙwarara a kogunan biyu zuwa yankin Naija Delta da ke kudancin ƙasar.
'A yayin da muke jajanta wa al'ummomin jihohin Borno da Yobe da Jigawa da Bauchi da sauran jihohin da suka fuskanci ambaliya, muna ƙara jan hankalin 'yan ƙasar game da yiwuwar sake fuskantar wata ambaliyar daga kogunan Benue da Neja da wasu yankunan yankin'', in ji ministan.
Kan haka ne mista Utsev ya yi kira ga mazauna yankin su ɗauki matakai domin kauce wa bala'in ambaliya a wasu sassan kudancin ƙasar.
Gargaɗin na zuwa ne a daidai lokacin da al'ummar birnin Maiduguri ke fuskantar mummunar ambaliya da ta auka wa birnin sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau da ke wajen birnin.