Shawara 5 da Dangote ya bai wa ƴan Najeriya kan talauci

Asalin hoton, Ɗangote/X
Attajirin nan na Afirka Aliko Dangote ya bai wa gwamnatin Najeriya da al'ummarta shawarwari kan yaƙi da talauci, bayan wata ganawa da ya yi da shugaban ƙasar Bola Tinubu a farkon wannan mako.
Daga alƙaluma na baya-baya da hukumar ƙididdiga ta Najeriya ta fitar, kimanin kashi 30.9% na al'ummar Najeriya ne ke rayuwa cikin ƙangin talauci, a cewar Bankin Duniya.
Hakan na nufin suna rayuwa a ƙasar da dalar Amurka 2.15 a kowace rana.
Bankin Duniya ya bayyana cewa gwamnati na buƙatar samar da sauye-sauyen da suka dace domin shawo kan matsalar talauci da ke ci gaba da yi wa al'umma katutu.
Rahoton Bankin ya ce duk da gwamnatin tarayyar ta ce ta fito da wasu shirye-shiryen, to amma ana tafiyar hawainiya wajen aiwatar da su.
Aliko Dangote, wanda ya fi kowa arziƙi a Afirka na da dukiyar da kimarta ta kai kimanin dala biliyan 30, bisa rahoton mujallar Forbes, inda ya tara arzikinsa ta hanyar manyan kamfanoninsa na siminti da sukari da takin zamani, sannan a baya-bayan nan katafariyar matatar man fetur.
Attajirin ya nuna damuwarsa kan yadda wasu masu kuɗi da manyan 'yan kasuwa ke rayuwa ba tare da la'akari da bukatun ƙasa ba.
Ya yi tsokaci kan yadda rayuwar alatu ke karkatar da hankali daga abin da zai kawo ci gaban tattalin arziki da ayyukan yi a ƙasa.
Dalilin hakane Dangote ya yi kira ga mutane su mayar da hankali kan gina masana'antu da sauran shawarwari kamar haka;
Zuba jari maimakon rayuwar alatu
Attajirin ya nuna damuwa kan yadda wasu masu kuɗi da ƴan kasuwa ke kashe kuɗi a kan abin alatu ba tare da la'akari da bukatun ƙasa ba. Ya yi kira ga masu arziƙi da ƴan kasuwa su mayar da kuɗaɗensu zuwa gina masana'antu da samar da ayyukan yi ga jama'a musamman a yankunan da ake bukata.
Ya ce duk wanda yake da kudin sayen motar alfarma ta Rolls-Royce da jiragen sama na alfarma, kamata ya yi ya kafa masana'anta.
Juya arziƙi a Najeriya maimakon ƙasashen waje

Asalin hoton, Getty Images
Dangote ya yi kira da a daina jiran masu zuba jari daga ƙasashen waje, ya ce babu yadda masu zuba jari daga ƙetare za su shigo Najeriya idan masu dukiya a cikin gida ba sa zuba jari a gida.
"Kyakkyawan tsari da shugabanci mai gaskiya da dokoki na gari ne ke janyo masu jarin waje." in ji shi.
Saboda haka masu kuɗi da 'yan kasuwa na cikin gida ne ginshiƙin tattalin arzikin ƙasa.
Ya ce masu kuɗi su buɗe masana'antu a yankunansu saboda hakan ne hanyar inganta rayuwar jama'a kuma zai janyo masu zuba jari daga waje.
A rage dogaro da kaya daga waje
Hukumomi a Najeriya na yawan kokawa kan yadda al'umma suka fi mayar da hankali wajen amfani da kayan ƙasashen ƙetare, wani lamari da ya sanya gwamnatin Najeriya ta haramta shigo da wasu kayan da take ganin za a iya sarrafawa a cikin gida.
Dangote ya ce "muna ƙoƙarin ganin mun mayar da Najeriya cibiyar sarrafa abubuwa a Afirka.
"Ƙasasehn Afirka na shigo da kaya, amma muna so ne mu tabbatar cewa muna sarrafa duk abin da muke buƙata a cikin gida."
A yi koyi da shugabannin baya
Dangote ya yi amfani da misalai na rayuwar shugabannin ƙasa a zamanin mulkin soja, inda ya ce: "A lokacin soja, kowa, duk girman muƙaminsa yana amfani ne da mota samfurin Peugeot 504—shi ne mafi girma. To wane ne kai da za ka hau mota Rolls-Royce?"
"Za ku iya jin dadin ku, amma yana da kyau a dinga yin abubuwa da tsari."
Ya bayyana cewa idan kana da irin waɗannan kudaɗen kamata ya yi ka kafa masana'anta.
A riƙa biyan haraji yadda ya kamata
Dangote ya ce haraji ne ke gina makarantu, asibitoci da gadojin da ake amfani dasu saboda haka ya kamata masu kuɗi da ƴan kasuwa su riƙa biyan haraji yadda ya kamata
"Gwamnati ita ce babbar mai zuba jari ga duk wani mai kamfani ko ɗan kasuwa saboda haka biyan haraji wajibi ne domin shi ne tushen ci gaban kasa." in ji shi.
Dangote ya kuma jaddada cewa Najeriya na fuskantar ƙalubale mai girma sakamakon yawan haihuwa, inda ake samun yara miliyan 8.7 duk shekara.
Ya ce wannan yana nuni da cewa akwai buƙatar samar da wutar lantarki da ababen more rayuwa, domin tabbatar da cewa ƙasa na iya ɗaukar wannan ƙaruwa ba tare da matsaloli ba wanda shi ya sa waɗannan shawarwari ke da muhimmanci.











