Sabuwar dokar Taliban da ta haramta jin muryar mata a bainar jama'a

Wata ƴar Afghanistan sanye da niƙabi tana tafiya a kusa da wani shago a wata kasuwa da ke Kandahar a ranar 25 ga Agustan 2024.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A sabuwar dokar, muryar mata na cikin abubuwan da aka haramta a bainar jama'a.
    • Marubuci, Ali Hussaini
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Persian
  • Lokacin karatu: Minti 5

Ƙungiyar Taliban ta Afghanistan ta amince da wasu sabbin dokoki a makon jiya, waɗanda ta ce, "za su taimaka wajen gyara tarbiyya da rage ayyukan baɗala," da suka ƙunshi hana mata ɗaga murya a bainar jama'a da bayyana fuskokinsu a waje.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi Allah-wadai da waɗannan dokoki, sannan ta nuna damuwa a kan ɗabbaƙa su.

Wani babban jami'in MDD ya yi gargaɗi a ranar Lahadi cewa sabbin dokokin, "suna tarnaƙi ga ci gaban Afghanistan."

Tuni jagoran Taliban, Haibatullah Akhundzada ya tabbatar da dokokin.

Ma'aikatar Gyara Tarbiyya - wadda a da ake kira da Ma'aikatar Yaɗa Abubuwa masu Kyau da Hana Assha - ta nanata cewa babu wanda aka ɗaga wa ƙafa a wannan sababbin dokokin.

Ƙarƙashin sabbin dokokin, an ba ƴansandan gyaran tarbiyya na Taliban, "Mohtasabeen" damar bibiyar rayuwar mutanen Afghanistan - tun daga irin tufafinsu da yadda suke fitowa da abincinsu da ruwan da suke sha.

A ƙarƙashin sabuwar dokar, muryar mata ta zama "haramun" a bainar jama'a. Dokokin sun ce, "duk lokacin da mace wadda ta balaga ta bar gidanta domin yin wani abu mai muhimmanci, dole ne ta rufe muryarta da fuskarta da jikinta."

Dama can ma'aikatar tana ɗora irin waɗannan dokokin bisa la'akari da shari'ar Musulunci, sannan ta ce ta kama dubban mutane da suka karya dokokin.

Dokokin, kamar yadda Taliban ta bayyana, sun yi daidai da fahimtarsu ta shari'ar Musulunci, kuma Ma'aikatar Gyara Tarbiyya ce za ta ɗabbaƙa, kuma an yi su ne bisa dogaro da ƙudurin da shugaban addini na Taliban ya rubuta a 2022, inda yanzu aka tabbatar da shi, ya zama doka.

Me dokar ta ce a game da mata?

Sharaɗɗun da aka sanya wa mata
Bayanan hoto, Sharaɗɗun da aka sanya wa mata

Dokar ta fayyace yadda mata za su rufe jikinsu, ciki har da fuskokinsu, "domin gudun jan hankalin maza da kuma baɗala."

Dokar ta ce:

  • Dole mace ta rufe jikinta baki ɗaya
  • Dole mace ta rufe fuskarta domin gudun "jan hankalin maza."
  • Muryar mata "al'aura" ce a sabuwar dokar, don haka dole a daina jin su a bainar jama'a. Al'aura na nufin ɓangaren jiki da dole a rufe.
  • Dole ba za a ji mata suna waƙa da ɗaga murya wajen karatu ba, ko da kuwa daga cikin gidansu ne.
  • Kada tufafin mata su zama matsattsu, shara-shara ko gajeru.
  • Dole mata su rufe fuskokinsu da jikinsu daga mazan da ba muharramansu ba.

Haka kuma an haramta wa maza kallon jiki da fuskokin mata, haka kuma an hana mata waɗanda suka balaga daga kallon maza.

Sababbin dokoki ga maza

Dokokin ga maza a cikin zayyana
Bayanan hoto, Dokokin ga maza a cikin zayyana

Sababbin dokokin gyara tarbiyyar sun kuma ɗora wasu sharuɗa a kan maza.

Daga ciki akwai rufe jikinsu daga cibiya zuwa gwiwa idan suna waje, domin waɗannan wuraren al'aura ce.

Ba a amince maza su yi askin 'banza' ba, irin wanda ya saɓa da shari'ar Musulunci. Taliban ɗin ta hana masu sana'ar aski saisaye da aske gemu, inda suka ce hakan ya saɓa dokokin shari'ar Musulunci. A ƙarkashin sabuwar dokar, dole gemu ya zama yana da tsawo. Haka kuma an haramta wa maza sanya nakatayel.

Su wane ne Mohtasabeen?

Wata mata sanye da niƙabi a bayan babur a birnin Kandahar a ranar 24 ga Agustan 2024

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A sabuwar dokar, mata da mazan da ba muharramai ba an haramta musu zama a kusa da juna.

Mohtasabeen su ne suke da alhakin tabbatar da dokokin, kuma suna aiki ne a kowace gunduma a ƙasar. Suna bibiya tare da tabbatar da ana amfani da dokokin, sannan suna kamawa tare da tuhumar waɗanda suka karya dokokin a kotu.

Bayan samar da dokar, an ƙara musu ƙarfi, musamman ganin suna da goyon bayan shugaban addini na Taliban.

Haka kuma dokar ta bai wa ƴansandan gyaran tarbiyyar damar hana direbobin tasi ɗaukar mata idan ba tare suke da wani namiji ba, kamar mahaifi da wani ɗan'uwa babba, ko kuma waɗanda suka fito ba tare da niƙabi ba.

An kuma hana maza da mata zama a kusa da juna a cikin mota.

Babu ɗaukar hoton abubuwan masu rai

Wasu mata sanye da niƙabi suna tafiya a cikin Kandahar a Afghanistan a ranar 22 ga watan Agustan 2024

Asalin hoton, QUDRATULLAH RAZWAN/EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Sabuwar dokar tana fuskantar suka sosai.

Sabuwar dokar ta kuma ce haramun ne wallafa hotunan abubuwa masu rai, wanda ya ƙunshi zana tsuntsu, ko wata dabba ko wani mutum.

Haka kuma an haramta saya da sayar da mutum-mutumi.

Haka kuma ƴansandan gyara tarbiyyar za su bibiya tare da taƙaita amfani da rediyo, kamar jin waƙoki waɗanda "haramun" ne a shari'ar Musulunci. Haka kuma ɗauka da kallon hotunan abubuwa masu rai haramun ne.

Sai dai kuma a wani abu mai kama da tufka da warwara, ana ganin kusan dukkan jami'an gwamnatin Taliban ɗin, ciki har da Mohammad Khaleed Hanafi, wanda shi ne Ministan Ma'aikatar Gyara tarbiyyar a talabijin.

Mene ne hukunci?

Wata mata sanye da niƙabi tana tafiya a titin Kandahar a ranar 28 ga Yulin 2024.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dole mata su rufe fuskokinsu domin gudun "jan hankalin maza"

Dokar ta ce idan mutum ya aikata "laifi" zai iya fuskantar hukunce-hukunce daban-daban, daga "nasiha a kan tsoron Allah" zuwa cin tara da zaman gidan yari na kwana uku.

Sai dai dokar na fuskantar suka.

Roza Otunbayeva, shugaban aikin agaji na MDD a Afghanistan ya ce, "Bayan gomman shekaru ana yaƙi da kuma hali na tsanani da mutane suka faɗa ciki, ai mutanen Afghanistan sun cancanci abubuwa masu kyau ne, ba barazanar zuwa kurkuku ba idan sun yi jinkirin zuwa sallah ko namiji ya kalli mace ko mace ta kalli namijin da ba muharramai ba, ko kuma don mutum ya ajiye hoton wanda yake ƙauna."

Sababbin dokokin da ba a riga an fara amfani da su ba

Gwamnatin Taliban ɗin ta ƙaƙaba dokoki, kuma babu abin da zai sa su janye daga ɗabbaƙa su a hukumance, amma sai dai a wasu sassan ƙasar, ciki har da Babban Birnin Ƙasar Kabul, har yanzu ba a ɗabbaƙa dokar sosai ba.

Wata majiya daga Ma'aikatar Gyara Tarbiyyar ta shaida wa BBC sashen Pashto cewa suna aiwatar da wasu tsare-tsare ne domin tabbatar da amfani da dokar.

Majiyar ta ce, da zarar an kammala tsare-tsaren, dokokin za su ƙara fitowa fili.

Sai dai tuni an fara amfani da yawancin dokokin a wasu sassa na ƙasar.

Ma'aikatar Gyara Tarbiyya na cikin ɓangarorin gwamnati da suka fi ƙarfi a ƙasar.

Ma'aikatar ta ce a bara, ƴansandan gyara tarbiyyar sun kama tare da tsare sama da mutum 13,000 bisa laifin saɓa dokokin shari'ar Musulunci.