Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Ba za mu iya rayuwa a duniyar da karnuka ke cinye yara ba'
Gargaɗi: Akwai abubuwa masu tayar da hankali a wannan labarin.
Mazauna garin Phomolong da ke Afrika Ta Kudu sun wayi gari da iface-iface a safiyar Lahadin da ta gabata.
Wani yaro ne ɗan shekara uku ke ihun a lokacin da wasu karnuka suka far masa inda har suka kashe shi.
Yaron yana waje da abokansa a makwafta inda karnukan nau'in pit bull suke ɗaure a jikin keji.
Amma a safiyar, karnukan sun kwance idan suka rinƙa gararamba. A lokacin da yaran ke wasa ne karnukan suka yi dirar mikiya a kan Keketso Saule.
Iyalan yaron waɗanda suke cikin jimami sun bayyana cewa karnukan sun ɗauki tsawon lokaci suna yaga yaron.
"Da wani bai zo ya janye shi daga karnukan ba da sun cinye shi," kamar yadda goggon yaron, Nthabeleng Saule ta shaida wa BBC.
"Sun cinye rabin fuskarsa har ana iya ganin ƙwaƙwalwarsa."
Wani bidiyo da aka ɗauka a lokacin da karnukan ke neman cinye yaron ya nuna ƴan uwa da makwafta suna ta ihu inda suke kallon karnukan tare da tunanin ya za su yi.
Sai da wani ya zuba wa karnukan ruwan zafi sa'annan jama'a suka yi ƙoƙari suka janye Keketso da karnukan.
Cikin fushi, mutanen da suka taru sai suka koma kan karnukan inda suka rinƙa jifan su.
Sun yi ƙoƙarin kama ɗaya daga ciki inda suka cinna masa wuta.
Daga nan sai ƴan sanda suka isa wurin da lamarin ya faru inda aka kama mai karnukan wato Lebohang Pali mai shekara 21 inda ake tuhumarsa kan ajiye karnuka masu hatsari.
Akwai yiwuwar idan aka same shi da laifi za a iya cin sa tara ko kuma ya shafe har shekara biyu a gidan yari ko kuma a haɗa masa duka.
Ɗayan karen da ya rage an ɗauke shi inda wata ƙungiyar dabbobi ce ta je ta ɗauke shi.
Amma tuni aka bayar da belin Mista Pali kan kimanin dala 18. Sai dai babu tabbaci ko Mista Pali zai koma gidansa da yake haya.
A lokacin da muka ziyarci Lardin Free State, mai nisan kilomita 250 daga Johannesburg, ana iya ganin sauran ƙunar karen da aka babbaka a wurin da lamarin ya faru.
Akwai duwatsu da sanduna da kuma taya a wurin da aka ƙona karen.
Mazauna garin sun fito sun bayyana yadda suka kaɗu da ransu ya ɓaci kan abin da suka gani a ranar Lahadi.
"Wannan lamarin ya karya mana zukata," in ji Emily Moerane, wadda wata uwa ce ɗauke da yaronta.
"Ba mu san irin waɗannan karnukan, in ji ta, inda ta ce idan mai karen ba a yanke masa hukunci ba za su ɗauki doka a hannunsu.
Miƙa karnukan pit bull
Ɗaya daga cikin waɗanda suka ga lamarin ya bayyana cewa akwai wani karen nau'in pitbull a kan layin, inda ya nuna wani gida daura da gidan su Saule.
Mai karen, Mokete Selebano ya yi maraba da ni inda ya kai ni bayan gidansa, karensa mai launin ruwan ƙasa yana ta tsalle kusa da shi da matarsa.
Wannan ne junior - kamar ɗa yake a wurina," in ji shi.
Amma sakamakon yadda al'umma ke tsoron pitbull, Mista Selebano ya ce zai bayar da karen nasa.
"Ba za mu iya rayuwa a duniya irin haka ba da kare zai iya cinye yara. Idan al'umma suna jin haushin su babu abin da zan iya. Amma barin shi ya tafi zai zama abu mai ciwo a gare ni da matata."
Sakamakon yadda irin yadda karnukan pit bulls ke far wa jama'a, tuni mutane irin su Mista Selebano suka sallama karnukansu.
Watanni uku bayan mutuwar Kekesto, akwai wani yaro ɗan wata 15 da ya rasu a asibti bayan pit bull ya kai masa hari a lardin Cape.
A Bloemfontein, karnuka 49 aka miƙa wa ƙungiyar dabbobi bayan wani kare ya kashe wani yaro mai suna Olebogeng Mosime.
A ranar da Kekesto ya rasu, wasu karnukan pit bull uku sun far wa wata yarinya a birnin Cape. Karnukan sun ji mata ciwo inda aka kai ta asibiti, inda al'ummar garin suka koma kan dabbobi suka rinƙa ƙona su da jifan su.