Leverkusen ta kammala Bundesliga ba tare da an doke ta ba

Bayer Leverkusen ta zama ta farko da ta buga kakar Bundesliga ba tare da rashin nasara ba a tarihi.

Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama tuni ta lashe kofin babbar gasar tamaula ta Jamus na kakar nan, wadda ta doke Augsburg 2-1 ranar Asabar, kenan ba ta yi rashin nasara ba a gabaki dayan wasannin.

Kenan Leverkusen ta yi wasa 51 a dukkan karawa ba tare da rashin nasara ba - tuni ta doke tarihin shekara 59 da aka kafa na yawan buga wasa a jere ba tare da rashin nasara ba

Ƙungiyar Jamus na bukatar nasara a wasa biyu nan gaba, domin ta lashe kofi uku a bana da ya hada da na Europa League da German Cup.

Za ta fafata da Atalanta a Europa League wasan karshe a Dublin ranar Laraba, daga nan za ta buga karawar karshe a German Cup da wadda take buga gasa mai daraja ta biyu a Jamus wato Kaiserslautern kwana uku tsakani.

Leverkusen ta doke tarihin wasa 49 a jere ba tare rashin nasara ba da Benfica ta Portugal ta kafa tsakanin 1963 zuwa 1965.

A kakar nan ta lashe wasa 28 daga karawa 34 a Bundesliga da cin kwallo 89 aka zura 24 a raga.

Rabonda a doke Leverkusen tun a bara a wasan karshe a Bundesliga, inda Bochum ta ci 3-0.

Idan har ta yi nasara a wasa biyun da suka rage mata, ya zama karawa 53 a jere kenan ba tare da rashin nasara a dukkan fafatawa.