Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rikicin Isra'ila da Iran: Wane ɓangare Rasha da China ke goyon baya?
- Marubuci, By Grigor Atanesian
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
- Lokacin karatu: Minti 6
Isra'ila ta kai hari kan shingayen sojoji na ƙasar Iran, a wani martani kan maƙamai masu linzami 200 da Tehran ɗin ta kai Isra'ila ranar 1 ga watan Oktoba.
Dakarun juyin-juya halin Iran sun ce hare-haren na a matsayin ramuwar gayya ne kan kashe shugabannin ƙungiyoyi biyu da take mara wa baya - Hamas da ke Gaza da kuma Hezbollah a Lebanon.
Hezbollah dai ta kasance tana kai hare-haren rokoki a faɗin iyaka da arewacin Isra'ila tun bayan da Hamas ta kai hari Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023.
Rikicin da ke yaɗuwa na sanya matsin lamba kan dangantaka tsakanin ƙasashe a faɗin duniya, ciki har da masu karfin iko guda biyu a duniya. Amurka ta ayyana goyon bayanta ga Isra'ila - Amma wane ɓangare Rasha da China ke goya wa baya kuma ta yaya za su mayar da martani?
Rasha: Ƙawance da jan hankali, amma idonta na kan Ukraine
Rasha da Iran ba ƙawaye ba ne na asali, sai dai ƙawancesu na ƙara kyautatuwa a baya-bayan nan kuma suna ƙoƙarin amincewa da wata yarjejeniya mai muhimmanci.
Lokacin da shugaba Vladimir Putin ya haɗu da sabon shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ranar 11 ga watan Oktoba dukkansu sun yi magana kan matsayarsu dangane da abubuwan da ke faruwa a duniya.
Iran ta kulla dangantaka da Rasha bayan fara yaƙi da Ukraine. Amurka da Birtaniya sun zargi Iran ɗin da bai wa Moscow makamai masu linzami da kuma ɗaruruwan jirage marasa matuki.
Iran ta musanta aika waɗannan maƙamai a hukumance, duk da cewa wani ɗan majalisar ƙasar ya ce an tura makaman ne domin shiga da kayan abinci zuwa Iran ɗin.
Sojojin saman Iran sun samu koma baya, bayan takunkumai na tsawon shekaru, kuma alamu na nuna cewa Rasha ta aika mata wani jirgi mai kai hari a baya-bayan nan, a cewar cibiyar tsaro ta Janes.
Bayan aika mata maƙamai, ana sa ran Moscow, bayan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Iran, za ta toshe duk wani ƙudiri na Majalisar Ɗinkin Duniya da ke sukar Iran da kuma adawa da duk wani amfani da karfi a kanta.
Ga Rasha, rikici a Gabas ta Tsakiya yana taimakawa wajen karkatar da hankalin yammacin Turai daga Ukraine, inda sojojin Rasha suka ƙara dannawa a fagen daga a 'yan watannin nan.
Sai dai fadar Kremlin za ta damu da irin tasirin da hare-haren da Isra'ila ke yi kan ɓangaren sufuri a cikin Iran.
Ƙasar Rasha na fuskantar manyan takunkumai daga ƙasashen duniya kuma tana da iyaka na hanyoyin sayar da man ta - ɗaya daga cikinsu shi ne zuwa Indiya ta Iran.
Tehran dai na goyon bayan jerin dakaru da ke yaƙi a Gabas ta Tsakiya, da suka haɗa da ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da kuma Hamas a Gaza. Da alama dai Moscow na ƙara kulla alaƙa da Hamas, tare da tawagar manyan shugabannin ƙungiyar da suka ziyarci Moscow a farkon wannan shekarar.
Sai dai duk da cewa Rasha na buƙatar Iran fiye da yadda take buƙatar Isra'ila, amma tana ƙoƙarin kiyaye alaƙa da ƙasashen biyu.
Isra'ila, yayin da take sukar yaƙin da Rasha ke yi a Ukraine da kuma ƙawancenta da Iran, zuwa yanzu ta ki ba wa Ukraine kayayyakin soji, duk da buƙatar da ta yi.
Kazalika Rasha za ta yi la'akari da cewa idan ta alaƙa ta ci gaba da wanzuwa tsakaninta da Iran, to Isra'ila za ta iya fara aika maƙamai zuwa Ukraine a matsayin martani - ko da yake wani babban yaƙi a Gabas ta Tsakiya zai iya takaita ikon Isra'ila na yin hakan.
Muradun Rasha da na Iran sun yi karo da juna a yankin Kudancin Caucasus, wanda ya zama cibiyar kasuwanci da makamashi mai muhimmanci ga Rasha karkashin takunkumi.
Azabaijan, ƙasa mafi arziki kuma mafi yawan al'umma a yankin, tana da iyaƙa da ƙasashen Rasha da Iran, kuma ta amince da samar da hanyar sufuri daga arewa zuwa kudu domin inganta hanyoyin mota, jiragen ƙasa da kuma jigilar kayayyaki tsakanin ƙasashen biyu.
Sai dai kuma ita ma Azabaijan na da alaƙar soji da Isra'ila, wadda ta daɗe tana bai wa sojojinta jiragen yaƙi marasa matuki da sauran manyan maƙamai.
A watan Satumban 2023, Azabaijan ta sake karɓe yankin Nagorno-Karabakh da ake takaddama a kai, abin da ya kawo karshen mulkin 'yan kabilar Armeniya na shekaru talatin.
Bayanan bin diddigin jirage da kamfanin dillacin labarai na AP ya yi nazari, sun nuna ƙaruwar jigilar maƙamai daga Isra'ila gabanin kai harin.
A baya ita ma Iran ta zargi Azabaijan da barin Isra'ila ta yi amfani da cibiyoyin soji wajen yi mata leƙen asiri - abin da Azabaijan ɗin ta musanta.
Ga Rasha, wannan dangantakar na iya nufin cewa dole ne ta yi takatsantsan idan wani harin da Isra'ila ta kai kan Iran ya matsa lamba kan dangantakarta da Azerbaijan.
Amma a cikin wannan rikici, kamar sauran wurare, Rasha ma za ta bi sahun China.
Moscow ta dogara sosai ga China a fannin fasaha, siyasa da kuma dabaru - musamman don shigo da kayan lantarki da kayan aiki na maƙamai. Lokacin da China ta bayyana damuwarta, za mu iya sa ran cewa Rasha za ta saurari batun.
China: Goyon bayan Iran ba tare da shiga cikin yaƙi tsundum ba
China da Iran sun daɗe suna alaƙa da juna - daga hulɗar diflomasiya zuwa dangantakar tattalin arziki.
Yanzu da Isra'ila ta kai hari kan Iran, ba a sani ko matsayar China za ta sauya.
Da alama Beijing za ta ci gaba da bai wa Iran goyon baya, yayin da take takatsantsan don kaucewa shiga cikin rikici da zai iya yaɗuwa.
Lokacin da aka nemi martani kan harin maƙami mai linzami da Iran ta kai kan Isra'ila ranar 1 ga Oktoba, kakakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar China ba ta ambaci Iran ba, amma ta ce Beijing na adawa da "ketare iyaƙar ƙasar Lebanon" - dangane da mamayar da Isra'ila ta yi a Lebanon. Ta bayyana Gaza a matsayin "tushen wannan tashin hankali a Gabas ta Tsakiya".
Irin wannan matsaya ta fito ƙarara a dukkan sakonnin Beijing, gami da kafofin yaɗa labaran gwamnati, tun bayan harin Hamas na 7 ga Oktoba - wanda China ba ta yi Alla-wadai da shi ba.
Beijing ta sha yin kira da a tsagaita wuta, sannan tana tallafawa Falasɗinawa da Lebanon ta fuskar diflomasiyya da taimakon jin-kai.
To amma ko wannan arangama tsakanin Isra'ila da Iran za ta haifar da ƙarin martani daga China?
China tana da ɗimbin hannayen jari a ƙasar Isra'ila, musamman a fannin samar da ababen more rayuwa da fasahohi, kuma tana kiyaye su a duk tsawon wannan rikici.
Tana son a guje wa haɗarin raba Isra'ila a matsayin abokiyar tattalin arzikinta ta hanyar daidaita kanta da Tehran.
A wannan zagaye na ramuwar gayya, Isra'ila ba ta far wa ɓangaren albarkatun man fetur na Iran ba, sai dai hakan ba yana nuna cewa ba za ta iya kai hare-hare kan waɗannan cibiyoyin ba a nan gaba.
China ta dogara kacokan kan shigo da ɗanyen mai, kuma kusan kashi 90 na ɗanyen man da Iran ke fitarwa na tafiya zuwa ƙasar, a cewar S&P Global, wani kamfanin mai fitar da bayanai kan harkokin kuɗi.
Idan harin ramuwar gayya na Isra'ila ya lalata kayayyakin albarkatun mai ta hanyar da ka iya shafar fitar da shi zuwa ƙasashen waje, to Beijing za ta iya ɗaga murya wajen yin Alla-wadai da abin da Isra'ila ke yi.
China ta kasance ƙasa ɗaya tilo da ke sayen man fetur daga Iran duk da takunkumin da Amurka ta kakaba mata, sannan ta kulla yarjejeniyar da ta mayar da hulɗar jakadanci tsakanin Iran da Saudiyya a shekarar 2023.
Kafafen yaɗa labarai sun ambato jami’an Amurka na cewa tuni Washington ta buƙaci China da ta yi amfani da karfinta a kan Tehran, alal misali, wajen tunkarar ‘yan tawayen Houthi da ke samun goyon bayan Iran a Yemen, waɗanda ke kai hare-hare kan jiragen ruwa a tekun Bahar Maliya.
Duk da cewa ana iya samun ƙarin buƙatu daga Washington, Tehran ba ta amsa wa Beijing, kuma da alama China ba za ta bi irin wannan buƙatar ba, musamman ganin ta fito daga Amurka.
Idan ba haka ba, China za ta ga haka a matsayin wata dama ta sukar Amurka, da kuma ƙara karfin tasirinta a duniya, ta hanyar nuna goyon baya ga buƙatar kafa kasar Falasɗinu ta hanyar da ta dace da ƙasashen da ke kudancin duniya.
Akwai haɗari ga China wajen kiyaye matsayinta na mai kallo a halin yanzu.
Bayan haka, Beijing na iya komawa ga sauran manyan masu fitar da mai, kamar Saudiyya ko Rasha idan buƙatar hakan ta taso.
Daga karshe, duk wani martani da muka ji daga birnin Beijing a cikin kwanaki masu zuwa, hakan zai nuna cewa da wuya ƙasar China ta kara shiga sosai cikin rikicin.