Ministan Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi da ke son Yahudawa su koma Gaza

Lokacin karatu: Minti 6

Ministan Isra'ila mai tsattsauran ra'ayi Bezalel Smotrich, mutum ne da ke yawan janyo ce-ce-ku-ce da ra'ayinsa na kishin Isra'ila da kuma matsayin siyasa mai karfi.

Jam'iyyarsa ta Zionism Party - tare da Jewish Power party ta ministan tsaro Itamar Ben-Gvir - na da muhimmanci ga ɗorewar gwamnatin haɗaka ta Firaiminista Benjamin Netanyahu, wadda ke ba shi tasiri mai ƙarfi a muhimman matakan da ake ɗauka a yaƙin Gaza.

Mista Smotrich shi ne ministan kuɗi kuma yana da muƙamin minista a ma'aikatar tsaro da ke ba shi iko kan kudurori da dama game da Gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

Yana goyon bayan Isra'ila ta mamaye Gaɓar Yamma da Kogin Jordan kuma yana adawa da tura agaji zuwa Gaza.

Ƙasashe da dama sun kakaba masa takunkumi ciki har da Birtaniya da Canada da Australiya da ke zarginsa da ingiza rikici kan Falasɗinawa. Netherlands ta zarge shi kan kudirinsa na ganin an kawar da Falasɗinawa.

A takaddamar baya-bayan nan, an gan shi a wani hoto yana murmushi, kusa da wani rubutu da ke nufin " mutuwa ga Larabawa" duk da cewa, a cewar kafafen yaɗa labaran Isra'ila, ma'aikatar kuɗi ta ce an gano kalmomin ne bayan da aka yaɗa hotunan kuma "kwata-kwata ba mu amince da haka ba."

'Munanan kalamai'

Mista Smotrich dai ya kasance ɗan majalisar dokoki a Isra'ila tun 2015 amma sai ya yi fice bayan zaɓen ƴan majalisa a shekarar 2022, lokacin da Mista Netanyahu ya sanya jam'iyyarsa cikin gwamnati mafi tsauri kuma mafi addini a tarihin Isra'ila.

Tsattsauran ra'ayin Mista Smotrich a yaƙin Gaza ya janyo suka daga ƙasashen duniya, a wasu lokutan kuma ya fusata jama'a.

Ya yi watsi da batun kai kayan jin-ƙai zuwa yankin inda ya ce yin hakan yana amfanar da Hamas ne kawai inda a Afrilu ya ce "ko alkama ba za a shigar Gaza ba".

A Agustan 2024, ya ce: "Babu wanda zai ƙyale mu mu hana farar hula miliyan biyu abinci, duk da cewa ana iya kare matakin har sai an mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su."

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce hakan ya ci karo da dokokin ƙasa da ƙasa da kuma dokar kare bil adama", inda ya ce jefa farar hula cikin yunwa da gayya laifin yaƙi ne". Ma'aikatar harkokin wajen Falasɗinawa ta kira hakan a matsayin amincewa da tsarin kisan kiyashi tare da yin alfahari da shi".

A Mayun 2025, Mista Smotrich ya ce za a lalata Gaza baki ɗayanta sannan mutanen yankin za su rasa makoma, ganin cewa ba su da wani abu a Gaza hakan zai sa su fara neman wasu wuraren domin ci gaba da rayuwa."

Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya yi Alla-wadai da kalaman.

Takunkumai

A watan Juli, Birtaniya tare da haɗin gwiwar Australia da Norway da Canada da New Zealand suka maka takunkumai a kan Mr Smotrich saboda "yawan kalaman tunzura da yake yi game da garuruwan yankin Falasɗinu" a gaɓar yamma da kogin Jordan. Birtaniya ta hana shi shiga ƙasarta sannan ta ƙwace wasu kadarorinsa da ke can.

Smotrich ya bayyana wa kafar Jerusalem Post cewa, "shi ko a jikinsa" amma "abu ne da yake da matuƙar girma a siyasar ƙasashe."

"Ƙasashe ƙawaye ba sa latfa wa kansu takunkumai ko da sun samu saɓani a tsakanin su. Wannan wuce iyaka ne."

A watan Yuli, ƙasar Netherlands ta hana shi shiga ƙasarta.

Sai ya rubuta a X cewa, "ban damu ba don an hana ni shiga Netherlands, abin da ya fi damuna shi ne yarana da jikokina da tattaɓa kunni da sauran Yahudawan duniya su samu sukunin gudanar da rayuwarsu a cikin Isra'ila cikin aminci."

"Na sadaukar da rayuwata domin tabbatar da tsaron Isra'ila, kuma zan cigaba da wannan fafatukar ko da kuwa duniya za ta juya min baya," in ji shi.

Buƙatarsu a Gaza

Mr Smotrich ƙwararren lauya ne, kuma ɗa ga wani malamin Yahudawa da ya taso a wani gari a gaɓar yamma da kogin Jordan, wanda kuma ya yi amannar cewa Allah ne ya ba Yahudawa yankin.

Ya daɗe yana kira ga Isra'ila ta mamaye yankin baki ɗaya, inda har ya ƙirƙiri wata ƙungiyar mai suna Regavim a shekarar 2006 domin fafutikar mamaye yankin.

Isra'ila ta gina gidaje kusan 160 da ke ɗauke da Yahudawa aƙalla 700,000 tun bayan da ta mamaye gaɓar yamma da kogin Jordan da Gabashin Jerusalem a yaƙin Gabas ta Tsakiya na 1967. Da waɗannan yankunan da Gaza ne mutanen Falasɗinu suke tunanin kafa ƴantacciyar ƙasarsu.

Isra'ila ta taɓa mamaye Gaza a 1967, amma sai ta ɗan ja baya a shekarar 2005, lamarin da Smotrich ya nuna rashin jin daɗinsa a kai.

Da yake magana a wajen wani taron ƙara wa juna sani, ya bayyana ƙarara cewa yana da burin ganin sun koma Gaza.

"A shekara 20 da suka gabata, muna tunanin abu ne da zai yi wahala, amma yanzu ina ganin abu ne mai yiwuwa."

Ya kwatanta Gaza da "yankin ba za a taɓa rabawa da Isra'ila ba."

Sai dai babu tabbacin me suke nufi da Falasɗinawa aƙalla miliyan biyu da suke zaune a a Gaza.

Amma Smotrich da Mr Ben-Gvir ya buƙaci ƴan zirin "bar yankin da kansu," amma masu kare haƙƙin ɗan'adam suna cewa hakan na nufin kisan mummuƙe ko ƙare dangi.

'Sabon babi' a gaɓar yamma da kogin Jordan

Nahum Barnea, mai rubutu na musamman a jaridar Isra'ila Yedioth Ahronoth, ya ce babban burin Smotrich shi ne zama ministan tsaron Isra'ila, inda zai samu ƙarfin kula da tsaro da tsare-tsaren kula da gaɓar yamma da kogin Jordan.

Burin faɗaɗa mamaye gaɓar yamma da kogin Jordan ya ƙaru a wannan gwamnatin, inda Smotrich da ministan tsaron ƙasar, Israel Katz suka sanar a watan Mayun 2005 cewa za su gina wasu garuru 22 a zirin, wanda shi ne mafi girma.

Wakilin jaridar Haaretz, Noa Shpigel, ya ce "ya fara fahimtar sabon babin da aka buɗe a Gaza, musamman "kuɗaɗen da aka ware" domin ayyuka a yankin Gaza.

"Suna da burin ganin gaɓar yamma da kogin Jordan ya koma a ƙarƙashin mulkin su."

Tun a baya ne Smotrich yake ƙalubalantar ƴancin Falasɗinu a gaɓar yamma da kogin Jordan da zirin Gaza da Gabashin Jerusalem."

Yaya ƙarfin ikon Smotrich?

Jam'iyyar Mr Smotrich mai tsattsauran ra'ayin kafa ƙasar Yahudawa zalla tana da kujera bakwai a majalisar ƙasar, sannan jam'iyyar Ben-Gvir ta Otzma Yehudit na da shida. Kafin 2025, haɗakar jam'iyyar da Netanyahu ke jagoranta ce ka da kujera 68 a cikin 120, amma da manyan jam'iyyu biyu suka fice daga haɗakar, sai kujerun suka koma 60, wanda hakan ya sa Netanyahu ya rasa rinjaye.

Mr Barnea ya ce, Smotrich "yana jagorantar wani ɗan sashe ne na mutanen ƙasar," amma kuma yana cikin waɗanda za su iya jawo tsaiko a haɗakar, wanda hakan zai iya tarnaƙi ga gwamnatin, "kuma ya san haka, shi ya sa yake yadda ya so."

"Yanzu alamu sun nuna Netanyahu ya fi tsoron Smotrich a kan sauran manyan hafsoshin tsaron ƙasar," in ji Mr Barnea.

Lahav Harkov, wakiliyar kafar Jewish Insider ta ce a bayyana yake cewa mafi yawan ƴan Isra'ila sun fi buƙatar a ɓullo da hanyoyin ceto ƴanuwansu da Hamas ke garkuwa da su da ma kawo ƙarshen yaƙin.

Amma ta ce Smotrich yana fitowa fili yana nuna cewa amfani da ƙarfin soji ya fi muhimmanci a kan batun ceto waɗanda ake garkuwa da su, "lamarin da ke ɓata ran Isra'ilawa da yawa."

Ms Shpigel ta ce Mr Smotrich da Mr Ben-Gvir suna da ƙarfin faɗa a ji a mulkin Mr Netanyahu, amma ta ce shi ne ya zaɓi "cigaba da mu'amala da su," domin a cewarta wasu jam'iyyun da ba sa tare da haɗakar sun ce za su kaɗa ƙuri'ar amincewa da aikin ceto waɗanda ake garkuwa da su.

BBC ta tuntuɓi Mr Smotrich domin jin ta bakinsa a kan wannan labarin, amma bai ce komai ba.