Ana 'sayar wa' mayaƙan al-Qaeda makaman da Amurka ta bari a Afghanistan

    • Marubuci, Yasin Rasouli
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Languages
    • Marubuci, Zia Shahreyar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Afghan Languages
  • Lokacin karatu: Minti 4

Makamai kusan rabin miliyan da Taliban ta gada daga dakarun sojin Amurka sun ɓace ko kuma an yi sumogar su zuwa wajen wasu ƙungiyoyi, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa BBC.

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta yi imanin cewa wasu daga cikin makaman ma suna hannun mayaƙan ƙungiyar al-Qaeda.

Taliban ta karɓe iko da makamai kusan miliyan ɗaya da sauran ƙananan kayan aikin soji - waɗanda akasarinsu na Amurka ne - bayan ta ƙwace mulkin Afghanistan a 2021, a cewar wani tsohon jami'in gwamnatin ta Afghanistan yayin hirarsa da BBC.

Ƙunshin makaman sun haɗa makaman harbi na Amurka, kamar manyan bindigogin M4 da M16.

Akasarinsu tsohuwar gwamnatin Afghanistan aka bai wa. Yayin da dakarun Taliban ke shirin ƙwace gwamnati a 2021, da yawan dakarun gwamnati sun miƙa wuya ko kuma sun gudu tare da barin makamansu da ababen hawa. Wasu makaman kuma dakarun Amurka ne suka bar su kawia.

Aƙalla rabin waɗannan makamai yanzu an bayyana su a matsayin "ɓatattu", kamar yadda Taliban ta shaida wa wani kwamatin zauren tsaro na MDD a birnin Doha na Qatar.

Cikin wani rahoto a watan Fabrairu, MDD ta bayyana cewa ƙungiyoyi ƙawayen al-Qaeda kamar Tehreek-e-Taliban Pakistan, da Islamic Movement of Uzbekistan, East Turkestan Islamic Movement, da Ansarullah ta Yemen na samun amfani da makaman da Taliban ta samu ko kuma suna sayen su a kasuwar bayan fage.

Da yake mayar da martani, mataimakin mai magana da yawun Taliban Hamdullah Fitrat ya faɗa wa BBC cewa gwamnatinsu tana ɗaukar kiyaye makamai da muhimmanci.

"Duka makamai ƙananana da manya na killace. Mun yi tir da rahotonnin da ke nuna cewa sun ɓace ko kuma an yi sumogar su," in ji shi.

Wani tsohon ɗanjarida a yankin Kandahar ya faɗa wa BBC cewa akwai kasuwar makamai maras sirri da ta dinga ci tsawon shekara guda bayan Taliban ta ƙwace mulki, amma yanzu ta koma kan shafukan zumunta na WhatsApp.

Adadin makaman da kwamatin Amurka na musamman a Afghanistan mai suna Sigar ya samu bayanansu sun yi ƙasa sosai da wanda majiyarmu ta bayyana, amma cikin wani rahoto a 2022 ya aminta cewa bai iya samun cikakkun adadi ba.

Sigar ya ƙara da cewa "akwai matsaloli game da aikin ma'aikatar tsaron Amurka na bi diddigin makamai a Afghanistan" tsawon shekara 10.

Kazalika Sigar ya soki ma'aikatar harkokin waje yana cewa: "Gwamnati ba ta ba mu cikakkun bayanai kuma sahihai ba game da makaman da ta bari." Sai dai ma'aikatar ta musanta wannan zargi.

Wannan lamari ne na siyasa kuma Shugaba Trump ya sha cewa zai ƙwato duka makaman da aka bari a Afghanistan. Ya ce an bar makaman da suka kai na dala biliyan 85 a can.

"Afghanistan na ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi sayar da makamai a duniya, kun san saboda me? Saboda suna sayar da makaman da muka bari," a cewar Trump lokacin taron ministocinsa na farko a wa'adi na biyu.

"Ina so na bincika wannan lamari. Idan akwai buƙatar mu biya su to shikenan, amma dai muna son dawo da kayayyakin aikinmu," in ji shi.

Sai dai an musanta alƙaluman kuɗin da Trump ya faɗa, saboda kuɗaɗen da aka kashe sun ƙunshi na horarwa da kuma albashi. Haka nan, Afghanistan ba ta cikin ƙasashe 25 na farko da suka fi sayar da makamai a bayanan da cibiyar Stockholm International Peace Research Institute ta fitar a 2024.

Mai magana da yawun Taliban, Zabihullah Mujahid, ya faɗa wa kafar talabijin ta ƙasar cewa: "Mun ƙwace waɗannan makamai ne daga hannun gwamnatin da ta shuɗe kuma za mu yi amfani da su wajen kare ƙasarmu daga barazana."

Taliban na yawan yin holen makaman Amurka, kamar a sansanin Bagram Airfield inda nan ne babban sansanin dakarun Amurka da Nato, kuma take nuna su a matsayin almomin nasara.

Bayan Amurka ta fice a 2021, ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta yi iƙirarin cewa makaman Amurka da aka bari an lalata su, amma kuma tuni Taliban ta gina rundunarta da wasu makaman da suka ba ta ikon samun galaba kan wasu ƙungiyoyin adawarta.

Ƙungiyoyin sun haɗa da National Resistance Front and Islamic State Khorasan Province, da kuma reshen ƙungiyar Islamic State a ƙasar.

Wata majiya daga tsohuwar gwamnatin ta Afghanistan ta shaida wa BBC cewa har yanzu akwai "ɗaruruwan" motoci masu sulke ƙirar Humvees, da jiragen helikwafta jibge a wuraren ajiyar makamai na Kandahar.

Taliban ta taɓa nuna irin waɗannan makamai a bidiyon farfaganda, amma ba za su iya kula tare da yin amfani da manyan makamai kamar jirgin helikwafta na Black Hawk saboda ƙarancin ƙwararru.

Amma kuma Taliban ta samu damar yin amfani da wasu makaman masu sauƙi, kamar Humvees.