Kotun Majistare ta ba da belin Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi

Bauchi Sheikh

Asalin hoton, Dutsen Tanshi Maslis Bauchi

Kotun Majistare a Bauchi ta bayar da belin fitaccen malamin Musuluncin nan na jihar, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.

A ranar Talata ne kotun majistare ta 1 ta yanke hukunci a kan buƙatar beli da lauyoyin fitaccen malamin mai janyo ka-ce-na-ce, suka nema bayan an gurfanar da shi a gaban kotu.

Tun farko a ranar Litinin ne, 'yan sanda suka shigar da Sheikh Idris Dutsen Tanshi ƙara gaban babbar kotun majistare ta ɗaya, inda suka tuhume shi da tada hankulan jama'a.

Sai dai malamin ya musanta zargin.

Lauyoyinsa sun shaida wa kotu cewa laifin da ake zargin malamin da aikatawa ba zai hana a bayar da shi beli ba, bisa tanadin dokokin Najeriya.

Daga nan sai alƙalin kotu ya sanya Talata a matsayin ranar da zai yanke hukunci game da buƙatarsu. Sannan ya ba da umarnin a ci gaba da tsare malamin a gidan yari kafin zaman kotu na gaba a washe gari.

Wata ƙungiyar addini mai suna Fityanul Islam ce ta kai ƙorafi kan malamin, tana zargin sa da furta miyagun kalamai a kan Annabi Muhammadu, sai dai Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi da magoya bayansa sun ce zargin ba gaskiya ba ne.

Waɗanne ne sharuɗɗan beli?

Barista Alƙassim Muhammad, ɗaya daga cikin lauyoyin Sheikh Idris Abdul'aziz ya shaida wa BBC cewa kotun ta bayar da belin malamin ne bisa wasu sharuɗɗa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Lauyan ya ambato kotu na cewa har yanzu dokokin Najeriya suna kallon malamin a matsayin wanda bai aikata wani laifi ba, don haka ba za a kama shi da laifi ba, har sai lokacin da aka tabbatar da da'awar da ake yi a kansa.

Ya ce sharaɗi na farko sai malamin ya gabatar da wani babban ma'aikacin gwamnati da ya kai matakin babban sakatare da kuma mai unguwa ko hakimi don su tsaya masa.

"Akwai kuma sharaɗin da za su gabatar da takarda, mallakan wani abu ko fili ko gida da ya kai naira miliyan biyar," in ji Barista Alƙassim.

A cewarsa, kotu ta kuma buƙaci sai mutanen da za su tsaya wa Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi, su gabatar da hotunansu ga rijistaran kotu, kafin sakin malamin.

Tun da farko, rahotanni sun ce magoya bayan malamin sun cika harabar kotun ta Mai shari'a Abdulfatah Shekoni duk da ɗumbin jami'an tsaro da aka jibge waɗanda suka riƙa taƙaita shigi da ficen cincirindon mutane.

Barista Alƙassim Muhammad sai an cika dukkan sharuɗɗan belin ne kafin a saki Sheikh Idris Abdul'aziz.

Za a ci gaba da sauraron ƙarar

Mai shari'a Abdulfatah Shekoni dai ya sanya ranar Laraba 24 ga watan Mayu, don ci gaba da zaman sauraron shari'ar ta Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi da kwamishinan 'yan sandan jihar Bauchi.

Shari'ar dai ta ja hankalin ɗumbin mutane a ciki da wajen jihar.

A farkon watan Afrilu ne fitaccen malamin na jihar Bauchi ya furta wasu kalamai da suka tayar da ƙura a tsakanin takwarorinsa malamai da mabiyansu.

Yanzu dai za a zuba ido a gani shaidun da ɓangarorin biyu za su gabatar a wannan ƙara, kafin kotu ta kai ga yanke hukunci.