Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya ta 'gargaɗi' Amurka kan bayanan kai hare-hare
Gwamnatin Najeriya ta nuna ɓacin ranta game da jerin gargaɗin da ofishin jakadancin Amurkar a Najeriya ke fitarwa kan barazanar kai hare-hare a wasu sasan ƙasar, har ma da Abuja.
A martanin da ta mayar ta bakin ministan yaɗa labaru Lai Mohammed, ranar Laraba, a Abuja, gwamnatin Najeriya ta ce mazauna Abuja da ma sauran yankunan ƙasar ba su cikin haɗari.
Lai Mohammed ya ce “Ina tabbatar wa al’ummar Najeriya da na ƙasashen waje da suke zaune a Najeriya cewa jam’ian tsaro na bakin ƙoƙarinsu kan matsalar tsaro”.
Ya ƙara da cewa “babu wata barazana, kuma babu baƙatar wani ya tayar da hankalinsa.”
Ministan ya ce ba Najeriya ce kawai take fama da matsalar tsaro ba, kasancewar kowace ƙasa na da irin nata matsalar tsaron da take fuskanta.
Inda ya kafa hujja da hare-haren da ɗaiɗaikun ƴan bindiga ke kai wa a makarantun Amurka.
Bayanin Lai Mohammed na zuwa ne bayan da a ranar Laraba, ofishin jakadanci Amurka a Najeriya ya bayar da umurnin kwashe wasu daga cikin ma’aikatansa daga ƙasar.
Haka nan a farkon mako ne Amurkar da takwararta Birtaniya suka fitar da sanarwar ankarar da ƴan asalin ƙasashensu game da yiwuwar kai hare-hare a sassan Najeriyar, har da Abuja, babban birnin ƙasar.
Gargaɗin ƙasashen Amurka da Birtaniya ya haifar da rufe makarantu
A cikin ƙarin bayani da ya yi, Lai Mohammed ya ce gargaɗin da Amurka ta fitar kan barzanar tsaro a ranar Lahadi ya haifar da rufe makarantu da dama, da kantuna.
Haka nan ya ce mutane da dama sun soke tafiye-tafiyen da suka shirya yi.
A cewar sa matsayar gwamnati ita ce – Jami’an tsaro suna aiki dare da rana wajen ganin sun shawo kan barazanar tsaro a ƙasar.
Abin da masana tsaro ke cewa
Wani masani kan tsaro a Najeriya Kabiru Adamu ya ce idan aka yi la’akari da tsari na diflomasiyya, bai kamata a rinƙa samun takun-saƙa tsakanin ƙasa da ƙasa ba kan irin waɗannan shawarwari da ofisoshin jakadanci ƙasashe ke fitarwa.
A cewarsa kafin duk wani ofishin jakadanci ya fitar da irin wannan bayani game da tsaron ƙasar da yake ciki, ya kamata ya tattauna da hukumomin tsaron ƙasar a kan duk wani bayani da ya tattara.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi Amurka, da Birtaniya su tattauna da jami'an gwamnatin Najeriya kafin fitar da wannan bayani.
Ya bayyana cewar wannan bayanai masu karo da juna da ke fitowa tsakanin ɓangarorin biyu sun nuna cewa ofisoshin jakadancin ba su bi matakan da suka kamata ba kafin fitar da bayanan nasu.
Wane hali ake ciki a Abuja?
Tun bayan gargaɗin da ƙasashen Amurka da Birtaniya suka fitar game da barazanar kai hare-haren ta'addanci a Najeriya, an ga ƙaruwar wuraren bincike a kan hanyoyin Abuja, babban birnin ƙasar.
Masu zirga-zirga kan titunan ƙasar sun bayyana yadda aka samu yawaitar wuraren bincike na sojoji a manyan hanyoyi, da mahaɗa, ko kuma hanyoyin shiga unguwannin birnin.
Sojojin kan tsayar tare da bincika ababen hawa kafin barin su su wuce, wani abu da ya janyo cunkoson ababen hawa a hanyoyi daban-daban na birnin.
Najeriya dai na fuskantar barazanar tsaro a ɓangarori da dama na ƙasar.
Dakarun ƙasar na yaƙi da mayaƙan Boko Haram a arewa-maso-gabashin ƙasar, sannan suna ƙoƙarin shawo kan matsalar ƴan bindiga masu garkuwa da mutane a arewa-maso-kudancin ƙasar.