Wadi al-Salam: Makabartar Musulmai mafi girma a duniya

Lokacin karatu: Minti 3

Maƙabartar Wadi al-Salam da ke birnin Najaf a ƙasar Iraqi, ita ce maƙabartar Musulmai da ta fi kowace maƙabarta girma a duniya.

An binne sama da mutum miliyan shida a cikinta, inda wasu ƙaburburan da ke ciki suka samo asali tun ƙarnuka da suka gabata.

Mafi yawan wadanda ake binnewa da kuma masu ziyara a maƙabartar mabiya aƙidar Shi'a ne.

Maƙabartar na da girman da ya kai eka 1,485.5, kuma wuri ne da ke karɓar baƙuncin miliyoyin Musulmai masu ziyara a kowace shekara.

Ana ganin cewa kusancin maƙabartar da hubbaren Ali ibn Abi Talib, sahabin Annabi Muhammad na daga cikin abubuwan da suka ƙara ɗaukaka darajar maƙabartar.

Imam Ali shi ne halifan Annabi Muhammad na huɗu a mahangar Ahlussunnan, amma mabiya mazhabar Shi'a na ɗaukar sa a matsayin na farko daga cikin imamansu 12.

Wannan ya sanya akasarin mabiya Shi'a na Iraqi kan buƙaci a binne su a maƙabartar, kuma sanadiyyar sauƙin sufuri a zamunnan baya-bayan nan, wasu mabiya Shi'a daga ƙasashen duniya kan so a binne su a maƙabartar.

Tsarin maƙabartar ya kasance cakuɗuwa ce ta gine-ginen hubbarai irin na zamanin baya, da hanyoyi masu tsuku da suka ratsa ta cikinta da kuma wasu wurare da ake yi wa kallon masu tsarki.

Me ya sa ake kiran maƙabartar Wadi al-Salam?

Ana kiran maƙabartar da sunan Wadi al-Salam, wato 'kwarin aminci' ne saboda dalilai na tarihi da dama.

Dalilai na addini: Ana yi wa maƙabartar ɗaukar mai daraja, tare da imanin cewa wa danda ke kwance a cikinta na cikin rahama.

Alaƙa da Imam Ali: Maƙabartar tana maƙwaftaka da kabarin Imam Ali bin Abi Talib a birnin Najaf, wanda hakan ya sa Musulmai, musamman mabiya aƙidar Shi'a ke girmama ta kuma suke kwaɗayin ganin an binne su a cikinta.

Girma: Maƙabartar ta kasance mafi girma a duniya, inda ta mamaye wuri mai girman gaske, ƙunshe da miliyoyin ƙaburbura, inda ta zamo tamakra wani birni na mamata.

Ziyara: Masu ziyara zuwa birnin Najaf, mai tsarki ga mabiya aƙidar Shi'a - sukan bi ta cikin maƙabartar tare da karanta Fatiha da kuma yin addu'o'in samun rahama ga waɗanda ke kwance, lamarin da ya mayar da wurin tamkar wuri na ziyarar ibada.

Waɗannan dalilai ne suka sanya tuntuni aka yi wa wurin laƙabi da 'kwarin aminci' tun asali, kuma ake ci gaba da kiranta da hakan har yanzu.

Tarihin kafuwar maƙabartar Wadi al-Salam

Maƙabartar ta samo asali ne tun kafin zuwan addinin Musulunci a lokacin Annabi Muhammad, inda tun kafin wancan lokaci ake binne mutane a wurin.

Wuri ne mai muhimmanci wanda ke karɓar baƙuncin masu bincike na kimiyya da masana addini, musamman mabiya Shi'a daga sassa daban-daban na duniya.

Wadi al-Salam na da ƙofofi da dama da ake bi wajen shigar ta, inda hakan ke sauƙaƙe zirga-zirga ga masu ziyara, kuma yawancin waɗannan ƙofofi na ƙaruwa ne bisa faɗaɗar maƙabartar.

A shekara ta 2016 ne Hukumar kula da ilimi da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta ayyana maƙabartar a matsayin ɗaya daga cikin wuraren tarihi na duniya.

Ƙalubalen da maƙabartar ke fuskanta

Ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da maƙabartar ke fuskanta shi ne ƙaruwar mutane da ake binnewa a lokacin yaƙi.

Misali, a lokacin da aka yi fama da rikicin ƙungiyar ISIS a Iraqi, yawan mutanen da ake binnewa a kowace rana a maƙabartar ya ɗaga zuwa 150 ko 200 a kowace rana, daga gawa 80 zuwa 120 da aka saba.

Wannan ya sanya wuraren binne sabbin mamata ya yi ƙaranci.

Farashin binne mamaci

Farashin binne mamaci a maƙabartar Wadi al-Salam ya danganta ne da lokaci da kuma halin da ake ciki na zaman lafiya.

Ya zuwa farkon shekara ta 2025, kudin sayen filin binne mamaci mai girman murabba'in mita 25 ya kai miliyan biyar na kuɗn ƙasar Iraqi, wato kimanin dala 4,100, inda hakan ya nunka farashin da ake biya a lokutan da ake zaman lumana sosai.