Yadda jefa abinci ta sama ya janyo cece-ku-ce a Gaza

United States Central Command and Royal Jordanian Air Force Conduct Combined Airdrops of Humanitarian Aid Into Gaza

Asalin hoton, USAF/Reuters

Bayanan hoto, Jiragen Amurka ƙirar C-130 sun jefa fiye da abinci 38,000 ta gaɓar teku a Gaza
    • Marubuci, Luis Barrucho & BBC Arabic
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service

Amurka ta ce ta jefa ƙunshin abinci na agaji a Gaza a karon farko, inda jiragen sama suka rika jefo abinci fiye da 30,000 ta jiragen sama, lamarin da ya janyo cece-ku-ce a tsakanin ƙungiyoyin agaji da mutanen da ke ƙasa.

Wannan shirin da aka kai tare da sojojin sama na ƙasar Jordan, shi ne karon farko da shugaban Amurka Joe Biden ya sanar, kuma ya faru ne bayan an kashe aƙalla mutane 112 a yayin da jama'a suka yi ta tururuwar zuwa ga ayarin motocin agaji a wajen birnin Gaza ranar Alhamis.

Sojojin Isra'ila sun ce akasarin Falasɗinawa sun mutu sakamakon turmutsitsin da aka samu amma jami'an kiwon lafiya na yankin sun ce waɗanda suka jikkata da aka kai asibitoci sun samu raunuka sanadin manyan harsasai. Isra'ila ta ce tana gudanar da bincike.

Jefa abinci ta jirgin sama da Amurka ta yi ya zo ne a daidai lokacin da wani babban jami'in Amurka ya ce tsarin yarjejeniyar tsagaita wuta na tsawon makonni shida a Gaza yana aiki.

Mene ne adadin agajin da aka bayar kuma me ya sa ya janyo cece-kuce?

Jirgin na Amurka ƙirar C-130 ya jefa abinci kusan 38,000 a gaɓar teku da ke kudu maso yammacin Gaza a ƙoƙarin da sojojin saman Amurka da na Jordan suka yi, in ji wata sanarwa da rundunar Amurka ta fitar.

Abincin ya ƙunshi adadin sinadarai masu bada kuzari na rana ɗaya a cikin rufaffen fakiti, a cewar jami'an Amurka da kamfanin dillancin labarai na AP ya ruwaito.

Sauran ƙasashe da suka haɗa da Birtaniya da Faransa da Masar da kuma Jordan a baya sun aika da agaji zuwa Gaza, amma wannan shi ne karon farko da Amurka ta yi.

Shugaba Biden ya kuma ce Amurka za ta "ruɓanya ƙoƙarinmu na buɗe hanyar teku, da faɗaɗa isar da kayayyaki ta kan tudu".

Ana isar da agaji zuwa Gaza ta hanyoyi da Isra'ila da Masar ke iko a kai. Yawancin su an rufe su tun da yaƙin ya fara, inda yake wahala a kai agaji a manyan motoci cikin Gaza.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce kashi huɗu na mutanen Gaza miliyan 2.3 na fuskantar yunwa.

'Kayan agajin ba su wadatar ba’

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani mazaunin Gaza, Ismail Mokbel, ya shaida wa sashen larabci na BBC cewa kayan da aka jefa ta sama a ranar Juma'a sun ƙunshi wake da gyaɗa da dangoginsu da kuma wasu kayayyakin buƙatu na mata.

Wani mutum, Abu Youssef, ya ce bai samu komai ba bayan an jefa kayan agajin ta sama a kusa da asibitin al-Shifa da ke birnin Gaza.

Ba zato ba tsammani, lokacin da muke kallon sama, sai muka ga kayan agaji da ake jefowa daga sama ta lema. Don haka, mun kasance a wurin da muke har sai da agajin ya sauka kimanin mita 500 daga gare mu. Akwai mutane da yawa, amma taimakon kaɗan ne, don haka ba mu iya samun komai ba.”

Agajin ba zai isa ɗimbin 'yan ƙasa da ke fuskantar ƙarancin duk wani abu mai mahimmanci ba, in ji Mista Mokbel.

“Dubban ‘yan kasar sun ga taimakon ya faɗo musu… Kuma a lokacin da daruruwa ko dubbai ke jira a irin waɗannan wuraren, mutane 10 zuwa 20 ne kaɗai ke samun kaya, yayin da sauran ke komawa ba tare da komai ba. Sai dai abin takaicin shi ne, wannan hanya ta jefo abinci daga sama ba ita ce hanya mafi dacewa ta kai kayan agaji zuwa yankin arewacin Gaza ba,” in ji shi.

"Gaza na buƙatar agaji ta hanyar ƙasa da ta ruwa maimakon yadda ake yi, don hakan ba zai biya buƙatar al'umma ba."

A Jordan aircraft drops humanitarian aid into Gaza, Northern GazaMOHAMMED SABER/EPA-EFE/REX/Shutterstock

Asalin hoton, MOHAMMED SABER/EPA-EFE/REX/Shutterstock

Bayanan hoto, Sauran ƙasashe da suka hada da Birtaniya da Faransa da Masar da kuma Jordan a baya sun aika da agaji zuwa Gaza, amma wannan shi ne farkon da Amurka ta yi

Tsada da haɗari wajen jefa agaji ƙasa

Da farko an yi aiki da shi a lokacin yaƙin duniya na biyu don samar da keɓaɓɓun sojoji a ƙasa, jiragen sama sun zama kayan aiki mai mahimmanci na taimakon jin ƙai tare da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fara amfani da su a cikin 1973.

Duk da cewa ana ɗaukar su a matsayin "makomar ƙarshe", kawai a yi amfani da su "lokacin da duk wasu matakai suka gaza" kamar yadda Hukumar samar da Abinci ta Duniya (WFP) ta ce a cikin rahoton 2021. Sudan ta Kudu ita ce wuri na ƙarshe da WFP ta jefa agaji ta hanyar amfani da jiragen sama.

Jan Egeland, shugaban kungiyar kula da ƴangudun hijra ta Norwegian Refugee Council, ya shaida wa BBC cewa, "kai agaji ta hanyar amfani da jiragen sama na da tsada, da hadari kuma yawanci kan kai ga mutanen da ba daidai ba su samu tallafin," in ji Egeland, bayan da ya dawo daga ziyarar kwanaki uku da ya kai baya-bayan nan zuwa Gaza.

Kai agaji ta jiragen sama ya fi tsada sau bakwai idan aka kwatanta da taimakon da ake bayarwa a ƙasa saboda farashin da ya shafi jiragen sama da man fetur da ma'aikata, in ji WFP.

Bugu da ƙari, abubuwa kaɗan ne kawai za a iya isar da su a kowane jirgin sama - idan aka kwatanta da abin da ayarin motoci za su iya shigo da su, da kuma muhimmiyar haɗin gwiwar ƙasa da ake buƙata a cikin yankin da ake bayarwa, in ji WFP.

Ƙungiyar agaji ta duniya, ICRC ita ma ta jaddada mahimmancin sa ido wajen raba kayan agaji don hana mutane shiga cikin kasada ta hanyar amfani da abubuwan da ba su dace ba, in ji wani rahoto na 2016 lokacin da ake jigilar kayan agaji zuwa Syria a lokacin yaƙin basasar ƙasar.

"Isar da nau'ikan abinci na kwatsam da rashin sa ido ga mutanen da ke fama da rashin abinci mai gina jiki ko ma yunwa na iya haifar da babban haɗari ga rayuwa. Ya kamata a auna waɗannan haɗuran ko hanyar isar da komai ta iska, ko jinkirin rarraba kayan ta ƙasa ke iya haifarwa," in ji ta.

WFP ta ƙara da cewa, ana iya sauke agajin daga sama ta hanyoyi daban-daban, daga kimanin mita 300 zuwa mita 5,600 a yankunan da ake fama da rikici, don haka, tabbatar da inganci hanyoyin da aka bi wajen ƙunshe kayan na da matuƙar muhimmanci don tabbatar da fakitin ya jure idan an wulla ƙasa.

A cewarsu, ya kamata wuraren da aka sauke kayan su kasance manyan wuraren, ba kasa da filin wasan ƙwallon ƙafa ba, wanda shi ne dalilin da ya sa ake yawan kaiwa gaɓar tekun Gaza.

Sai dai, a wasu lokuta agajin na faɗowa cikin teku ko kuma iska ta ɗauka zuwa Isra'ila, a cewar bayanan mutanen yankin.

A U.S. Air Force loadmaster releases humanitarian aid pallets of food and water over Gaza

Asalin hoton, USAF/Reuters

Bayanan hoto, Abincin ya ƙunshi adadin sinadarai masu bada kuzari na rana ɗaya da aka ƙulle cikin fakiti

Akwai buƙatar a tsagaita wuta

Wani mazaunin Gaza Samir Abo Sabha ya shaida wa BBC Arabic cewa yana ganin ya kamata Amurka ta ƙara ƙaimi tare da matsa wa Isra'ila lamba kan tsagaita wuta.

“Don haka a matsayina na ɗan Gaza, waɗannan kaya ba su da wani amfani; Abin da muke so [shi ne] Amurka ta matsa wa Isra'ila lamba a tsagaita wuta da kuma daina bai wa Isra'ila makamai da makamai masu linzami."

Wasu ƙungiyoyin jin ƙai sun yi na'am da wannan ra'ayi.

A makon da ya gabata, ƙungiyar agaji ta Oxfam ta soki matakin da gwamnatin Biden ta sanar, tana mai cewa jiragen saman "za su fi taimakawa wajen sauke laifuffukan manyan jami'an Amurka waɗanda manufofinsu ke taimakawa wajen cin zarafi da kuma haɗarin yunwa a Gaza", Scott Paul, wanda ke jagorantar aikin oxfam a Amurka ya ce cikin wata sanarwa.

Amma, yayin da matsalar jin ƙai ta zurfafa a yankin Falasdinu, wasu suna jayayya cewa dole ne a isar da abinci a wurin "ta kowace hanya".

"Muna buƙatar mu kawo abinci a Gaza ta yadda za mu iya. Ya kamata mu kawo ta bakin teku ... Ya kamata mu sanya jiragen ruwa a gaban Gaza," José Andrés - wani mai dafa abinci kuma wanda ya kafa Cibiyar cin Abinci ta World Central Kitchen, wadda ke aika abinci zuwa Gaza kuma 'yan Democrat suka zaɓa don samun kyautar Nobel a farkon wannan shekara - ya shaida wa gidan rediyon Amurka ABC.

Dubawa - Alexandra Fouché