Abin da ya sa za a fara bai wa mata masu zaman kansu hutun haihuwa da fansho a Belgium

Mel ta ce sabuwar dokar za ta inganta rayuwarta.
Bayanan hoto, Mel na ɗaya daga cikin matan da suka ce sabuwar dokar za ta inganta rayuwarta.
    • Marubuci, Sofia Bettiza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gender and identity correspondent, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gargaɗi: Labarin na ƙunshe da bayanai na batsa.

“Dole na yi sana'ata, alhalin ina ɗauke da cikin wata tara,'' in ji Sophie, wata mace mai zaman kanta a Belgium''.

''Na kasance ina kwanciya da maza mako guda kafin na haihu''.

Ta kasance tana wannan sana'a, yayin da take kula da 'ya'yanta biyu - wanda hakan na matuƙar ''ba ta wahala''.

A lokacin da Sophie (wadda ba sunanta ne na ainihi ba) za ta haifi ɗanta na biyar, sai da aka yi mata tiyata, kuma likita ya ce tana buƙatar hutu na mako shida. Amma sai ta ce hakan ba mafita ba ce, inda ta gaggauta komawa bakin aiki.

“Ba zan iya zama ba, saboda ina buƙatar kuɗi.”

Rayuwarta za ta iya inganta inda ana biyan ta kuɗin hutu, da wanda take yi wa aiki zai biya ta.

A ƙarƙashin sabuwar dokar a Belgium - wadda ita ce irin ta ta farko a faɗin duniya - za a kula da wannan.

Za a riƙa bai wa mata masu zaman kansu kwantiragin aiki a hukumance da ya ƙunshi inshorar lafiya da kuɗin fansho da hutun haihuwa da hutun rashin lafiya. A taƙaice dai za a ɗauki sana'ar kamar sauran ayyukan gwamnati.

“Wannan dama ce muka samu domin mu rayu kamar kowa,” in ji Sophie.

A faɗin duniya akwai aƙalla mata masu zaman kansu miliyan 52, kamar yadda ƙungiyar Mata Masu Zaman Kansu ta Duniya ta bayyana.

A shekarar 2022 aka halasta sana'ar karuwanci a Belgium, kuma ƙasashen duniya da dama suka halarta sana'ar ciki har da Turkiyya da Peru. Amma bai wa masu sana'ar wasu haƙƙoƙin kwantiragi shi ne na farko irin sa a duniya.

“Wannan muhimmin abu ne, kuma muhimmin mataki ne da muka gani a duniya,'' in ji Erin Kilbride, wani mai bincike a ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta HRW.

''Muna buƙatar kowace ƙasa a duniya ta yi irin wannan doka.''

An gudanar da zanga-zangar neman ɓullo da dokokin kyautata wa mata masu zaman kansu bayan ƙarewar annobar Covid.

Asalin hoton, (UTSOPI

Bayanan hoto, An gudanar da zanga-zangar neman ɓullo da dokokin kyautata wa mata masu zaman kansu bayan ƙarewar annobar Covid.
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To sai dai masu suka sun ce wannan sana'a na haifar da safarar mata da cutar da su - wanda kuma wannan doka ba za ta hana ba.

“Dokar na da hatsari, saboda tana ƙoƙarin inganta sana'ar da a mafi yawan lokuta ke cike da abubuwa na tashin hankali,'' in ji Julia Crumière, wata mai aiki da ƙungiyar Isala - da ke taimaka wa mata masu zaman kansu a kan titunan Belgium.

Mafi yawan masu sana'ar tilas ce ta sa suke yin ta, kuma dokar ba ta yi la'akari da hakan ba, a cewar masu fafutikar.

Mel ta fara shiga sana'ar a lokacin tana shekara 23 - saboda tana buƙatar kuɗi, kuma nan take ta fara samun kuɗi fiye da yadda ta zata.

A lokacin ta shigar sana'ar da ƙafar dama, amma samun labarin hatsarin kamuwa da cutakan da ake ɗauka ta hanyar jima'ai ya rage mata ƙarfin gwiwa a sana'ar.

A yanzu Mel kan guje wa kwastomomin da ta ji ba su kwanta mata a rai ba, hakan na nufin ba da kowa take hulɗa ba.

“A yanzu zan iya kallon kwastomana, in ce masa ga yadda nake so ya mu'amalanceni, ko in ce ya saɓa wata ƙa'ida, saboda a yanzu ina da kariya a hukumance.''

Victoria tsaye a gaban kyamara sanye da rigar sanyi a gaban wasu bishiyoyi
Bayanan hoto, Victoria na ɗaukar sana'ar zaman kai a matsayin aikin hidimta wa al'umma

Belgium ta ɗauki matakin ne bayan watannin da aka ɗauka ana zanga-zanga a 2022, domin neman ƙasar ta tallafa wa masu sana'ar barikanci bayan ƙarewar annobar korona.

Ɗaya daga cikin na gaba-gaba a wancan lokaci ita ce Victoria, shugabar ƙungiyar mata masu zaman kansu a Belgium, wadda kuma ta shafe shekara 12 tana sana'ar

A gare ta wannan yi wa kai ne. Victoria na ɗaukar sana'ar barikanci a matsayin aikin hidimta wa al'umma, inda jima'i ya zama kashi 10 cikin 100 na abubuwan da take yi.

“Nakan bai wa mutane kula, na saurari labarai, na ci abinci da halartar gidan rawa,'' in ji ta.

Amma kasancewar kafin 2022, sana'arta haramtacciya ce ta shiga ƙalubale masu yawa. Takan yi aiki a yanayi maras kariya, kuma ba ta da zaɓi ga kowane irin kwastoma, sannan kuma ƙungiyarta kan yanke wani babban ɓangare na kuɗaɗen da take samu.

A taƙaice, Victoria ta ce wani kwastomanta da suka shaƙu, ya taɓa yi mata fyaɗe.

Ta ce ta je ofishin 'yansanda, inda ta ce wata jami'a mace ba ta yi mata ''da daɗi ba''.

"Ta faɗa min cewa, wai ba ta yadda za a yi wa mace mai zaman kanta fyaɗe. Ta sa na fara ganin laifin kaina, saboda sana'ar da nake yi.'' Victoria ta fice daga ofishin tana kuka.

Da dama cikin masu zaman kansu da muka tattauna da su, sun bayyana mana cewa an taɓa tilasta musu yin abin da ba su da ra'ayi.

Saboda haka, Victoria ke ganin sabuwar dokar za ta inganta rayuwarsu.

“Idan babu wata doka, sana'ar haramtacciya ce kenan, babu wasu ƙa'ido da za su taimaka maka. Wannan dokar za ta ba mu kariya sosai.''

Alexandra da Kris sun ce suna hidimta wa kwastomomisu yadda ya kamata.
Bayanan hoto, Alexandra da Kris sun ce suna hidimta wa kwastomomisu yadda ya kamata.

A ƙarƙashin sabuwar dokar, kawalai na da damar gudanar da ayyukansu, idan za su bi ƙa'idojin dokar. Duk wanda aka samu da aikata wani babban laifi ba za a ƙara barin shi ya ɗauki ma'aikata masu sana'ar ba.

“Ina ganin da dama daga cikin kawalan za a rufe sana'arsu, saboda da dama daga cikinsu na da tarihin aikata manyan laifuka,'' in ji Kris Reekmans.

Shi da matarsa na da wani ƙaramin gida da suke ajiye mata masu zaman kansu a garin Bekkevoort, domin haɗa su da kwastomomi.

A lokacin da muka ziyarci gidan ya cika maƙil da kwastomomi, ba kamar yadda muka yi tsammanin samu ba a ranar Litinin da safe.

An nuna mana ɗakunan da aka ƙawata da gadajen tausa da sabbin tawul-tawul da rigunan kwanciya da manyan bahunan wanka da wuraren ninƙaya a cikin gidan.

Kris da matarsa sun ɗauki mata masu zaman kansu 15 aiki, kuma suna alfahari da kansu kan yadda suke mu'amalantarsu da ba su kariya da kuma biyan su albashi mai kyau.

“Ina fatan za a rufe irin waɗannan sana'o'i na mutanen da ba sa biyan abin da ya kamata, amma waɗanda suka ɗauke ta da gaskiya za su ci gaba da aiki,'' in ji Reekmans.

Ana ɗaukar Mel hoto domin tura wa kwastomomi.
Bayanan hoto, Mel ta yi amanna cewa wannan dokar za ta tallafa wa mata

Amma Julia Crumière ta ce mafi yawan matan da ta taimaka mawa, sun ce suna son barin sana'ar, domin samun wata ''sana'ar daban'' - ba wai haƙƙin ma'aikata ba.

A ƙarƙashin sabuwar dokar, za a ƙawata kowane ɗakin mace mai zaman kanta (inda take aiwatar da sana'ar) da wata ƙararrawa da mace za ta danna idan tana fuskantar cin zarafi daga kwastomanta.

Amma dai Julia ta yi imanin cewa hakan ba zai yi wani tasiri ba wajen kare mata masu zaman kansu.

“A wace sana'a ce kake buƙatar ƙararrawar ankararwa? Ba tsohuwar sana'a ba ce, tsohuwar cutarwa ce a duniya."

Har yanzu duniya na ci gaba da samun rarrabuwa kan yadda za a gudanar sana'ar zaman kai . Amma a ganin Mel fito da matsalar fili zai taimaka wa mata masu sana'ar.

“Ina alfaharin cewa a yanzu Belium ta shiga gaba, don haka ina da makoma mai kyau.''

Mun sauya wasu sunayen domin kare su.