Yaƙin Isra'ila da Gaza: 'Na gaji, Ba mu san inda za mu je ba'

.

Asalin hoton, getty images

Fararen hular da ke gujewa mummunan rikicin arewacin Gaza sun bayyana yadda suka riƙa ganin ruɓaɓɓun gawarwaki da tankokin yaƙin da suka lalace a kan hanyarsu ta zuwa kudancin yankin.

Rundunar sojin Isra’ila (IDF) sun riƙa wallafa sanarwa a shafukan sada munuta tare da ajiye takardun da ke kiran mazauna yankin da su yi amfani da hanyar Salah al-Din a tsakanin wasu lokuta.

Yaya wanan tafiyar take?

Sashen bin diddigi na BBC ya nazarci wasu bidiyo, tare da jin bahasi daga bakin shaidun ganin gani da ido tare da yin nazarin hotunan tauraron ɗan’adam domin sanin gaskiyar abin da ya faru.

Kafin a fara yaƙin, akwai kimanin fiye da mutum miliyan guda a arewacin Gaza.

Amma yanzu yankin ya fuskanci ruwan boma-bomai, yayin da dakarun sojin ƙasa na Isra’ila ke yaƙar Hamas, bayan harin da ta kai cikin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Hanyar Salah al-Din, ita ce babbar hanyar da ta haɗa Isra’ila ga Gaza, kuma dakarun sojin Isra’ila sun shawaraci fararen hula su yi amfani da ita don komawa kudancin Gaza.

Hanyar ta zarta kilomita 14 daga can ƙuryar Gaza zuwa Wadi Gaza, wani kwari da sojojin Israila suka yi amfani da shi wajen raba tsakanin kudu da arewacin Gaza.

Rundunar sojin Isra’ila ta ce fararen hula za su fi samun kariya a kudancin Gaza, duk da cewa tana ci gaba da kai hare-hare ta sama a yankin.

A ranar Laraba Ahmed Zayadah ya shaida wa BBC abubuwan da ya gani a lokacin tafiyar da ya yi daga arewa zuwa kudancin Gaza.

Ya yi tafiya ne daga gidansa da ke gundumar al-Nasr a yankin arewacin Gaza.

Yayin da yake riƙe da wani ƙaramin yaro, ya ce “na yi matuƙar gajiya. Ba mu san abin da za mu yi ba, ba mu san inda za mu je ba. Wajen wa za mu je? Wa za mu faɗa wa? Domin ya cece mu.

Mahmoud Ghazzaawi ya bar gidansa a al-Zeitoun da ke arewaci Gaza, saboda yawaitar hare-hare.

Ya ce ya bar gidansa da tsakar rana, inda ya yi tafiyar sa’o’i biyar, ba tare da sanin inda zai je ba.

"Akwai gawarwakin mutane yashe a gefen titi, muna fata Allah ya gafarta musu,” in ji shi.

.
Bayanan hoto, Ahmed Zeyadah ya yi tafiya da ƙafa daga Salah al-Din ɗauke da ƙaramin ɗansa
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An ga mutane da dama suna tafiyar ƙasa. Majalisar Dinkin Duniya ta ce sojojin Isra'ila sun tilasta wa mutane barin ababen hawansu a wajen yankin kudancin birnin Gaza.

Daga nan ne mutanen ke tafiyar ƙafa ta kusan kilomita 20 ga waɗanda suka taho daga arewacin Gaza mai nisa.

Daya daga cikin waɗanda suka baro arewqacin Gaza ya shaida wa masu sanya idanu na MDD cewa "Na ga ɓarna mai yawan gaske a kan hanyata, na ga tankokin yaƙin Isra'ila da sojojinsu a gefen titi a gabashin yankin, kusa da Netzarim, amma ba su yi mana komai ba".

"Na ga gawarwaki 'yan ƙalilan da kuma sassan jikin gawarwakin a kan hanya."

A wani bidiyon da aka wallafaa shafin Telegram ranar Talata, an ga wata mata na magana kan gawarwakin da ta gania kan hanyarta ta zuwa Kudancin Gaza.

Ta ce ta yi ta neman ɗanta a kusa da marabar Netzarim, ta kuma bayyana yadda ta ga gawarsa cikin gawarwakin mutanen da suka mutu a kan hanyarsu ta zuwa kudancin Gaza.

"Na ga tankokin yaƙin Isra'ila, amma ban damu ba, na yi ta dubawa kawai sai na ga gawar ɗana. Na gane gawar ne ta hanyar gane belet ɗinsa, da wayarsa", kamar yadda ta faɗa a cikin bidiyon.

BBC ta zanta da wani ɗan jaridar yankin wanda ya ce ya gane matar, yana mai cewa ta je asibitin Al Aqsa da ke Deir al-Balah, a tsakiyar Gaza, ranar Talata inda ta kai rahoton mutuwar ɗanta, an kuma yi masa jana'iza a wannan rana, kamar yadda ya ce.

BBC ba ta ga bidiyon ko hotunan gawarwakin da aka yi iƙirarin gani a babban titin Salah al-Din a 'yan kwanakin nan.

Mun kuma tuntuɓi dakarun sojin Isra'ila kan rahoton ganin gawarwaki a gefen titin

b
Bayanan hoto, An ga wannan matar cikin wani bidiyo da aka wallafa a shafin Telegram, tana cewa ta ga gawar ɗanta a gefen titin Salah al-Din

Mutane na ɗaga fararen tutoci

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan mutum 15,000 ne suka yi tafiyar a ranar Talata, yayin da kusan 5,000 suka isa wurin ranar Litinin.

A ranar Laraba sojojin Isra'ila suka ce sun ƙara sa'a guda zuwa ƙarfe uku na rana agogon yankin, ganin yadda yawan mutane ke amfani da ita.

Daga baya mai magana da yawun sojojin na Isra'ila ya ce kimanin mutum 50,000 ne suka bar yankin arewacin Gaza ranar Laraba ta hanyar amfani da titin Salah al-Din.

Rundunar sojin Isra'ila ta wallafa wani bidiyo a shafinta na X, wanda ke nuna yadda wasu gungun mutane ke tafiya ta kan hanyar, inda wasu daga cikinsu ke ɗaga fararen tutoci(dake nuna su fararen hula ne) inda ake ganin tankokin yaƙin Isra'ila a gefen titin.

Rashin kyawun hanyar

Sashen bin diddigi na BBC ya yi nazarin hotunan da aka ɗauka ta hanyar tauraron ɗan'adam na titin Salah al-Din daka Wadi Gaza domin auna yawan lalacewar da titin ya yi a lokacin yaƙin.

Rundunar sojin Isra'ila ta ce tana yunƙurin ganin ba a cutar da fararen hula ba, ta kuma ce za ta ci gaba da barin mutane suna barin yankin.