Yadda aka yi ɓarin kuɗi a bikin ɗan attajirin duniya na 11 a Indiya

..

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Anant Ambani tare da mariyarsa Radhika Merchant a lokacin bikin a birnin Mumbai

A yau lahadi ne ake ƙarƙasre bikin ɗan gidan hamshaƙin attajirin nan na yankin Asiya wato Mukesh Ambani.

Taron bikin ya samu halartar manyan mutane da suka haɗa da tsoffin firaministocin Birtaniya biyu, da manyan hamshaƙan 'yan kasuwa da fitattun taurarin fina-finan duniya da mawaƙa daban-daban.

Biki ne na ɗan autan hamshaƙin attajiri, Mukesh Ambani, wato Anant da amariyarsa Radhika Merchant, wanda aka ɗaura aurensu ranar Asabar a birnin Mumbai na ƙasar Indiya, bayan shafe watanni ana shagulgulan bikin na ango da amariyar waɗanda duka shekarunsu 29.

An gudanar da taron ɗaurin auren a wani katafaren ɗakin taro mai cin mutum 16,000, inda ango da amariya suka zauna aka yi musu ajo gaban manyan hamshaƙan mutane daga sassa daban-daban na duniya.

..

Asalin hoton, ANI

Bayanan hoto, Amariya, Radhika Merchant, 'ya ce ga fitaccen dillalan magunguna Viren da Shaila Merchant

Gabanin haka a ranar Juma'a aka gudanar da wani gagarumin fati, wanda fitattun mutane a duniya ciki har da tauraron wasan damben nan na duniya John Cena da tsoffin firaministocin Birtaniya Tony Blair da Boris Johnson.

Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya, Fifa, Gianni Infantino, da fitaccen tauraron fina-finan Indiya, Shah Rukh Khan da shugaban kamfanin Samsung, Jay Y Lee na daga cikin ɗaruruwan mutanen da suka halarci bikin.

"Gagarumin bikin aure!" kamar yadda jakadan China a Indiya, Xu Feihong ya wallafa a shafinsa na X , tare da hotunan ango da amariya.

"Fatan alkairi ga ango da amariya, Allah ya ba da zaman lafiya!", kamar yadda ya rubuta.

A yau Lahadi ne za a ƙarƙare taron gagarumin bikin a wani taron liyafar cin abinci da maraice.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tauraruwar fina-finan Indiya, Madhuri Dixit a wurin bikin

Yadda fitattun mawaƙa suka baje-kolinsu

Daga cikin tarukan shirye-shiryen shagulgulan bikin da aka gudanar a farkon wannan shekarar, har da wanda dangin Ambani suka yi a wani wurin bauta n addinin Hindu, inda aka gayyaci makaɗa da mawaƙa ciki har da Rihanna da Justin Bieber.

Manyna baƙin da sukla halarci wannan taro har da mamallakin kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg da Ivanka Trump 'yar gidan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump.

A cikin watan Yuni ango da amariyar suka shirya wani gagarumin fati a gaɓar teku a Faransa, wanda baƙi fiye da 1,200 suka halarci inda fitattun mawaƙa irinsu Katy Perry da Backstreet Boys na Amurka da Andrea Bocelli na Italiya suka cashe.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tauraron fina-finan Indiya, Arjun Kapoor tare da ƙanwarsa, Anshula Kapoor.

An ɗauki shatar jirage don jigilar mahalarta bikin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Shugaban kamfanin jiragen sama na Club One Air Rajan Mehra, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai an Reuters cewa iyalan ma'auratan sun ɗauki shatar jirage domin jigilar baƙin da suka halarci bikin auren da aka gudana da a wannan mako.

“Baƙi sun zo daga ko'ina a faɗin duniya, kuma kowane jirgi zai yi jigilar baƙi daga sassan daban-daban na ƙasar nan,” in ji shi.

Mahaifin angon, Mukesh mai shekara 66, shi ne shugaban rukunin kamfanonin Reliance, kamfanin da ya yi zarra ta fuskar jari tsakanin takwarorinsa a faɗin Indiya.

Shi ne kuma mutum 11 a jerin attajiran duniya, inda ya mallaki kadarorin da suka kai darajar fiye da dala biliyan 123, kamar yadda mujallar Forbes ta nuna.

Daga cikin fannonin da kamfaninsa ke zuba jari a ciki har da kashi 40 cikin 100 na kasuwancin waya a Indiya, da kuma gasar kwallon kirket ta Indiya.

Gidansa, wanda bene ne mai hawa 27 na ɗaya daga cikin fitattun gine-gine a Mumbai, wanda aka ƙiyasta an kashe dala biliyan guda wajen gina shi, inda fiye da mutum 600 aiki wajen kula da gidan.

Ita kuwa amariyar 'yar gidan fitattun mamallakan kamfanonin harhaɗa magunguna.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An kwashe watanni ana gudanar da shagulgulan bikin a nahiyoyi daban-daban na duniya

An toshe manyan titunan Mumbai a lokacin bikin

A lokacin shagulgulan bikin an tsohe manyan titunan birnin Mumbai na kusan sa'ao'i masu yawa rana gudan kafin ranar ɗaurin auren har zuwa ranar Litinin domin bai wa baƙi damar gudanar da shagulgulansu.

Sannan an ci gaba da wallafa hotuna da bayanan bikin a shafukan sada zumunta a kowane minti.

Mazauna birnin sun yi ƙorafin cewa ruge wasu titunan ya haifar da ƙarin cunkoso a birnin, yayin da wasu ke mamakin yadda aka ɓarnatar da dukiya a auren.

Iyalan Ambani ba su bayyana adadin abin da suka kashe a bikin ba, to amma masu shirya bukukuwa sun yi ƙayasin cewa abin da aka kashe ya kasi tsakanin dala miliyan 123 zuwa 156.

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ango, Anant Ambani a lokacin bikin

An ce abin da ka biya Rihanna a cashiyar da ta yi ya kai dala miliyan bakwai, yayin da aka ce an biya Justin Bieber dala miliyan 10.

Wani mutum da ba a bayyana sunansa ba - wanda ke cikin jagororin kamfanin Reliance ya yi iƙirarin cewa bikin wata ''alama ce ta Indiya ta kai wani matsayi a duniya''.

To amma wasu 'yan siyasar hamayya a ƙasar, Thomas Isac ya ce kuɗin da aka kashe ''almubazzaranci ne''

"Mun yadda kuɗin na halaliyasu, to amma wannan almubazzaranci ka iya zama laifi ga ƙasarmu, musamman yadda talakawa ke fama'', kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.