'Na gwammace na mutu kan abin da aka yi min': Matan da aka ci zarafi a lokacin yaƙi

Zanen wata mata da hannu a bayan ta, daga ƙasan ta kuma zaben wasu matan ne da kuma bishiyoyi a gefe.

Asalin hoton, Klawe Rzeczy

    • Marubuci, BBC World Service
  • Lokacin karatu: Minti 7

Gargaɗi: Wannan rahoton ya ƙumshi bayanin fyaɗe da cin zarafin mata. An canza sunayen mutanen da abin ya shafa domin kare su.

Enat ta ce tana zaune a gida tare da ɗiyar yayanta mai shekara takwas lokacin da sojojim suka shiga a ranar Lahadi da safe.

Dakarun Habasha na bincike a gidaje a yankin Amhara a ranar 5 ga watan Janairun bana, daga cikin ƙoƙarin ta na murƙushe ƴan tawayen Fano.

Enat ta ce sojoji uku sanye da kakinsu sun shiga gidanta da ke kudancin Gondar kuma sun fara da tambayar ta bayani a kan jama'ar gidan su, da kuma neman sanin ko mayaƙan Fano sun taɓa ziyartar mashayar da take aiki.

Enat, mai shekara 21, ta shaida masu cewa ƴan tawayen suna zuwa.

"Ta yaya za mu yi ƙarya? A kan me za mu ɓoye gaskiya?" in ji Enat says. Fano kalmar harshen Amhara ce da ke nufin mayaƙan sa kai.

Abubuwa sun rincaɓe daga nan.

Bayan tambayar ta tarihin gidan su, Enat ta ce daga nan sai sojojin suka fara zagin ta da kuma yi masu barazanar harbe su, inda ɗiyar yayan nata ta fara kuka.

Enat says one of the soldiers then raped her in front of her niece while the others kept guard.

"Na roƙe su kada su cutar da ni. Na haɗa su da Allah, amma zuciyar su ta bushe. Sun ci zarafi na."

Dubban rahotannin fyaɗe da cin zarafi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Enat, yar ƙabilar Amhara ce, ƙabila mafi yawan jama'a ta biyu a Habasha, kuma tana cikin dubban matan da aka ci zarafin su ta hanyar fyaɗe tun bayan da aka fara rikici tsakanin dakarun Habaha da mayaƙan Fano a watan Agustan 2023.

Cin zarafin da aka aikata a yankin yana da yawa kuma da dama ba a tattara rahoton faruwar su, amma BBC ta tattara bayanai da suka nuna cewa an aikata dubban fyaɗe daga watan Yulin 2023 zuwa Mayun 2025, kuma daga cikin waɗanda aka yiwa fyaɗen akwai ƙananan yara masu shekaru takwas da kuma tsaffi masu shekara 65.

Yayin da aka sanya wa wasu kafafen yaɗa labarai takunkumin shiga Amhara domin ɗauko labaran rikicin da ya faru, tawagar BBC a Nairobi ta zanta da wasu mata da likitoci daga yankin, waɗanda suka bayar da labarin yadda rikicin ya shafi al'umma.

Rikicin ya fara ne lokacin da gwamnati ta yi yunƙurin rushe ƙungiyoyin ƴan tawaye ciki harda na Amhara, wadda ta yi yaƙi da sojoji a lokacin yaƙin basasa a a maƙwabciyar su, Tigray a tsakanin 2020 da 2022.

Lamarin ya sa mayaƙan Fano suka ƙaddamar da tawaye da kuma ƙwace wasu manyan garuruwa. Sun yi iƙirarin neman ƴanci ga yankin, da kuma kare jama'ar su daga wariyar da gwamnatin Habasha ke nunawa.

Hakan ya janyo mummunan rikici, inda dakarun Habasha suka sha alwashin ƙwamushe Fano, ƙungiyar da suka kira mai tsattsauran ra'ayi.

Zanen hannuriƙe da bindiga ƙirar AK-47 da wasu mata guda biyu, dukkan su sanye da farin mayafi

Asalin hoton, Klawe Rzeczy

Tun bayan ɓarkewar rikicin, ɓangarorin biyu sun zargi juna da aikata laifukan cin zarafi da keta haƙƙin ɗan Adam da kisan gilla da tsare mutane ba bisa ƙa'ida ba da satar dukiya da kuma fyaɗe.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam, ciki harda Amnesty International sun ɗora wa dakarun sojin Habasha laifukan. Sun kuma ce a lokuta da dama dakarun Habashan sun ƙaddamar da hari kan al'ummar Amhara.

Kafin a kai mata hari, Enat ba ta taɓa yin jima'ai ba kuma tana da burin cewa wata rana za ta yi aure a coci kamar yadda addinin ta ya yi tanadi, kamar yadda sauran mata a zuri'arsu ke yi.

Irin wanna aure yana da matuƙar ƙima a tsakanin jama'ar Amhara, waɗanda mafi yawan su kiristoci ne da suka yarda cewa dole mace ta tsarkake kanta daga jimi'i har sai bayan ta yi aure.

"Kafin wannan ranar ban taɓa sani ɗa namiji ba," in ji ta.

"Da ma kashe ni suka yi, zai fiye mani alheri."

'Ƴan uwana sun same ni ba a cikin hayyacina ba'

Tigist, mai shekara 18, daga yammacin Gojjam, duk dai a yankin Amhara, tana aiki ne a wajen sayar da shayin gargajiya mallakin ƴan gidansu, lokacin da aka kai mata hari.

Ta bayyana yadda a watan Janairun 2024 wani soja wanda ya daɗe yana siyayya a wajenta, ya afka mata. Ta ce taƙi amincewa da yunƙurinsa na neman ta, lamarin da ya daga baya ya afka mata.

Ta ce wata rana da marece tana dawowa daga aiki sai wasu sojoji uku ciki harda wanda ya taɓa neman ta suka tare ta a kan titi, inda suka yi mata fyaɗe a gefen titi.

Ta ce "Ƴan uwana sun same ni ba a cikin hayyacina ba a gefen hanya,'' "Sun ɗauke ni suka kai ni wani asibiti, inda na shafe kwana biyar ina jinya."

Tun bayan harin, Tigist ta ce ba ta iya fita daga gida kuma tana matuƙar tsoron maza da kuma duk wani mutum da ba ta sani ba.

"Tsoron da nake ji ya hana ni zuwa wajen aiki.... duk lokacin da na ga soja ko wani mutum ina shiga firgici da tsoro."

Ta ce lamarin ya sa ta sauya sosai, kuma ya tilasta mata fasa auren da a baya aka sanya mata rana da saurayin ta, kuma ba ta taɓa faɗawa saurayin nata abin da ya faru ba.

Tigist ta kuma yi yunƙurin kashe kanta, amma ƴan uwanta sun yi nasarar hana ta, kuma daga baya ta sha alwashin ba za ta sake tunanin kashe kanta ba.

'Abin takaici ne a haife ki a mace'

BBC ta tattara bayanai daga asibitoci 43 a Amhara, kamar kashi 4% na jimillar asibitocin yankin, da kuma wasu majiyoyi na daban domin gano abin da ke faruwa.

A waɗannan asibitoci, akwai rahotanni 2,697 na aikata fyaɗe daga ranar 18 ga watan Yulin 2023 zuwa Mayun 2025. Kuma kashi 45% na waɗanda abin ya shafa ƙananan yara ne ƴan ƙasa da shekara 18.

Fiye da rabin waɗanda aka yi wa fyaɗen an tabbatar da cewa suna ɗauke da cutukan da ake samu ta hanyar jima'i, yayin da da dama suka samu juna biyu kuma suke fama da matsananciyar damuwa.

Akwai kuma da dama da basu bayar da labarin fyaɗen da aka yi masu saboda tsoron tsangwama ko kamuwa da cuta ko kuma kada gwajiya tabbatar da suna ɗauke da juna biyu.

Wani babban jami'in kiwon lafiya da ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa BBC cewa ƴan kaɗan ne daga cikin waɗanda aka yi wa fyaɗe a Amhara ke zuwa asibiti.

Lemlem tana cikin waɗanda suka ƙi bayar da rahoton fyaɗen da aka yi mata ko kuma neman kulawar likita saboda tsoron kamuwa da cutuka irin HIV.

Mai shekara 23 daga kudancin Gondar, ta ce sojojin gwamnati sun shiga gidan ta a ranar 6 ga watan Janairu domin neman bayanai, wani abu da aka saba da shi.

Ta ce ɗaya daga cikin sojojin ya yi mata fyaɗe bayan bai samu bayanan da yake nema ba.

"Ya yi mani barazanar cewa idan na yi ihu, harsashi ɗaya ya isa ya aika dani lahira,'' in ji Lemlem.

Ta ce "Na yi kuka babu ƙaƙƙautawa har tsawon wata ɗaya. Na kasa cinabinci, babu abin da nake yi sai kuka. Na kasa tsayuwa, kotafiya, kuma na yi fama da jinya.''

Ta bayyana yadda lamarin ya hana ta zuwa coci saboda tsoron tsangwama.

Zanen wata mata da aka oye fuskarta sanye da farin mayafi, a gefenta kuma titin mota ne da kuma bishiyoyi.

Asalin hoton, Klawe Rzeczy

Ma'aikatan lafiya da BBC ta zanta da su sun ce an samu matuƙar ƙaruwar matanda ake ci zarafin su a Amhara, masu zuwa asibiti domin a kula da su.

"Suna zo mana a firgice, ta yadda ko magana na gagarar su,'' in ji wani ma'aikacin lafiya.

Duk da ƙoƙarin kwantar masu da hankali,waɗanda aka yi wa fyaɗen ba su iya bayyana ko waye ya yi masu. Kuma ba su iya tashi domin neman haƙƙin su.

Bayanan da ƙwararru a kiwon lafiya suka tattara sun nuna cewa akwai alamar za a samu yawaitar yaɗuwar cutar HIV da kuma cutukan ƙwaƙwalwa, tare da nuni da cewa wasu daga cikin su na yunƙurin kashe kansu.

Taswira mai nuna yankin Amhara da ke arewa maso yammacin Habasha.

A watan Yunin 2024, ofishin MajalisarDinkin Duniya mai kula da ƴancin ɗan Adam ya bayar da rahoton cewa ma'aikatar tsaron Habasha, wadda ta ƙumshi dakarun sojin ƙasar ta aikata laifukan cin zarafi ta hanyar lalata ga mata, ciki harda ƙananan yara a yankin Amhara.

BBC ta tambayi ma'aikatar tsaron, amma bayan watanni ana jira, babu wani martani da muka samu.

Haka nan kuma BBC ta nemi a ba ta bayanan da hukumomi suka tattara kan abin da ya faru a yankin amma babu wanda ya ba ta.

Jagoran Fano, Asres Mare Damtie, ya shaidawa BBC cewa ƙungiyar ba ta san komai ba a kai, kuma babu hannun ta a cikin laifukan da aka aikata domin a cewarta, tana hukunta duk wanda ta samu da aikata laifi a cikin mabiyan ta.

BBC ta gano cewa akwai wani bincike da gwamnati ta ƙaddamar da haɗin gwiwar jami'ar Bahir Dar game da fyaɗe da sauran cin zarafin da aka yi wa mata a Amhara ya yi nisa, kuma ana sa ran fitar da sakamakon sa cikin watanni masu zuwa.

Global Women
  • This is part of the Global Women series from the BBC World Service, sharing untold and important stories from around the globe