Shin wa Amurka ke kai wa hare-hare a Iraqi?

Rubutuwa: Aine Gallagher

Amurka ta kai hare-hare ta sama kan wasu cibiyoyi mallakin mayakan da ke samun goyon bayan kasar Iran a Iraqi. Ta ce hare-haren "martani ne kai tsaye" ga jerin hare-hare" kan Amurka da sojojin kasashen duniya a Iraqi da Syria.

Menene martanin?

Gwamnatin Iraqi ta yi allahwadai da hare-haren Amurkar. Kakakin Firaministan Iraqi, Mohammed Shia al-Sudani ya ce hare-haren "karara sun take dokokin yancin kasarsa. Amurka ta ce ta kai hare-haren ne kan kungiyoyin da ke da alaka da Iran."

Wa ke da hannu a hare-hare kan gine-ginen Amurka?

Kataib Hezbollah, na daya daga cikin kungiyoyi uku da ke da hannu a hare-hare kan sansanonin Amurka da ke Iraqi wadda daga bisani Amurka ta kai mata hari.

Kungiyar mayakan Shi'a ta Iraqi na da karfi wadda take samun tallafin makamai da kudi daga Iran.

Ana kuma tunanin kungiyar na da alaka mai karfi da dakarun Quds ta Iran, reshen sojojin juyin-juya halin kasar ta Iran wato IRGC.

Mene ne silar rikicin?

Kungiyoyin mayaka da ke samun goyon bayan Iran a Iraqi sun ce rikicin ya samo asali ne daga yakin da ake a Gaza, bayan harin da kungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba. Iran na goyon bayan Hamas yayin da Amurka ke mara wa Isra'ila.

Tun lokacin, sojojin Amurka suke fuskantar hare-hare sau akalla 151 a Iraqi da Syria, inda Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce akasari hare-haren rokoki da na jirage marasa matuki ne.

Amurka ta ce sojoji 2,500 a Iraqi da 900 a Syria mai makwabtaka sun mayar da hankali wajen hana sake dawowar mayakan IS.

Kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran sun dage cewa matsayarsu ta kai hari kan sansanonin Amurka a Iraqi abu ne da suka yi a cikin gida babu sa bakin Tehran.

Sai dai sun kuma ce suna aiki ne karkashin tuta guda a Iraqi da Syria da Lebanon karkashin wata gamayyar kungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran (Axis of Resistance).

Kwararru sun ce kungiyar ta zama daya daga cikin "kayan aikin"da Iran ke amfani da shi wajen matsa lamba a yankin.

Ya batun sauran kungiyoyi masu samun goyon bayan Iran da ke Iraqi?

Kungiya mafi girma a baya ita ce ta Popular Mobilisation Forces (PMF). Mayakan shi'a ne suka kafa ta da suka hada kai domin fatattakar kungiyar IS daga Iraqi.

PMF da farko a rabe take kuma ana kallon ta a matsayin mai samun goyon bayan Iran. Sai dai ta zama wani reshe karkashin ikon sojojin Iraqi a 2016.

Me gwamnatin Iraqi ta ce?

Gwamnatin Iraqi ta ce Amurka na kai hare-haren ne kan sansanonin sojinta kuma suna kashe mambobin kungiyar PMF. Tana kwatanta ayyukan Amurka a Iraqi da kuma mummunan halin da ake ciki yanzu a Gaza.

"Yankin yana cikin hadarin fadada rikicin da mummunan tasirin luguden wutar da ake a Gaza da kuma kazamin yaki da Falasdinawa ke fuskanta," in ji Manjo Janar Yehia Rasool, wani kakakin Firaiministan Iraqi, kamar yadda ya fada cikin wata sanarwa.

"Yayin da kasashe masu karfin iko har da Amurka suka yi tsit game da wadannan munanan laifuka, mun ga Amurka ta soki matakin da kuma kai hare-hare ba dalili kan yankunan Iraqi.

Kalaman jama'a a bayan fage, gwamnatin Iraqi na kokarin shiga tsakani da kawo saukin yakin tsakanin kungiyoyi masu tallafin Iran da Amurka amma zuwa yanzu ba ta yi nasara ba.

Firaiministan Iraqi yana aika sakonni daban-daban kan ko ya kamata Amurka ta kawo karshen ayyukan sojinta a Iraqi, inda Washington ta tura sojoji tun mamayar 2003.