Ɓatar da kama don bankaɗo yadda 'yan sumoga ke safarar mutane zuwa Turai

    • Marubuci, By Reha Kansara, Samrah Fatima & Jasmin Dyer
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Trending, BBC Urdu & BBC Newsnight

"Babu wata damuwa. Ko 'yan shekara 12 ne ko 18, muna ɗaukar irin waɗannan yaran su ma."

Wani mai safarar mutane ne a Quetta ke yi wa wakilin BBC da ya ɓatar da kama yadda yake gudanar da harkokinsa a Pakistan. Idan aka biya miliyan 2.5 na rupee ɗin Pakistan (dala 9,000), mutum zai isa Turai "lafiya kalau" cikin kamar mako uku, a cewarsa, ta hanyar tsallaka iyaka zuwa Iran a ƙafa da kuma zuwa Turkiyya da Italiya a mota.

Akwai ƙwarin gwiwa a muryarsa.

"Ya kamata ya tafi da kayan jefawa a baki (Snacks). Dole ne ya saka takalmi mai inganci, da kuma tufafi kamar kala uku. Shi ke nan. Zai iya sayen ruwa a Quetta. Da zarar ya shiga Quetta, zai kira ya faɗa sai wani ya zo ya tafi da shi."

Ɗan sumogar mai suna Azam ya yi iƙirarin cewa ɗaruruwan baƙin-haure ne ke shiga Iran a kullum. Ya nuna ƙarancin haɗarin da ke cikin tafiyar lokacin da yake yi wa wakilinmu bayani a matsayin wanda yake so ya kai ɗan’uwansa Birtaniya.

Yayin da hauhawar farashi ke ƙaruwa kuma darajar rupee na Pakistan ke faɗuwa, mutane da dama na barin ƙasar. Hukumomi a Pakistan sun faɗa wa BBC cewa kusan mutum 13,000 ne suka bar Pakistan zuwa Libya da Masar cikin wata shida na farkon 2023, idan aka kwatanta da 7,000 da suka fice a 2022.

A watan Yuni, ɗaruruwan baƙin-haure ne suka mutu bayan jirgin ruwan da suke ciki ya kife a kusa da gaɓar ruwa ta Girka. Ana zaton akwai 'yan Pakistan 350 a cikinsu.

"Ko da an kama shi a kan hanya, gida kawai za a dawo da shi. Babu wanda zai sace shi don ya nemi kuɗin fansa ," in ji Azam.

Sai dai kuma matafiyan kan faɗa hannun ƙungiyoyi a Libya. Wani ɗan Pakistan da muka yi magana da shi wanda ya bi 'yan sumoga zuwa Italiya, ya ce an kama shi kuma aka tsare shi a gidan yari tsawon wata uku a Libya.

Saeed (ba sunansa na gaskiya ba ne) ya ce an sake shi ne bayan 'yan’uwansa sun biya kuɗin fansa dala 2,500 (fan 2,000).

'Tura saƙonnin neman game'

'Yan sumogar da yawa kan tallata ayyukansu a fili a shafukan sada zumunta kamar Facebook da TikTok - a kan shafukansu da ke da dubun dubatar mabiya.

Tun daga watan Mayu, BBC ta yi ta bin shafukan zumunta da ke tallata yin ƙaura ba bisa ƙa'ida ba. Da alama suna sakaya kalmominsu ne saboda su guje wa sa-idon kamfanonin sada zumuntar da kuma hukumomi. Sukan shirya tafiyar da kuma karɓar a ɓoye ta shafukan tura saƙo kamar WhatApp.

Ɓoyayyun kalmomi kamar "dunki" da "game" ake amfani da su wajen tallata zuwa Turai ba bisa ƙa'ida ba. "Dunki" na nufin tsallakawa ta jirgin ruwa, "game" kuma na nufin balaguron da mutum zai yi daga farko har ƙarshe.

Bayan kifewar jirgi, masu sumogar da BBC ta lura da su sun yi ta tallata "taxi games" - taƙaitattun kalmomin da ke nufin balaguro ta Gabashin Turai - a matsayin hanyar da suka fi so.

'Yan sumogar kan wallafa hotunan bidiyo na rukunin baƙin-haure sun ɓoye fuskokinsu da hulunan rigunansu kuma suna shiga ƙananan motoci, inda aka rubuta sunaye da lambar wayar 'yan sumogar a jiki.

Azam ya ƙware wajen shirya "taxi games", yana mai iƙirarin cewa sun fi lafiya fiye da bin jirgin ruwa. Sai dai akwai haɗurra a wannan hanyar ma.

Hukumar UNHCR ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ta ce tsananin sanyi ya kashe matafiya da yawa yayin da suke tafiya a ƙafa, da kuma haɗurran mota.

Balaguron Saeed zuwa Libya

Wasu 'yan sumoga biyar da muka yi magana da su sun ce sun fi son "taxi game". Wani ya ce zai iya kai mutum Turai har Faransa kan dala 1,228 (fan 1,000).

Mun nuna wa kamfanin Meta - mamallakin Facebook da WhatsApp - da kuma TikTok, cewa ana amfani da shafukansu wajen tallata safarar mutane.

Meta ya goge dukkan adireshi zuwa zaurukan WhatsApp da muka nuna musu, amma ba su goge shafukan mutanen da ke yaɗa su ba. Bai goge zaurukan na WhastApp ba saboda tsarinsa na sirri tsakanin hirar mutane bai bayar da damar a ga abin da suke tattaunawa ba.

TikTok ya goge adireshin mutanen da muka nuna masa. Ya ce "kamfanin ba ya lamuntar saƙonnin da ke goyon bayan safara" kuma ya "goge shafuka da saƙonnin da suka saɓa wa dokokinsa".

'Balaguron mutuwa'

Saeed ya bar garinsu na Kashmir da ke ƙarƙashin ikon Pakistan kusan shekara ɗaya da ta wuce saboda rashin aikin yi ga matasa a yankinsu - da kuma yawan hatsaniya a kan iyaka da ɓangaren Indiya. Yana zaune kusa da iyakar - wanda ake kallo a matsayin layin da ya raba Indiya da Pakistan - amma ya zauna a Italiya tsawon wata 10.

Ya ce ya samu ƙwarin gwiwar zuwa Turai ne saboda bidiyon da ya gani a TikTok da kuma wani da abokinsa ya nuna masa wanda ya bar Pakistan kafin shi.

"Na ji ana cewa abu ne mai sauƙi mutum ya zo nan, kuma kwana 15 zuwa 20 ne kawai. Amma duk ƙarya ce. Sai da na shafe sama da wata bakwai," a cewarsa.

Saeed na jiran matsayar da za a dauka kan izinin samun mafaka da ya nema a Italiya, yana mai cewa ya yi nadamar bin hanyar bayan fage inda ya ce "tafiyar mutuwa ce". Amma yana yawan wallafa bidiyo kan sabuwar raywursa a TikTok.

'Yan wasu bidiyo da ya wallafa sun nuna yadda balaguron nasa ya kasance daga Pakistan zuwa Turai.

Cikin wani bidiyo da aka yi wa take da "Pakistan zuwa Lbiya", wani abokin tafiyarsa ya ɗauke su tare zaune cikin wani jirgi suna murmushi.

Ya ce wannan "ɗaya ne cikin abubuwan neman birgewa" wallafa irin waɗannan bidiyon a TikTok saboda "ba ita ce haƙiƙanin halin da mutanen ke ciki ba".

Sati biyu bayan wakilinmu da ya ɓatar da kama ya tuntuɓi ɗan sumogar mutane, mun sake tuntuɓar sa - amma mun ce masa 'yan jaridar BBC ne.

Da muka ƙalubalance shi game da haɗurran irin wannan balaguro, sai ya kashe wayar.