Dalilan da suka sa Tinubu ya dakatar da ministar jin ƙai Betta Edu

Asalin hoton, Ministry for humanitarian affairs/Facebook
- Marubuci, Mukhatari Bawa
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba da kai ga ɗumbin matsin lambar da aka yi ta yi masa, tun cikin makon jiya, daga 'yan Najeriya, masu fafutukar yaƙi da rashawa da kuma 'yan adawa a kan ministarsa ta jin ƙai da yaƙi da talauci.
Tinubu ya dakatar da Betta Edu nan take daga kan muƙaminta a ranar Litinin.
Matakin na zuwa ne kwana ɗaya bayan ministan yaɗa labaran ƙasar ya fitar da sanarwa game da ka-ce-na-cen da ya ɓarke a kan ministar, bayan an zarge ta da tafka jerin almundahana.
Sai dai ta fito tana musanta zar-zargen waɗanda ta ce bi-ta-ƙulli ne kawai.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale, ta umarci EFCC, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta gudanar da bincike kan zarge-zargen da ake yi wa Betta Edu.
Wani abin arashi, a yanzu haka hukumar na bincike a kan wadda ta gabaci ministar, wato Sadiya Farouq a kan zargin halasta kuɗin haram, sama da naira biliyan 37 lokacin da take mulki zamanin gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.
Haka zalika, dakatar da ministar na zuwa ne kwana shida kacal bayan dakatar da Halima Shehu, shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa wato National Social Investment Programme Agency, wadda ita ma aka yi zargin hannunta a badaƙalar halasta kuɗin haram.
Umarnin tura kuɗi zuwa asusun ajiyar wata
Taƙaddama ta faro ne tun lokacin da aka zargi Betta Edu da ba da umarnin biyan sama da naira miliyan 585 cikin asusun ajiyar wani mutum, lamarin da ya saɓa da ƙa'idar aiki.
A cikin wata wasiƙa da aka yi zargin ministar ta sanya hannu, Betta ta umarci babbar akantar Najeriya, Oluwatoyin Madein ta zuba kuɗi cikin asusun wata mai suna Oniyelu Bridget, a matsayin tallafi ga ƙungiyoyin mutane masu rauni a jihohin Akwa Ibom da Cross River da Lagos da kuma Ogun.
Sai dai babbar akantar ta yi bayanin cewa, ko da yake ofishinta ya karɓi wannan buƙata daga ma'aikatar jin ƙai, amma bai yi abin da aka nema ba.
Betta Edu, 'yar shekara 37, wadda ita ce matashiya mafi ƙaranci shekaru a jerin ministocin Tinubu, daga bisani ta ce ƙulle-ƙulle ne kawai ake yi don a ɓata mata suna, ta ƙara da cewa ba za ta yi almundahana da duniyar gwamnati ba.
Biyan kuɗin tafiyar jirgin sama zuwa jihar da ba ta da filin jirgi
Baya ga wannan badaƙala, da kuma zargin keta dokokin tafi da dukiyar al'umma, an kuma zargi ministar da amincewa da biyan kuɗin tikitin jirgin sama zuwa jihar Kogi.
Haka zalika, an zarge ta da biyan kuɗin shiga taksi daga filin jirgin sama zuwa cikin gari ga ma'aikatanta a lokacin wata ziyara, don kai tallafin dogaro da kai ga wasu masu rauni a jihar.
Sai dai rahotanni sun ce jihar Kogi, kusan sanin kowa ne a Najeriya, ba ta filin jirgin sama da yake aiki.
Waɗanda suka bankaɗo zargin sun yi ta kafa hujja ta hanyar wasu takardun biyan kuɗi da suka yi zargin ministar ta amince da su a shafukan sada zumunta.
Dangane da haka ne shugaban ƙasa ya naɗa ministan kuɗi da kula da tattalin arziƙi, Wale Edun ya jagoranci wani kwamiti da zai yi bincike a kan zargin almundahana a ma'aikatar jin ƙai da yaƙi da fatara.
Saɓa ƙa'idar aiki
Ƙungiyoyin fafutuka da dama a Najeriya, sun yi ta kiraye-kirayen a gudanar da bincike, inda suka zargi Betta Edu da saɓa ƙa'idar aiki.
Muhimmi daga ciki shi ne umarnin da ake zargin ta bayar na a biya kuɗi cikin wani asusu mallakar wata mata maimakon yadda tsarin kashe kuɗi na gwamnati yake, abin da suka ce kai tsaye keta dokoki da tsare-tsaren harkokin kuɗi ne da aka tanada.
Katsalandan ga hukumomin da ke ƙarƙashinta
Ɗaya daga cikin manyan zarge-zargen da aka yi wa Betta Edu, shi ne fitar da kuɗi kai tsaye ba tare da masaniyar shugabancin hukumomin da ke ƙarƙashin ma'aikatarta ba.
Zargin ya faro ne tun lokacin da aka dakatar da shugabar hukumar ba da tallafin dogaro da kai ta ƙasa NSIPA, Halima Shehu, wadda wasu makusanta suka zargi ministar da ƙoƙarin shafa wa Halima kashin kaji.
Sun dai yi zargin cewa ministar ta riƙa tsallake shugabar NSIPA tana fitar da kuɗaɗe daga asusun hukumar, don rabawa a matsayin tallafin dogaro da kai ga masu rauni.
Haka kuma wata ƙungiya ta nemi gudanar da bincike kan zargin katsalandan da karkatar da kuɗaɗen hukumar ba da tallafin dogaro da kai.
Ƙungiyar ta yi zargin cewa a watan Disamban 2023, Betta Edu ta gudanar da harkokin kuɗi da suka kai naira biliyan 11 daga asusun NSIPA, ba tare da sanin shugabar hukumar ba.











