Mene ne maganin pregabalin kuma me ya sa shansa zai iya zama hatsari?

Magani a kan tafin hannu

Asalin hoton, Getty Images

An danganta maganin pregabalin ga adadin mace-mace a duniya.

Yawancin masu amfani suna siyan maganin ne a kasuwar bayan fage, yawanci daga shafukan intanet da ba a sa ido a kansu.

Mene ne maganin pregabalin kuma mene ne amfaninsa?

Ana amfani da maganin Pregabalin wajen magance yanayin da suka haɗa da farfaɗiya da ciwon jijiya da kuma damuwa.

Maganin na zuwa ne a matsayin ƙwaya ko kafso ko na ruwa, kuma ana iya kiransa Alzain ko Axalid ko Lyrica ko Signature, duk dai ya danganta da kamfanin da yayi maganin.

Mece ne illar pregabalin?

Wasu suna kiran pregabalin a matsayin wani magani da ke magance damuwa saboda yana iya sa masu amfani da shi su ji annashuwa da kwanciyar hankali.

Amma shan shi da yawa - musamman idan aka haɗa shi da sauran magunguna waɗanda su ma suna da tasirin kwantar da hankali - na iya haifar da yawan saurin jin bacci da matsalolin numfashi.

An shawarci marasa lafiyar da aka bai wa maganin pregabalin su guje wa shan giya.

Tabar Heroin and allura

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shan maganin pregabalin tare da abubuwan maye kamar tabar wiwi, na iya zama babban hatsari ga lafiyar mutum.

Shan maganin pregbalin haɗe da abubuwan maye kamar tabar wiwi suna rage numfashi.

Maganin gaggawa da ake kira naloxone wanda ke aiki kan abubuwan maye ba ya barin maganin pregabalin ya yi tasiri.

Za a iya kamuwa da jarabar shan maganin pregabalin?

Tasirin maganin pregabalin wajen kwantar da hankali - wani lokaci ana bayyana shi a matsayin "maye mara bugarwa" - na iya nufin wasu masu amfani da maganin ba sa la'akari da yanayin kamuwa da jarabar shan maganin na tsawon lokaci.

Dogaro da pregabalin yana da haɗari musamman ga waɗanda ke da tarihin shan miyagun ƙwayoyi ko kuma kamuwa da jarabar shan ƙwayoyi.

Ta yaya za a iya daina shan Pregbalin, kuma matsala ce?

Wasu mutane suna jin wuya ko wahalar daina shan maganin pregabalin.

Alamun janyewa shan maganin na iya haɗawa da canje-canjen yanayi kamar fushi da bacin rai da damuwa da firgita da sauran alamu kamar gumi da tashin zuciya da sanyi.

Duk wanda ke ƙoƙarin janyewa shan wannan magani ya kamata ya nemi shawarar likita kafin komai.

Kada mutum ya daina shan pregabalin kwatsam sai dai idan likitansu ya ba su shawara kan hakan. Yawancin lokaci ana rage adadin shan maganin sama da mako guda ko fiye da haka.

Shin ya halatta a yi amfani da pregbalin da likita bai rubuta ba?

A cikin ƙasashe da dama, ciki har da Birtaniya, pregabalin magani ne da dole sai likita ya rubuta kuma ya bai wa mutum damar sha, kuma mallakarsa ba tare da ingantaccen rubutun likita ba laifi ne.

Duk da haka ana sayar da maganin ta kan layi a cikin kantin magani a ƙasashe da dama a Gabas ta Tsakiya, alal misali, da kuma a yawancin jihohi a Indiya.

Mutuwa nawa aka danganta da shan maganin pregabalin?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An gabatar da Pregabalin a cikin Amurka da Birtaniya a shekarar1993.

Wani bincike da mujallar kiwon lafiya ta Nature Communications ta buga ya yi ƙiyasin cewa adadin alluran pregabalin da makamantansu na gabapentin da ake sha a kullum a duniya ya haura fiye da sau huɗu tsakanin shekarar 2008 zuwa 2018.

An ba da magungunan pregabalin fiye da miliyan takwas a Ingila a cikin 2022.

A wannan shekarar, an samu rahoton mutuwar mutane 441 dangane da maganin a Ingila da Wales.

A cikin 2023, Rahoton Yawan shan maganin fiye da ƙima na Shekara-shekara na Ostiraliya ya gano mutuwar mutum 887 da ke da alaƙa da pregabalin da gabapentin tsakanin shekarar 2000 zuwa 2021 - wanda kashi 93 cikin 100 ya fi shafan pregabalin.

Bayanai daga Birtaniya sun nuna yawancin mace-mace tsakanin shekarar 2004 da 2020 da suka shafi pregabalin sun faru ne lokacin da aka sha tare da wani magani kamar methadone ko morphine.

A yawancin lokuta, ba likita bane ya rubuta shan magungunan ba.

Waɗanne ƙasashe ne suka ga ƙaruwar shan pregabalin fiye da kima?

Amfani da pregabalin da gabapentin a Serbia ya ƙaru da kashi 60 cikin 100 a kowace shekara tsakanin 2008 da 2018.

A cewar bayanai daga Cibiyar Kula da Guba ta Ƙasa, magungunan sun gurɓata jikin mutum 374 a tsakanin 2012 da 2022. Daga cikin waɗannan, kashi 96 cikin 100 sun fi shan pregabalin.

Rahotannin hukuma sun nuna cewa ana kuma kara shan maganin a ƙasashen Saudiyya da Jordan, galibi kuma samari.

A cikin 2017, Cibiyar Gyaran Ƙasa ta Ƙasar Larabawa (UAE) ta ce pregabalin da gabapentin sune magungunan da aka fi amfani da su a cikin 'yan kasa da shekara 30.

An kama manyan pregabalin da aka yi cinikinsu ba bisa ka'ida ba a cikin UAE da Kuwait.

A cikin Maris, an kama kwayoyin maganin miliyan 2.75 daga wata ƙungiyar masu safarar mutane a Haɗadɗiyar Daular Larabawa.

A cikin 2023, hukumomi a Kuwait sun kama kapso na pregabalin miliyan 15 da rabin tan na ƙwayar maganin a gari.