An fara aikin ƙirƙirar ƙwayar halittar ɗan'adam mai cike da taƙaddama

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Pallab Ghosh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Correspondent
- Marubuci, Gwyndaf Hughes
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Science Videographer
- Lokacin karatu: Minti 3
An fara aikin ƙirƙirar ƙwayar halittar ɗan Adam, wani aiki mai cike da ruɗani wanda ake ganin wannan ne karon farko da za a yi irinsa a duniya.
A baya dai ana ganin wannan bincike a matsayin wani abin haramci, wanda ake fargabar zai buɗe kafar ƙirƙirar jarirai, tare da shafar yadda rayuwar mutane za ta kasance a nan gaba.
Amma a yanzu ƙungiyar bayar da tallafin samar da magunguna mafi girma a duniya, the Wellcome Trust, ta ware £10m domin a fara binciken, kuma ya ce aikin zai zamo mai alfanu ga duniya ta hanyar tallafawa aikin kula da lafiyar jama'a, musamman manyan cutuka da a yanzu ake ganin ba za a iya magance su ba.
Dr Julian Sale, na cibiyar gwajin ƙwayoyin halittu ta MRC Laboratory of Molecular Biology a Cambridge, wanda kuma ya ke cikin ƙwararrun da za su yi wannan aiki ya shaidawa BBC cewa sabon binciken zai zama gagarumin aikin da zai kawo canji a tarihin nazarin rayuwar ɗan Adam.
Ya ce: "Muna aikin samar da yanayi na inganta rayuwar jama'a, musamman idan suka tsufa, kuma hakan dama ce ta yaƙar cutukan da ke damun su, ta yadda mutane za su tsufa ba tare da fama da cutuka ba.
"Muna fatan amfani da wannan nazari wajen ƙirƙirar ƙwayoyin halitta da za su taimaka wajen gyara sassan jikin mutum da cuta ta lalata, kamar zuciya da hanta, da kuma bunƙasa ƙarfin lafiyar jama'a,''
Amma masu sukar binciken sun ce hanya ce ta bai wa wasu masu bincike damar ƙirƙirar mutane masu wata siffa ta musamman.
Dr Pat Thomas, daraktan kamfanin Beyond GM, ya ce: "Muna yawan tunanin cewa dukkan masu bincike suna yi ne da niyya mai kyau, amma akwai ƙwararru da za su iya amfani da binciken wajen kawo abin da zai cutar da duniya da hana walwala".
An bai wa BBC cikakken bayanin yadda wannan aiki zai gudana a wajen bikin cika shekara 25 da fara shirin bincike domin tantance yadda za a inganta ƙwayar halittar ɗan Adam.
Shirin binciken yadda ƙwayar halittar mutum take ya bai wa ƙwararru damar nazari a kan abubuwa da dama da suka shafi ƙwayar halittar ɗan Adam.

Asalin hoton, BBC News
Aikin farko da masanan suka sa a gaba shi ne samar da wani rumbu da za a ajiye ƙwayoyin halittar ɗan Adam, ta yadda idan suka yi yawa za su iya ƙirƙirar ɗan Adam. Haka kuma aikin zai bayar da damar amfani da ƙwayoyin wajen gyarawa da kuma bunƙasa ƙwayar halitar ɗan Adam.
Ana kuma sa ran amfani da wannan bincike wajen ƙara sanin yadda ƙwayar halitar ke tafiyar da jikin ɗan Adam.
Cutuka da dama na kama mutum idan aka samu akasi a ƙwayar halitta da kuma wasu sinadarai na jiki, in ji Farfesa Matthew Hurles, daraktan cibiyar Wellcome Sanger, wadda ta bayar da kaso mafi tsoka na kuɗaɗen gudanar da binciken.
Ya ce "Ƙirƙirar ƙwayar halitta wata hanya ce ta bamu damar yin gwaji kan bayanai masu cewa ana iya gyara ƙwayoyin halitta da suka daɗe a duniya. ''

Asalin hoton, BBC News
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan bincike zai bayar da damar aiwatar da dukkan matakan haɗa ƙwayar halitta amma ba za a yi yunƙurin busa mata rai ba. Amma fasahar za ta bai wa masana damar gudanar da sauyi a kan halittar mutanen da ke raye.
Duk da cewa shirin na cike da fatan samar da mafita a yunƙurin inganta kiwon lafiyar jama'a, babu wani mataki da aka ɗauka na hana masana damar shigar da tasu buƙatar ta mummunar manufa a cikin aikin.
A misali, ana tsoron cewa za su iya ƙirƙirar wani makamin ƙare dangi, ko kuma ƙirƙirar mutum mai wasu siffofi na daban da suka fi ƙarfin sauran mutane, kamar yadda Farfesa Bill Earnshaw na jami'ar Edinburgh ya jaddada.
Ya ce "Idan muka yi nasarar ƙirƙirar mutum ta amfanin da ƙwayar halitta da aka samar daga ɗakin gwaji, ta yaya za mu iya tafiyar da su, kuma su waye za su zamu sun mallake su?''
Akwai kuma fargabar cewa kamfanoni za su yi amfani da wannan damar wajen kambama farashin kayan aikin kula da lafiya da kuma bincike.










