Tottenham ta sanya Solanke a kasuwa, an yi watsi da tayin Man Utd kan Semenyo

Dominic Solanke

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Tottenham Thomas Frank bai gamsu da Dominic Solanke, mai shekara 28 ba, kuma yana iya neman cefanar da ɗan wasan na Ingila a watan Janairu. (Football Insider)

Bournemouth ta ki amincewa da tayin fam miliyan 50 daga Manchester United da Tottenham kan ɗan wasan Ghana Antoine Semenyo mai shekara 25, a bazarar da ta gabata. (Telegraph)

Tottenham na zawarcin Samu Aghehowa na Porto, mai shekara 21, amma ta na fuskantar hamayya daga Arsenal da Newcastle da Nottingham Forest. (Caught Offside)

Ɗan wasan tsakiya na Portugal Fabio Carvalho, mai shekara 23, zai iya barin Brentford a matsayin aro a watan Janairu don samun damar buga wasa, inda ɗan wasan ke nazari kan komawa gasar Bundesliga. (Florian Plettenberg)

Manchester United na son sanya hannu kan yarjejeniyar bayar da aron Joshua Zirkzee mai shekara 24 a watan Janairu, yayin da Roma ta shiga jerin ƙungiyoyin da ke zawarcin ɗan wasan na Netherlands. (TBR Football)

Ɗan wasan tsakiya na Ingila Morgan Rogers, mai shekara 23, yana tattaunawa da Aston Villa kan sabon kwantaragi. (Football Insider)

Barcelona ta gabatar da tayin Yuro miliyan 30 kan ɗan wasan Colombia da Crystal Palace Daniel Munoz mai shekara 29. (Fichajes)

Juventus na sa ido kan ɗan wasan Chelsea Malo Gusto, mai shekara 22, inda ta ke tunanin zawarcin ɗan wasan na Faransa a watan Janairu. (Calciomercarto)

Mai riƙe da babban kason hannun jari a ƙungiyar Manchester United Sir Jim Ratcliffe ya dakatar da batun ɗaukar ɗan wasan gaban Poland Robert Lewandowski mai shekara 37, wanda kwantiraginsa a Barcelona zai ƙare a a bazara mai zuwa. (Mirror)

Manchester United ba ta shirin tsawaita kwantiragin Casemiro a halin yanzu, kuma ɗan wasan na Brazil mai shekara 33 zai iya tafiya a ƙarshen kakar wasa ta bana. (Football Insider)