Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan da suka ƙara haddasa tsadar man fetur a Najeriya
Da alamu matsalar tsadar man fetur da ƙarancinsa ta fara kunno kai a wasu biranen Najeriya, inda rahotanni suka ce farashin ya kai N1,000 kowacce lita a wasu gidajen mai.
A wannan makon 'ƴan Najeriya suka koma sayen litar man fetur kan N950 a gidajen man NNPCL a Abuja da kuma gidajen mai na MRS da ke sayar da fetur daga Matatar Dangote.
A wasu biranen Najeriya musamman na yankin arewaci ana sayar da litar man fetur N955 har zuwa N1,000.
Wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar mai a Najeriya, sun danganta hakan ne da karin farashin danyen mai, da kuma lalacewar hanyoyin jigilar man daga Legas zuwa sassan kasar.
Shugaban kungiyar dillalan mai ta IPMAN na Suleja da yankin Abuja, Alhaji Yahaya Alhasan ya ce tashin farashin ɗanyen mai ne ya haddasa tsadar man fetur a Najeriya.
"An samu ƙarin saboda Matatar mai ta Dangote da kamfanin NNPC duka sun yi ƙarin farashin lodin man fetur," in ji shi.
Ya ƙara da cewa matsalar hanya ce a Legas ta haifar da karancin man a wasu yankunan Najeriya inda aka fara ganin layi a gidajen mai.
A ranar Alhamis, farashin ɗanyen mai ya sauka da sama da kashi ɗaya, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya amince su gana da Hungary domin tattauna yadda za a kawo ƙarshen yakin Ukraine.
A kwanakin baya, Matatar Dangote ta yi wa ƴan Najeriya alƙawalin cewa farashin mai zai sauka saboda tsarin kamfanin na rarraba mai zuwa gidajen mai a kyauta. Sai dai kuma a yanzu tsadar fetur aka gani.
Farashin man fetur a Najeriya a yanzu ya danganta da nisan wuri inda ya bambanta a sassan Najeriya - jihohin da ke yankin kudu maso yammaci suna sayen lita da sauƙi fiye da yankunan da ke arewacin ƙasar.