'Wani hukuncin sai a lahira': Matar da aka kashe wa ƴaƴa a gwamnatin Assad

    • Marubuci, Sebastian Usher
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC's Middle East analyst
    • Aiko rahoto daga, Damascus, Syria
  • Lokacin karatu: Minti 5

Sabuwar gwamnati a Syria ta yi alƙawarin yin adalci ga wadanda aka zalunta a lokacin mulkin gwamnatin Bashar al-Assad da aka hamɓarar. Sai dai wannan ba ƙaramin aiki ba ne, kasancewar akwai mutane da dama da ke neman a bi masu hakkinsu daga abubuwan da suka faru a tsawon lokacin da aka kwashe ana yaƙin basasar ƙasar.

Wakilin BBC, Sebastian Usher ya gana da wasu mazauna birnin Damascus, waɗanda ke kallon adalcin sabuwar gwamnatin zai taka muhimmiyar rawa wajen tantance makomar Syria.

A garin Douma, ɗaya daga cikin garuruwa da ke wajen birnin Damascus wanda yaƙi ya ɗaiɗaita, a kusa da wani ɗaki, Umm Mazen na zaune tana tuna shekara 12 da ta ɗauka tana neman ƴaƴanta biyu, waɗanda aka kama a shekarun farko na yaƙin basasar Syria, inda daga nan ba ta sake jin ɗuriyarsu ba.

Ta samu takardar cewa babban ɗanta ya mutu, amma babu wani labari kan ɗanta na biyu mai suna Abu Hadi.

Ɗanta na uku kuwa wanda ake kira Ahmed, ya shafe shekara uku yana tsare, ciki har da watanni takwas a cikin gidan yarin Saydnaya da ake tsare da fursunonin siyasa da kuma gana musu azaba.

Har hakori aka cire masa sakamakon gallazawa a gidan yarin, ya tuna wani lokaci da ya yi imanin cewa ya jiyo muryar ɗan uwansa Mazen na amsa kiran sunaye da ake yi a cikin gidan yarin, amma ba su ga juna ba.

Wani adalci Umm Mazen ke nema saboda tarwatsa mata iyali?

"Wani hukuncin sai a lahira," in ji ta.

"Na ga wasu mazauna nan garin suna kawo wani mai goyon bayan masu riƙe da makamai domin kashe shi.

"Na faɗa musu cewa: 'Kada ku kashe shi. Maimakon haka, ku azabtar da shi kamar yadda ya azabtar da matasan mu'."

"Ƴaƴana biyu sun mutu - ko in ce watakila sun mutu, sai dai akwai dubban wasu matasa da aka yi ta azabtarwa.

"Ina rokon Allah cewa Bashar al-Assad ya kasance a cikin ɗaki mai duhu a karkashin ƙasa, kuma Rasha ba za ta iya taimaka masa ba kamar yadda ta saba yi.

"Ina rokon Allah da ya saka shi a wani wuri a karkashin ƙasa - ya kuma sa ya kasa sanin abin da ke faruwa a kusa da shi - kamar yadda ya bar matasan mu cikin gidajen yarinsa."

Lauya Hussein Issa ya nema wa gomman mutane adalci waɗanda aka zarga da aikata laifuka a karkashin gwamnatin Assad.

Ya sha matsin lamba daga wajen hukumomi saboda gwagwarmayarsa, sai dai ya yi ƙoƙari wajen ceto wasu mutane daga azabar da suke sha a Syria.

Amma ga waɗanda aka tura kotuna na musamman na masu manyan laifuka, babu abin da za a iya yi.

Dokar da kula da masu aikata manyan laifuka ta tsananta a Syria yayin da aka ci gaba da gwabzawa a ƴakin basasar ƙasar.

Yanzu, lauyan mai shekara 54 da ke zaune cikin ofishinsa a birnin Damascus, ya ce ya kamata a sallami yawancin alkalai waɗanda suka haɗa kai wajen aikata laifuka a lokacin gwamnatin Assad, sannan a kuma ɗauki matakin shari'a a kansu.

Sai dai ya ce wasu daga cikinsu da suka yi zamani a mulkin Assada, suna da rawar takawa a sabon tsarin shari'ar ƙasar.

Ga ƙoƙarin bin diddigi da kuma ganin an yi wa waɗanda aka musgunawa na tsawon shekara 50 adalci, Mista Issa ya ce kirkiro da tsarin shari'a a kan haka, shi ne abu mafi muhimmanci da ya kamata sabon gwamnati a Syria ta mayar da hankali a kai.

"Idan wannan tsari ba shi da kyau, makomar Syria zai kasance mafi muni.

"Ba mu san wani irin muni abin zai yi ba. Muna cikin fargabar cewa wasu ɓangarori za su iya haddasa rikici.

"Idan muna da gwamnati da kuma tsari mai karfi, to ba za mu yi fargaba kan waɗannan abubuwa ba.

"Idan ba mu da su, dole mu yi fargaba. Sai dai, tun da ina da tsammani mai kyau, ina tunanin cewa sabuwar gwamnatin za ta zama mai kyau."

An rufe ginin da ma'aikatar shari'a ke ciki a babban birnin Syria makonni da dama bayan faɗuwar gwamnatin Assad.

Yanzu, wasu ƙungiyar lauyoyi sun taru a cikin ginin gabanin sake buɗe kotuna.

A cikin ofishinta da ke hawa na biyar, mataimakiyar ministar shari'a, Khitam Haddad, ta ce za a sake fara sauraron ƙanana da kuma manyan laifuka, sai dai ba za a iya duba laifukan da aka aikata ba karkashin gwamnatin da ta shuɗe a yanzu.

A ofishinta mai cike da takardu, ta ce tana aiki a matsayin mai shari'a tun 2013.

An naɗa ta mataimakiyar ministar shari'a a 2023. A yanzu, tana kan matsayin.

"Ina jin kamar ina da alhaki a batun," in ji ta.

"Ya zama wajibi a ci gaba da aiki, alkalai su koma bakin aiki sannan kotun su sake buɗewa, saboda a matsayina na ƴar Syria ina son aikina ya cigaba kuma ina son nasara ta ɗore, domin mutane su daina jin fargaba.

"Ina son in miƙa sakonnin tabbatarwa, ba wai magana kaɗai ba."

Sai dai wasu lauyoyi sun fara nuna damuwa kan yunkurin gwamnatin riƙo na ƙasar na kirkiro da wata hukuma da za ta sa ido kan ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar ba tare da jefa kuri'a kan batun ba.

A wani korafi, sun ce matakin ba zai haifar da ɗa mai ido ba.

Zuwa yanzu, dokoki da kuma tsarin shari'a da ake da su lokacin mulkin Assad suna ci gaba da aiki, ciki har da dokar kula da masu aikata manyan laifuka.

Za a ɗauki tsawon lokaci kafin a gurfanar da waɗanda suka aikata laifi karkashin gwamnatin da aka hamɓarar.

Sabuwar gwamnatin ta faɗa wa ƴan Syria cewa kada su ɗauki hukunci a hannunsu, yayin da hotunan bidiyo da suka karaɗe shafukan sada zumunta suka nuna yadda aka yi ɗauki hukunci kan wasu tsoffin jami'ai.

An yi ta kai samame da kuma kame - sannan wasu daga cikin waɗanda suka tsere daga kan iyaka zuwa Lebanon ko Iraqi sun koma.

Amma akwai babbar ayar tambaya kan cewa ko tsarin shari'ar - wanda ya daɗe yana gallazawa mutane - ko za a iya sauya shi ya zama kan daidai.

A can saman wani tsauni a birnin Damascus, wasu matasa da tsofaffi na can suna shakar iskar ƴanci zuwa yanzu - a iska mai cike da sanyi na lokacin hunturu - a wuri kuma da jami'an tsaro suka haramta musu shiga na sama da shekara goma.

Mutane sun cika wuraren cin abinci da kuma shaguna a makonni tun bayan hamɓarar da Assad, suna ta kallon yadda birnin su yake - inda suke tunanin irin mawuyacin halin da aka shiga da kuma makomarsu, inda adalci da kuma bayyana gaskiya zai taka rawa matuka.