Yadda rayuka ke salwanta a rikicin manoma da makiyaya a Taraba

Lokacin karatu: Minti 2

Al'ummar garuruwan Mungalalau da Mungadosa duk a karamar hukumar Karim Lamido da ke jihar Taraba a arewa maso gabashin Najeriya, sun ce suna cikin zaman dar dar tun bayan rikicin da ya barke a yankin tsakanin manoma da makiyaya.

Yanzu haka dai ana ci gaba da zaman makoki bayan hallaka mutum sama da 40 sakamakon rikicin da ya faru a ƙarshen mako.

Rikicin ya kuma tilastawa daruruwan mutane barin muhallansu domin tsira da ransu.

Wani mazaunin garin Mungalalau, ya shaida wa BBC cewa, fiye rabin mutanen garin sun tsere saboda fargabar abin da zai iya biyo baya.

Ya ce, "A yanzu mazauna wadannan garuruwa na cikin yanayi na tashin hankali don ba a bacci da yawa daga cikin mutanen garinmu sun gudu zuwa garin Karim, wato ainihin hedikwatar karamar hukumar um dominsu tsira da ranzu."

Mutumin ya ce, "Mutane na guduwa ne saboda jami'na tsaron da ke wadannan garuruwa ba su da yawa shi y asa mutane garin ke ganin kamar ba za su iya kare rayukansu ba don haka suke barin garin."

Ya kara da cewa ainihin abin da ya janyo rikicin shine akan gona.

Shima wani mutum da ke gudun hijira saboda rikicin ya shaida wa BBC cewa bayan faruwar rikicin yanzu a Mungadoso ana zaman dar dar, don da yawan mutane gari sun koma makarantar firamaren garin da zama.

Ya ce," A inda muke zaune a yanzu mun kai mu 1,700, ga babu wajen kwanciya ba abinci yunwa duk ta ishemu."

Kazalika wani mazaunin dayadaga cikin yankunan ma ya shaida wa BBC cewa sun rasa abubuwa da yawa saboda wannan rikici.

Ya ce," Mu babban abin da yafi damunmu shi ne mu samu zaman lafiya domin kullum hankalinmu a tashe ya ke, a don haka muna kira ga mahukunta da a kara yawan jami'na tsaron da ke wannan yankin."

To sai dai kuma rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba ta tabbatar da faruwar lamarin amma kuma ta ce mutum 30 aka kashe kodayake ana ci gaba da neman gawarwaki, kamar yadda mai magana da yawun yansandan jihar, Asp James Lashen Saminu ya shaida wa BBC.

Ya ce, yanzu an kara yawan jami'an tsaro a wadannan yankunan, don haka al'ummar yankin su kwantar da hankalinsu.

Shi ma gwamnan jihar ta Taraba Agbu Kefas, ya yi alawadai da faruwar lamarin tare da shan alwashin daukar matakin da ya dace.