Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hindu - Yarinya ƴar Falasɗin da ake tababar makomarta a yakin Gaza
Muryar da ke daya bangaren wayar ta kasance karama, wata karamar yarinya ce ke ta kokawa a wayar da ke hannunta a Gaza.
"Tankar na matsowa kusa da ni. Ta na tahowa".
Zaune a kusa da cibiyar kiran bayar da agajin gaggawa na hukumar bayar da agaji ta Red Cross a Gaza, Rana ta yi kokarin karfafa wa yarinyar gwiwa da ta yi kasa da muryarta.
'Ta zo kusa sosai'
Sosai fa! Sosai fa, karamar muryar ta bayar da amsa. "Za ku zo ku ceto da ni daga nan? ina jin tsoro matuka".
Babu wani abu da Rana za ta iya yi illa ci gaba da magana da ita.
Hind Rajab mai shekaru 6 ta sami kanta a tsakiyar musayar wuta a birnin Gaza, inda take neman a kawo mata dauki, yayin da ta buya a cikin motar kawunta da gawarwakin danginta a kewaye da ita.
Muryar Rana ita ce kadai ke sa ta tunawa da akwai sauran mutane a duniya.
Hind ta bar gidasu da ke Gaza ne da safiyar ranar, da kawunta da 'yan’uwanta su biyar.
Ranar ta kasance Litinin 29, ga watan Janairu. A wannan safiya sojojin Isra'ila sun sanar da mutane da su bar yammaci Gaza zuwa Kudanci da yankin titin Coast.
Mahaifiyar Wissam, ta iya tuna cewar an yi ta harba bamabamai babu kakautawa a yankin. "Mun yi matukar kaduwa, wanda hakan ya sa muka yi yunkurin mu tseratar da rayuwarmu, in ji ta. "muna kaura daga wuri zuwa wani, don kauce wa hare-haren da ake kaiwa ta sama.
Iyalin sun yanke shawarar zuwa asibitin Ahli zuwa gabashinn birnin, da fatan nan zai fi kwanciyar hankali har su sami matsuguni.
Wissam da babban danta sun fara wannan tafiya ne a kafa, Hind ta tafi a cikin motar kawunta, kirar Kia Piccanto.
"An yi sanyi ga shi ana ruwa" Kamar yadda Wissam ta yi bayani. "Sai na ce da Hind ta shiga cikin motar, saboda ba na son ta sha wahala, sakamakon dukan ruwan sama".
Motar na tafiya ne, sai suka ji wata kara mai karfi ta fito daga inda motar ta bi.
Kawun Hind ya tuka motar zuwa fitattaciyar jami'ar Al-Azhar, sai kawai motar ta yi gaba da gaba da tankar sojojin Isra'ila. Suka taka burki sannan suka shiga wani gidan Mai na Fares don tseratar da kansu, amman sai aka ringa kai musu hari.
Wadanda ke cikin motar, sai suka kira 'yan’uwansu don a kawo musu dauki. Daya daga cikinsu ya kira babban ofishin hukumar bayar da agaji ta Red cross a yankin Faladinawa mai nisan Mil 50 (Kilo mita 80) daga yamma da gabar kogin Jordan.
Lokacin ya kasance 14:30 (12:30 GMT): jami'an cibiyar bayar da agajin ta Red Cresent da ke Ramallah ta kira wayar kawun Hind, amma 'yarsa mai shekaru 15 Layan ita ce ta amsa ba shi ba.
A wayar da suka yi wadda aka nada, Layan ta sanar da ma'aikatan hukumar bayar da agajin ta Red Crescent cewar an halaka iyayenta da kannenta, kuma akwai tankar yaki a kusa da motar tasu. "Suna harbin mu", ta ce, kafin su gama magana sai aka ji harbin bindiga, da ihu.
Da Red Cresent suka sake kiran su, Hind ce ta amsa wayar, tana magana kasa-kasa wadda ba ma a iya jin ta, sannan tana cikin kaduwa da tsananin tsoro.
A nan aka fahimci cewar ita kadai ce take da sauran numfashi a cikin motar, kuma har yanu ana ci gaba da harbi zuwa inda ta ke.
"Ki buya a karkashin kujerun motar", jami'an suka fada mata. "Kar ki bari kowa ya gan ki".
jami'in da ke aiki, Rana Faqih ya tsaya a kan layi tsawon awanni tare da Hind a kan waya, yayin da Red Cresent ta yi ta rokon Sojojin Isra'ila da su kyale motar asibiti ta shiga yankin.
"Ta yi matukar kaduwa, cikin damuwa, sannan tana neman a kawo mata dauki, "Rana ya tuna yadda lamarin ya faru. "Ta sanar da mu cewar danginta duk sun mutu. Daga bisani sai ta ce da mu bacci suke yi. Sai muka sanar da ita cewar ta 'kyale su su ci gaba da baccin, ba ma son mu dame su."
Hind ta yi ta tambayar, wa zai zo ya ceto ta.
"A wata gaba, sai ta sanar da ni cewar an fara duhu, "Rana ya sanar da BBC. "Tana jin tsoro. Ta tambaye ni nisan da ke tsakaninta da gidana. Sai na sandare, tare da jin takaici rashin iya tabuka komai.
Bayan shafe sa'o'i uku da fara kiran wayar, daga karshe an tashi motar daukar mara lafiya, don ceto Hind.
A hannu guda kuma sai jami'in Red Cresent ya tuntubi mahaifiyar Hind Wissam, sannan aka hada kiran da layin wayar Hind.
Ta yi kuka sosai a lokacin da ta ji muryar mahaifiyarta, a cewar Rana.
"Ta yi ta roko na da kar na ajiye wayar, " Wissam ta sanar da BBC. "Na tambaye ta ko ta samu raunuka, sai na dauke hankalinta da karatun Alkur'ani, sannan muka yi addu'a. tana maimaita dukkan wata kalma da na fada."
Dare ya yi a lokacin da jami'an kula da motar daukar marasa lafiyar Yousef da Ahmad suka sanar da jami'an Red Cresent din cewar suna gab da wajen, kuma suna neman izinin shiga wajen daga dakarun Isra'ila.
Wannan ne lokaci na karshe da suka ji daga abokan aikin nasu da kuma Hind, sakamakon katsewar da dukka layukan wayar suka yi.
Kakan Hind Bahaa Hamada ya sanar da BBC cewar layin wayar yarinyar da mahaifiyarta ya jima na wani lokaci, kuma abu na karshe da Wissam ta ji shi ne karar an bude kofar motar, sannan ta ce tana iya ganin motar daukar marasa lafiyar daga nesa.
"Ko wacce dakika, ina jin kuna a zuciyata," Wissam ta fada wa BBC. "Duk lokacin da na ji sautin motar daukar marasa lafiya, 'sai in dauka ita ce'. Dukkan wani sauti ko karar harbin bindiga da na ji, ko faduwar makami mai linzami, kowani bam, sai in ta taradadin Allah ya sa ba a kan 'yata ya fada ba.
Ba ga jami'an Red Cresent ba, ba kuma ga dangin Hind ba, babu wanda ya iya kaiwa ga inda ta ke, da ke tsakiyar inda ake musayar wuta, sannan yake a karkashin ikon Sojojin Isra'ila.
"Abu ne mai wuya a cikin dare, "Rana ya fada, "idan ka tashi daga bacci, ka na jin muryarta ta na cewar 'ku zo ku dauke ni.'"
Mun tambayi Sojojin Isra'ila cikakken bayani kan yadda suka kai hare-haren su na ranar, da kuma bacewar Hind da motar daukar marasa lafiyar da ta je dauko ta. mun sake tambayar su bayan awa 24, sun ce da mu suna kan bincikawa.
"Ina kotun hukunta manya laifuka ta duniya? Me shugabanin ta suke ci gaba da zama a kan kujerar?" Mahaifiyar Hind Wissam ta tambaya.
Mako guda bayan bacewar 'yar tata, a kullum Wissam na zaman jiran 'yarta a asibitin Ahli, da fatan za a kawo mata Hind a raye.
"Na taho da kayanta, ina jiran ta a nan,” in ji ta. "ina jiran 'yata a kowane lokaci, kowane dakika. Ina kira da zuciyar uwa mai rauni da ba za ta manta da wannan labarin ba."