Me ya sa farashin gas ya yi tashin gwauron zabi?

...

Asalin hoton, Tolu Owoeye/Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Ƴan Najeriya na ci gaba da kokawa kan tashin farashin iskar gas da ake amfani da ita wajen girki, wanda ya yi tsadar da ba a taɓa gani ba a baya.

A halin yanzu, a birnin Legas ana sayar da kilogram ɗaya tsakanin naira 2,500 zuwa 3,000, abin da ya sa farashin silinda mai nauyin kilogram 12.5 ya haura sama da naira 25,000.

Wannan hauhawar farashin ta janyo ƙalubale ga al'umma, musamman ma talakawa da ke fama da matsin tattalin arziƙi.

A wasu ɗakunan ajiya na iskar gas a yankin yammacin ƙasar, ana sayar da kowace lita a tsakanin naira 2,000 zuwa 2,200, wanda ke nuni da cewa farashin ya ninka fiye da sau biyu cikin watanni kaɗan.

A babban birnin tarayya Abuja, farashin gas ya karu daga naira 1,000 zuwa naira 1,800 a wasu wurare, yayin da wasu dillalai ke sayarwa a naira 1,700.

Wannan hauhawar ta sa wasu daga cikin mazauna birnin sun fara rage yawan amfani da gas ko kuma sun koma amfani da itace da gawayi don dafa abinci.

A jihar Ogun da ke kudu maso yammacin Najeriya, ana sayar da lita ɗaya na iskar gas a kan naira 2,200.

Masu amfani da gas a jihar sun koka da cewa tsadar ta fi ƙarfin mafi yawan jama'a, musamman masu ƙaramin karfi, inda wasu ke cewa yanzu sai sun biya fiye da rabin albashinsu wajen siyan gas kawai.

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rahoton BBC ya gano cewa a wasu sassan Legas, an fara samun ƙarancin iskar gas ɗin yayin da wasu dillalai suka fara ɓoye kayansu saboda tsoron rashin samun riba ko ƙarin farashi daga masana'antun iskar gas.

Wannan ya sa mutane da dama ke yawo daga wuri zuwa wuri suna neman inda za su samu gas.

Wani dillali mai suna Mista Chika Umodu ya bayyana cewa yana da iskar gas amma ba zai iya wadatar da duk abokan cinikinsa ba saboda ƙarancinsa.

"Idan wani ya buƙaci kilo 10, sai mu ba shi kilo 4 kawai domin gas ɗin ya isa ga kowa. Ina da abokan cinikayya dayawa da nake yi wa hidima, saboda haka dole ne na yi la'akari da su," in ji shi.

Wani dillali da bai so a ambaci sunansa ba ya ce tsawon kwanaki biyar da suka gabata bai samu iskar gas ba. Ya ce wanda yake da shi yanzu ne kawai ya isa yau, shiyasa mutane da yawa suka ruga zuwa a shagonsa domin su saya in ji shi.

Ya bayyana cewa yajin aikin ma'aikatan man fetur ne ya jawo haka. Farashin iskar gas ta CNG da ake amfani da ita a motoci ma ya tashi daga Naira 230 zuwa Naira 380 a kowace lita.

Ba a tabbatar da ainihin abin da ya jawo ƙarancin da tashin farashin ba tukuna, amma mutane da dama na danganta shi da yajin aikin da ma'aikatan man suka yi a makon da ya gabata wanda ya sa suka dakatar da aiki na wasu kwanaki.

'Ƙirƙirarre abu ne'

...

Asalin hoton, Gift Andrew/BBC

Shugaban kamfanin NNPCL na ƙasa, Mista Bayo Ojulari, ya bayyana wa manema labarai yayin da yake ganawa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu cewa tashin farashin iskar gas ya samo asali ne daga yajin aikin da Ƙungiyar Ma'aikatan Man Fetur da Gas ta Najeriya (PENGASSAN) ta gudanar.

Duk da cewa ya yi ziyarar ne domin gabatar da rahoton ci gaban da aka samu musamman a fannin samar da mai da yake kula da shi, Ojulari ya kuma yi tsokaci kan halin da farashin iskar gas yake ciki a Najeriya.

Ya ce, "Tashin farashin iskar gas ɗin ƙirƙirarriya ce, saboda yajin aikin da PENGASSAN ta gudanar. Wannan ya sa lodi na gas ya samu jinkiri na tsawon kwana biyu zuwa uku. Saboda haka dole a ga tasirin hakan, amma muna fatan nan da ɗan lokaci, farashin gas ɗin zai kom yadda yake a da."

Shugaban NNPC ɗin ya ƙara da cewa wasu daga cikin masu rike da iskar gas sun ajiye kayansu suna jiran lokacin da za su iya ƙara farashi saboda ba a samun gas sosai lokacin da aka yi yajin aikin PENGASSAN.