Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Real Madrid ta lashe Copa del Rey na 20 jimilla
Real Madrid ta dauki Copa del Rey na 20, bayan da ta doke Osasuna 2-1 ranar Asabar.
Wasan karshe na 40 da Real ta buga a gasar. kuma karon farko da ta dauki kofin tun bayan shekara tara da ta wuce lokacin da ta yi nasara a kan Barcelona.
Minti biyu da fara wasa ne, Rodrygo ya ci kwallo daga baya Osasuna ta farke ta hannun Lucas Torro, bayan da suka koma zagaye na biyu.
Real ta ci na biyu ta hannun Rodrygo, saura minti 20 a tashi fafatawar, shine aka zaba dan kwallon da yafi taka rawar gani a karawar.
Rodrygo ya ci kwallon da wuri a Copa del Rey, rabon da yin wannan bajintar a gasar tun 2006 - kaka daya tsakani da Osasuna ta yi ta biyu, bayan da Real Betis ta lashe kofin.
Osasuna, wadda ba ta taba daukar babban kofi a gasar tamaula ta Sifaniya ba, ta yi iya kokarin ganin ta dauki kofin nan, wadda karo biyu ta je fafatawar karshe.
Kofi na uku da Real Madrid ta dauka a bana kenan, bayan European Super Cup da kuma Fifa Club World Cup.
Ancelotti ya ajiye Luka Modric a benci, bayan da ya warke daga jinya, yayin da kociyan Osasuna, Jagoba Arrasate ya saka Jon Moncayola domin ya hana Vinicius Junior sakat.
Duk da hakan dan kwallon Brazil ya motsa da yawa ya kuma kai hare-hare ya kuma raba kwallaye yadda ya kamata a fafatawar.
Barcelona ce kan gaba a yawan lashe Copa del Rey mai 31, sai Athletic Bilbao mai 23, sannan Real Madrid mai guda 19 da kuma mai 10, Atletico Madrid.
Real Madrid mai rike da La Liga na bara tana ta uku a teburin kakar bana da maki 68, Barcelona ke jan ragama da maki 82, sai Atletico ta biyu mai maki 69.
Ranar 9 ga watan Mayu, Real Madrid za ta karbi bakuncin Manchester City a wasan farko a daf da karshe a Champions League a Santiago Bernabeu.
Real Madrid ce mai rike da kofin zakarun Turai na kakar bara kuma na 14 da take da shi jimilla.