Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne ke sa mata masu ciki ciye-ciyen abubuwan da ba abinci ba?
Matsalar ƙwaɗayin cin wasu abubuwan da ba abinci ba ne da ake kira (PICA) a likitance, an fi samunta a tsakanin mata masu juna biyu da kuma ƙananan yara.
Masana a fannin kiwon lafiya sun alaƙanta matsalar da ƙarancin sinadarin Iron a jiki.
Dr. Dorcas Chiroma, likita ce a fannin mata da ke aiki da asibitin koyarwa na gwamnatin Najeriya da ke jihar Gombe, ta ce yawancin masu cikin da ke da wannan matsala na cin abubuwan da basu da amfani ga jiki.
"Abun da ke janyo PICA yawanci shi ne ƙarancin Iron a jini, wanda zai kai ga ƙarancin jini gaba ɗaya (amosanin jini). Saboda da sinadari ake amfani wajen sarrara jini a jikin mutum. "
Ta ƙara da cewa duk wasu sinadarai da jariri ke buƙata a lokacin da yake ciki, yana samunsu ne ta hanyar jinin mahaifiyarsa.
"Shi sinadarin Iron yana da muhimmanci ga mai ciki, domin mutane biyu ne. Ita tana buƙatar gina jiki, abun da take ɗauke da shi ma haka. Wannan iron ɗin ne ke taimaka wa ta samu isasshen jinin da take buƙata. Don haka ga mai ciki buƙatar sinadarin na ƙaruwa. " A cewar Dokta Dorcas
Ta kuma yi ƙarin bayani da cewa "Mai juna biyu na iya neman wasu abubuwan da ke da amfani ga jikinta, wanda sai ta ji tana son cin wani abu kuma lokacin da ta samu ba lallai ta ci ba sai ta ji tafi son wani abun. Duk wannan ya shafi yanayi ne na ciki da kuma wasu sunadarai da ke ƙwaƙalwar mace da ake kira Hormones. "
Mata sun fi samun wannan yanayi a watanni uku na farkon samun ciki. Ko da yake akan samu wasu da su ke zarta wannan lokaci, in ji ta.
Likitar ta ce ƙarancin Iron ga mai ciki na iya shafar jaririn da zata haifa. Domin idan ta fuskanci ƙarancin jini ya kan shafi halittar jariri.
Shafin intanet na health direct, mallakar gwamnatin Australia ya bayyana cewa a je asibiti idan larura cin abubuwan da ba abinci ba ya wuce wata guda.
Masu wannan matsala na cin abubuwa da dama da suka haɗa da ƙasa, laka, takarda, ƙanƙara, ƙarfe da kuma fenti. A cewar shafin.
Inda shafin ya ƙara da cewa masu matsalar PICA a mafi yawancin lokuta na jin sha'awar cin abu guda ɗaya ne.
Duk da cewa a kan samu wasu da ke sha'awar cin fiye da abu ɗaya.
Sai dai a cewar shafin cin irin wadannan abubuwan da ba abinci ba, na janyo wasu matsalolin kiwon lafiya kamar cushewar hanji da wasu matsaloli da suka shafi ciki, ko lalata haƙori ko kuma shaƙewa saboda haɗiyar wani abu.
Ga misali cin ƙasa kan sa a ci guba, wanda zai iya kaiwa ga samun ƙwayoyin cuta.
Kuma idan yaro ko babba ya ci guba wasu daga cikin alamomin hakan su ne ciwon ciki da amai, numfashi da ƙyar, ko tafiyar ruwa, da samun ƙuraje a fata da jin raɗaɗi a leɓe ko harshe ko kuma a maƙogwaro.
Sai dai shafin ya ce babu wata hanya guda ta magance matsalar, amma ya danganta da abin da ke janyo sha'awar cin abubuwan da ba abincin ba.
Sannan ga waɗanda ƙarancin wani sinadari ne ya janyo shi ga misali, ƙarancin Iron, to likita zai iya bayar da abin da zai taimaka wajen cike giɓin sinadarin ko kuma a sanar da mace irin abincin da ya kamata ta dinga ci don cike giɓin sinadarin.