Yadda ɓarayi suka sace kambin sarakunan Faransa

Asalin hoton, Getty Images
An rufe gidan tarihi na Louvre Museum da ke birnin Paris na ƙasar Faransa biyo bayan fashi da rana tsaka da aka.
Ministar al'ada ta Faransa, Rachida Dati ta rubuta a shafinta na X cewa fashin ya faru ne ranar Lahadi da safe a daidai lokacin da gidan tarihin yake a buɗe.
Ta faɗi cewa tana wurin a lokacin da ƴansanda ke bincike.
Sai dai kuma daga baya ta ce an samu kayan ƙawar da aka sace a kusa da wurin da aka yi wa fashin, kenan waɗanda suka sace ne suka ajiye.
Da take bayanin ƴan fashin, Dati ta ce ɓarayin sun gudanar da abin bisa ƙwarewa ba tare da tashin hankali ba. Babu rahoton rasa rai.
Gidan tarihin ya sanar da cewa zai tsaya da aiki a ranar saboda wasu dalilai.
Louvre ne gidan tarihin da aka fi ziyarta a duniya kuma yana ɗauke da zayyana da kayan tarihi na duniya masu yawan gaske.
Me ya faru?

Asalin hoton, Mohammed Badra/EPA/Shutterstock
Wakilin sashen BBC na birnin Paris, Hugh Scoffield ya rawaito cewa wasu mutane ne da suka rufe fuskokinsu suka shiga gidan tarihin jim kaɗan bayan buɗe shi da safe.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ma'aikatar cikin gida ta Faransa ta ce da misalin ƙarfe 9:30 da rabi, wasu mutane masu dama suka shiga ɗakin Apollo Gallery ta tagar da suka fasa. Shi wannan ɗakin wanda ke kallon wani ruwa na ɗauke da ragowar kayan ƙawa na sarautar Faransa.
Ministar ma'aikatar, Laurent Nunez ta ce ɓarayi uku zuwa huɗu sun yi amfani da tsani mai taya a kan wata mota ƙirar a-kori-kura a kusa da ginin.
Bayan shigarsu ɗakin ne sai ɓarayin suka sace kayan ƙawa daga akwatunan da suke ciki sannan suka tsere suka bar wurin a kan babura. Nunez ta ce fashin ya ɗauki mintuna bakwai ne kacal.
Masu bincike na tattara bayanan abubuwan da aka sace.
Ma'aikatar cikin gidan ta Faransa ta ce kayan ƙawar da aka sace ɗin na da tarihi da ƙima a al'ada baya ga irin darajarsu dangane da abin da ya shafi kuɗi.
Wakilin BBC, Andrew Harding wanda yake kusa da gidan tarihin na Louvre ya ce ƴansandan Faransa sun toshe dukkannin hanyoyin da ke haɗuwa da gidan tarihin da suka haɗa da titin da ke bakin gaɓar kogin da ke kusa da gidan tarihin.
Binciken ya mayar da hankali ne ga ɓangaren kudu maso gabashin ginin wanda yake kallon wurin da aka yi satar.
Daga nesa ana iya ganin tsanin da ake iya matsar da shi irin wanda ake gani a kan motar ƴan kwana-kwana ko saman motocin kamfani.
Ana amfani da irin tsanin a Paris wajen kai kayan gado da kujeru ga gidaje masu benaye.
Saman tsanin na tarar da barandar ɗakin gaban bene, abin da ya sa ake tunanin ta yadda ɓarayin suka samu damar isa ga gine-ginen da ke saman gidan tarihin.
Akwai ƴan yawon buɗe ido da dama a wurin da suka kasa zuwa Louvre a ranar.

Asalin hoton, Reuters
Ɗakin na Gallery of Apollo, wanda ɓarayin suka hara na ɗauke da abin da ya rage na tarihi na kambin sarautar Faransa.
Suna daga cikin abin da ya yi saura na kayan tarihin da aka ko dai siyar ko kuma aka sace bayan juyin-juya halin ƙasar Faransa.
Daga cikin kayan akwai waɗanda aka samu bayan juyin-juya halin ga Sarki Napoleone, da ɗan ɗan'uwansa, Napoleon III da kuma matan sarakunan Marie-Louise da Eugenie.
Shafin intanet na gidan tarihin ya ce kayan mafiya daraja da ke ɗakin sun haɗa da lu'ulu'u guda uku da ake kira Regent da Sancy da kuma Horttensia.
Gidan tarihi mafi girma a duniya

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Gidan tarihin na Louvre shi ne mafi girma a duniya wanda ke da dandalin da ke cikin mutum 73,000 a lokutan baje koli.
An gina gidan ne a 1546 a matsayin fadar sarautar faransa. Sarki Francis I, wanda shi ne ya fara zama a cikinta, ne mai son zane-zane kuma ya kudurci aniyar yin amfani da Louvre wajen baje kolin abubuwansa na tarihi.
Sauran sarakunan ƙasar Faransa sun faɗaɗa kayan tarihin na Sarauta inda sarki Louis XIV ya mallaki kayan tarihin Sarkin Ingila, Charles I bayan kashe shi a yaƙin basasar Ingila.
Kayan sun kasance a ɓoye har zuwa lokacin da aka fara juyin-juya halin Faransa a 1789, inda kuma a 1793 gidan tarihin na Louvre ya buɗe ƙofofinsa ga al'umma a matsayin gidan baje kolin tarihin.
A yanzu haka, gidan tarihin na Louvre yana ɗauke da kayan tarihi fiye da 35,000 da suka haɗa da fitaccen zanan "Monna Lisa" da Leonardo da Vinci.
Masu yawon buɗe 30,000 ke kai ziyara gidan tarihin na Louvre a kullum.

Asalin hoton, Mohammed Badra/EPA/Shutterstock
Yawan sace-sace daga Louvre

Asalin hoton, Getty Images
Sace-sace daga Louvre ba abu ne da ke faruwa kodayaushe ba saboda irin tsaron da gidan yake da shi to amma akwai lokutan da aka sace-sacen a baya musamman wadda aka yi a 1911 lokacin da aka sace zanen da Leonardo da Vinci ya yi mai suna Monna Lisa.
Sai dai an samo zanen bayan shekaru uku a Florence kuma an mayar da shi birnin Paris. A lokacin zane-zane ba su da ƙima irin ta yanzu.
Haka kuma a 1983 ma wasu kayayyaki wata garkuwa tun ta ƙarni 16 sun ɓatan dabo inda ba a gan su ba har sai 2011.
A baya-bayan kuma wani zanen ƙarni na 19 wanda Camille Corot ya yi da aka ɗauke a 1998. An cire zanen ne mai suna Le Chemin de Sevres daga jikin bangon da yake. Satar zanen ta haifar da garambawul ga jami'an tsaron gidan. Har kawo yanzu ba a samu zanen ba.











