Yadda yaran da ake haihuwa ba tare da takamaiman uba ba ke fuskantar tsangwama

.

Asalin hoton, BBC/Hanna Samosir

Bayanan hoto, 'Yan uwan juna Esti da Aminah da Fatma sun taso a hannun dangin mahaifiyarsu a Indonesia da ke aikin aikatau a Ƙetara
    • Marubuci, Hanna Samosir
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Indonesia
  • Lokacin karatu: Minti 5

Gargadi: Wannan maƙala na tattare da wasu bayanai masu iya tada hankula

Ana kirasu da 'yayan takari ko baƙin-haure".

Iyayensu sun kasance baƙin-haure da ke zuwa ƙetare aiki daga nan su gina alaƙar da ke kai wa ga haihuwan yara, galibin irin waɗannan yara ana samun su a Indonesia babu iyaye kuma suna fuskantar tsangwana a cikin al'ummar da suka taso.

A tarihi irin waɗannan yara na shan wahala matuƙa wajen samun takardu, ma'ana dai ba sa samun damar ilimi da samun kulawar lafiya.

Wannan yanayi da suke tsintar kai na jefa su cikin kangi na talauci, auren wuri da cin zarafinsu.

Dubban "yaran takarin" na rayuwa a yammacn lardin Nusa Tenggara, ɗaya daga cikin ƙasashen da aka fi samun kwararan 'yan ci-rani.

Rayuwa a ƙeɓe

.

Asalin hoton, BBC/Hanna Samosir

Bayanan hoto, Siti Aminah tun tana yarinya take fuskantar tsangwama

Siti Aminah mai shekara 23 na ɗaya daga cikin irin waɗannan "yara na takari". Uwarta ta bar Lombork zuwa Saudiyya aikatau.

A hanyar tafiya ta yi auren wucin-gadi - da ake kira nikah siri - da wani ɗan Pakistan, sannan daga baya ta auri ɗan Saudiyya, kafin daga bisani kuma ta koma Indonesia domin ta haihu.

A Indonesia, "Yaran takari" ana haihuwarsu daga ire-iren wannan aure da ake yinsu bisa tsari na addinin Musulunci, amma ba tare da rajista ba a hukumance.

Maman Aminah ta bar yaranta shida a gabashin Lombok, suna zaune a gidan 'yan uwanta daban-daban.

"Galibin 'yan ci-rani Indonesia irinsu Sahmin na aure da rabuwa da mazajensu, kuma suna yin hakan ne domin su samu abokin zama a inda suke rayuwa," a cewar Endang Susilowati, Jami'a da ke sa ido kan 'yan ci-rani a lardin.

Ta taso a hannun 'yanuwanta babu iyaye, Aminah ta sha fama da wariya,"Ana ce mata ke Balarabiya ce. Kina da Uba fiye da guda," kamar yadda ake goranta mata.

Yayarta, Fatma, tana yawaita tuna kalaman ƙiyayya da ake mata. "Idan mahaifiyarmu ba ta turo kuɗi ba, ana mana tsawa da duka," a cewarta.

..

Asalin hoton, Family archive

Bayanan hoto, Hoton Fatma tana yarinya lokacin da aka bar bata a hannun 'yan uwan mahaifiyarta a gabashin Lombok

BBC ta tuntuɓi mahaifiyarsu Fatma da Amina amma taƙi cewa komai.

Waɗannan 'yan uwan junan na cikin jeren ire-iren yaran nan da iyayensu mata ke tafiya ci-rani kuma suke shan wahala matuƙa saboda rashin asali a cikin al'umma.

Ƙungiyoyi masu zaman kansu a Lombok irinsu cibiyar Rudat na aiki tukuru wajen ganin su ba wa irin waɗannan yara taimako bisa tsari na doka da tabbatar da cewa irin waɗannan yara na samun takardu da zai ba su damar zuwa makaranta da samun kulawar lafiya.

Barazanar auren wuri

Cibiyar Rudat ta ce ƙyamar da irin waɗannan yara ke fuskanta na jefasu cikin haɗari har da na auren wuri.

Indonesia ita ce ƙasa ta hudu a duniya da ake yi wa yara auren wuri kuma yankin yammacin Nusa Tenggara a nan ne abin ya fi kamari.

Ta kasa jure ƙiyayyar da 'yan uwanta ke mata, amma Fatma ta bar makaranta domin kula da kannenta kuma any i mata aure tana da shekara 15.

"Gwara auren. Ko ba komai ka samu mai kula da kai," a cewarta.

.

Asalin hoton, BBC/Hanna Samosir

Bayanan hoto, Fatma ta yi auren farko tana da shekara 15 a duniya

A cewar ƙwararru, auren wuri ba ya karko.

Wannan shi ne abin da ya faru da Fatma, wanda a shekarunta 25 tayi aure uku wand babu rajista, sannan ta haifi yara biyu.

A bisa dokar Musuluncin Indonesia sai mace ta kai shekara 19 za a yi mata aure, kuma auren wuri ana masa kallon ɗaya daga cikin laifukan cin zarafi karkashin dokar cin zarafi da laifuka ta ƙasar.

Waɗanda suka aikata ko suka bada daman auren wuri na iya fuskantar hukunci dauri na shekara tara a gidan yari ko kuma tarar har ta dala 12,340, sai dai amfani da wannan doka na da rauni.

Duk da cewa doka ta bada dama iyaye su nemi izini na musamman idan auren yarinya ta taso, ana aurar da yara kanana da dama ba tare da neman irin wannan izini ba ko rajistar kotu.

Saurin ɗaukan ciki

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Saurin ɗaukan ciki tsakanin waɗannan kananan yara da ake yiwa aure na faruwa cikin hanzari.

Hukumar da ke kula da haihuwa da daidato tsakanin maza da mata a Majalisar Dinkin Duniya, UNFPA ta ce kananan uwaye su suka fi fuskantar barazanar cututtuka irinsu hawan jini, cutar bayan haihuwa da sauransu.

Sannan yaransu na fuskantar barazanar haihuwa tun lokaci bai yi ba, ko jariri mara nauyi, da kuma waɗanda ke mutuwa.

Aminah ta haihuwa tana da shekara 16 ga bakwaini wanda ya mutu bayan watanni.

Bayan mutuwar jaririn, Aminah ta ce bango gidanta ya raushe saboda tsananin azabar da mijinta ke yi mata.

Ba tare da wani karatu ba, Aminah ta kasance ba ta da sauran zaɓi.

A cewar ƙungiyoyi masu zaman kansu saboda tsangwama, mutane da dama ba sa son daukan irin waɗannan "yara na takari' aiki.

Aminah ta zama ma'aikaciyar gini a Jakarta, amma na tsawon wata shida kawai.

A lokacin da take da shekara 19, ta zama ma'aikaciyar ci-rani a Saudiyya ta haramtacciyar hanya.

Ta ce ta fuskanci cin zarafi mara imani a lokacin da take aiki har ta ji kamar ta kashe kanta.

"Ana lakaɗa mun dukan tsiya, ana cin zarafina har sai na ji kamar nayi hauka," a cewarta.

Bayan ta dawo gida sai ta gano cewa duk kuɗaɗen da take aikowa gida an sace su.

"Na dawo gida babu ko sisi tattare da ni," a cewarta.

Cibiyar Rudat ta ce tana yawaita cin karo da irin waɗannan matsaloli.

"Iyalan da ake bai wa amanar ajiyar kuɗi na cikin talauci, saboda aiki na da wahala anan. Akwai mutane da dama marasa aikinyi. Don haka idan an samu kuɗi ko an turo sai su cinye," a cewar Zurhan Afriadi ta cibiyar Rudat.

..

Asalin hoton, BBC/Hanna Samosir

Bayanan hoto, Shekarun Esti 18 kuma ta yi auren sirri da ɗanta guda

'Yanayi mai tsanani'

Duk da hakan, akwai cigaba. Da taimakon tallafin da ake samu daga ƙungiyoyi masu zaman kansu, a shekarar da ta gabata gwamnati ta samar da takardu ga kusan dukkanin irin waɗannan yara a gabashin Lombok, hakan ya basu damar shiga makaranta da samun kulawar lafiya.

Sai dai hakan bai hana tsangwama da wariyar da suke fuskanta ba.

"Tsangwaman na nan, dole sai a hankali za a kawar da shi", a cewar wata ma'aikaciya Turmawazi.

Esti, ita ce karamar kanwarsu, ba ta yi makaranta ba, tana da shekara 14 aka yi mata aure, ta haihu amma daga baya ta rabu da mijinta.

Yayinda take kokarin samawa kanta mafita, ta samu wani aikin karfi da take yi saboda ta samu kuɗin taimakawa kanta da danta.

Cibiyar Rudat ta yi gargaɗi kan karuwar matsalolin, inda ake samun karuwar yaran da takari ke haifa da sake dawo da su cikin wahalar da suka ɗana a baya.

Aminah da Fatma da Esti na son ganin abubuwa sun sauya.

Aminah ta dogara da kuɗaɗen da mijinta ɗan ci-rani ke samu wajen rainin ɗanta. Esti ta zaɓi cigaba da zama a inda take, kwatakwata ba ta da ra'ayin tafiya ci-rani, burinta shi ne ta raya ɗanta. Fatma, ta sake aure ga wani mutum da ke taimaka mata, kuma tana maganganu alkhairai a kansa.

"Abin kunya ne ga yara iri na, waɗanda za su cigaba da tsintar kansu cikin wannan yanayi mai tsanani," a cewarta.