Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Nawa ne albashin shugaban ƙasar Amurka?
Mutane kan yi tunanin cewa shugaban ƙasar Amurka na samun maƙudan kuɗaɗe a matsayin albashi da alawus-alawus.
Babu kuskure a wannan tunanin saboda shugaban Amurka jagora ne na ɗaya daga cikin ƙasashe mafiya girma, kuma mafiya ƙarfin iko a duniya.
Amma fa ba haka abin yake ba kwatakwata.
Dalili shi ne an tsara duk shugaban da ke mulkin Amurka zai zama ma'aikacin gwamnati ne, akan biya su albashi ne da harajin da sauran 'yan ƙasa ke biya.
Shugaba Joe Biden da ke mulki a yanzu na karɓar dala 400,000 a shekara.
Amma kuma ba shi ne kuɗin da sabon shugaba mai zuwa - Kamala ko Trump - zai karɓa ba.
Wannan ba abin mamaki ba ne saboda an ɗauki tsawon lokaci ba a sauya albashin shugaban ƙasa ba.
Idan Kamala Harris ta yi nasara, bayanai sun nuna cewa za a ƙara mata dala 235,100 kan albashinta na mataimakiyar shugaban ƙasa.
Shekara huɗu da ya yi a kan mulki, Donald Trump bai karɓi albashin shugaban ƙasa ba. Maimakon haka, ya dinga karkatar da shi zuwa wasu ma'aikatun gwamnati duk wata uku.
A cewar sakataren kula da ayyukan gwamnati, Trump ya ba da umarnin zuba kuɗin a fannin kula da harkokin lafiya da yaƙi da annobar cutar korona a 2020.
Albashi da kasafin kuɗi na shugaban ƙasar Amurka
Adadin albashi na tsakatsaki a shekara - $400,000
Sauran kasafi kamar sutura - $50,000
Kuɗin kula da baƙi - $19,000
Akan yi amfani da kuɗaɗen wajen kula da jami'ai, da ma'aikatan fadar White House - kamar masu kula da lambun fadar.
Haka nan, akan kula da lafiyar shugaban ƙasa a kyauta, zirga-zirgarsa ma kyauta a abin hawa na gwamnati, da kuma jirgi.
Sannan kuma yakan samu dala 100,000 duk shekara, wadda ba a cire wa haraji.
Lokutan da aka sauya albashin shugaban ƙasa
Tun daga 1789, lokacin da George Washington ya fara zama shugaban ƙasa, sau shida kawai aka taɓa sauya albashin da ake bai wa shugaban ƙasar Amurka.
A baya, shugaban ƙasa kan karɓi dala 25,000 duk wata. Amma da za a ƙiyasta darajar kuɗin a yanzu za su kai dala 895,700.
Dalilin da ya sa ake bai wa shugaban ƙasa alawus-alawus shi ne don a hana su yin almubazzaranci da dukiyar al'umma.
Shekarar 2001 ce lokaci na ƙrshe da aka sauya albashin shugaban ƙasar, inda 'yanmalisar wakilai suka ninka shi daga $200,000 zuwa $400,000.
- 1789: $25,000
- 1873: $50,000
- 1909: $75,000
- 1949: $100,000
- 1969: $200,000
- 2001: $400,000
Idan muka yi la'akari da albashin kaɗai, kuɗin da shugaban ƙasa ke samu bai kai na manyan ma'aikatan da suka fi kowa albashi ke samu ba a Amurka.
Sai dai kuma zai ci gaba karɓar kusan $244,000 duk shekara bayan ya sauka daga mulki.
Haka nan za a ci gaba da ba shi jami'an tsaro, da kula da lafiyarsa kyauta, da kuma kai shi duk inda yake so a kyauta.