Yadda za a fafata a zagayen kwata fayinal na Champions League

Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal za ta kara da Real Madrid, Aston Villa kuma ta ɓarje gumi da Paris St-Germain a zagayen kwata fayinal na gasar zakarun Turai ta Champions League.

Madrid ta kai zagayen ne bayan doke Atletico Madrid a bugun finareti, bayan wasa ya tashi 2-2 gida da waje, yayin da Arsenal ta yagalgala PSV 9-3 gida da waje.

Villa kuwa ta doke Club Brugge 3-0 a ranar Laraba, 6-1 kenan gida da waje.

Paris St-Germain ta kai zagayen bayan fitar da Liverpool a bugun finareti sakamakon wasan ya tashi 1-1 gida da waje a ranar Talata.

Sauran wasannin su ne wanda Inter Milan za ta kara da Bayern Munich, sai kuma Borussia Dortmund ta fafata da Barcelona.

Barcelona ta doke Benfica 4-1 gida da waje

Bayern Munich ta doke Bayer Leverkusen 5-0 gida da waje

Inter Milan beat Feyenoord 4-1 gida da waje

Paris St-Germain ta doke Liverpool gida da waje 1-1 a bugun finareti

Borussia Dortmund ta doke Lille 3-2 gida da waje

Aston Villa ta doke Club Brugge 6-1 gida da waje

Real Madrid ta doke Atletico Madrid 2-2 gida da waje - a bugun finareti

Arsenal ta doke PSV 9-3 gida da waje

Yaushe za a buga kwata fayinal da semi fayinal?

Za a fara buga wasannin farko na zagayen kwata fayinal a ranakun 8 da 9 ga watan Afrilu, sai kuma wasa na biyu sati ɗaya bayan haka.

Sai kuma semi fayinal da za a buga ranar 29 da 30 ga watan na Afrilu, a yi wasa na biyu ranar 6 da 7 ga watan Mayu.

Yaushe ne kuma a ina za a buga wasan ƙarshe?

Za a buga wasan ƙarshe ranar 31 ga watan Mayu a filin wasa na Allianz Arena - wato gidan ƙungiyar Bayern Munich.