Chelsea na ta kokarin ɗaukar Omorodion daga Atletico

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea na kokarin ɗaukar ɗan wasan tawagar Sifaniya, Samu Omorodion daga Atletico Madrid.
Ƙungiyar ta Sifaniya ta amince da biyan fam miliyan 81.5 don sayen ɗan wasan Manchester City, Julian Alvarez ranar Litinin, kuma sayar da Omorodion zai taimaka mata wajen biyan kuɗin ɗan kasar Argentina.
An fahimci cewa tuni an ƙulla yarjejeniya da Alvarez, wanda zai koma Sifaniya da taka leda kan £64.4m da ƙarin £ 17.1m na tsarabe-tsarabe.
A wata yarjejeniya ta dabam ɗan wasan Chelsea, Conor Gallagher ya amince ya koma Atletico mai buga La Liga kan fan miliyan 33 kan fara kakar bana.
Omorodion, mai shekara 20, ya koma Atletico a bara, wanda ya fara buga La Liga a Granada, har ma ya zura ƙwallo a ragar Madrid.
Nan take Atletico ta bayar da aron Omorodion zuwa Alaves, shi kuma ya zura kwallo takwas a wasa 35 da ya buga a bara.
A yanzu haka yana gasar Olympics da ake yi a birnin Paris, kuma ya zura kwallo daya a ragar, inda Sifaniya ta kai karawar karshe.
Kafin fara kakar nan Chelsea ta kashe kusan fam miliyan 115 wajen sayen 'yan wasa da suka hada da Kiernan Dewsbury-Hall da Renato Veiga da Omari Kellyman da mai tsaron raga, Filip Jorgensen da Tosin Adarabioyo da Caleb Wiley da Estevao Willian da kuma Marc Guiu.
Tuni kuma Chelsea ta sayar da Ian Maatsen da Lewis Hall da Omari Hutchinson, yayin da Hakim Ziyech da Malang Sarr da Thiago Silva suka bar ƙungiyar, bayan da yarjejeniyarsu ta kare, inda Gallagher ke daf da komawa Spain.
Har yanzu ba a san makomar Romelu Lukaku ba, bayan da ɗan wasan tawagar Belgium ya yi wasannin aro kaka biyu a gasar Italiya.











