Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Daga Bakin Mai Ita tare da Safiya Adamu
A wannan karo cikin filinmu na Daga Bakin Mai Ita mun tattauna da ɗaya daga cikin dattijai mata na masana'antar fim ta Kannywood, wato Safiya Adamu, wadda aka fi sani da Safiya Kishiya.
Ta bai wa matasa da ke neman shiga harkar fim shawara domin guje wa yin da na sani.