Jam'iyyar Conservatives ta sha kaye a zaben cike gurbi

Jam'iyyar adawa ce ta Liberal Democrat ce ta yi nasara a zaben cike gurbin

Asalin hoton, PA Media

Jam'iyyar Conservatives mai mulkin Burtaniya ta sha mummunan kaye a zabuka biyu na cike gurbi da aka gudanar a kasar domin maye gurabe wasu 'yan majalisa da suka ajiye aiki. Babbar jam'iyyar adawa ta Labour ce ta yi nasara a gundumar Wakefield da ke arewacin kasar ta Ingila yayin da Liberal Democrats ta yi nasara mai cike da tarihi a gundurmar Tiverton.

Daukacin 'yan takara biyu da suka yi nasara sun ce hakan alama ce ta cewar masu kada kuri'a na juya baya ga mulkin rashin gaskiya da kwamacala irin na firaminista Boris Johnson.

Zababben dan majalisar na jam'iyyar Liberal Democrat Richard Foord, ya ce Idan ba a dauki matakin dawo da mutunci da martabar fada ta Downing Street ba, to kuwa za a rinka shan kaye a zabe kamar yadda ka sha a wannan karon. Kuma Mr Johnson ba shi ne ya cancanci ya jagoranci Birtaniya ba.

Wadannan kaye da Boris Johnson ya sha babban abin damuwa ne ga jam'iyyarsa ta Conservatives.

Sun nuna cewa jam'iyyar na rasa magoya baya daga cikin magoya bayanta na ga ni kashe ni da yankunan karkara na kudanci da kuma ma'aikata a arewacin kasar wadanda a baya suka koma goya wa jam'iyyar baya domin mara wa aniyarta ta ficewa daga tarayyar Turai.

Duk da cewa dama akan yi amfani da zabukan cike gurbi domin nuna adawa da wasu manufofin jam'iyya mai mulki, to amma wadannan zabuka sun nuna cewa a dai wannan yanayi da ake ciki to kuwa a matsayinsa na firaminista, Boris Johnson ba ya da goyon bayan al'umma.

Za a iya cewa a yanzu ya tsira da mukaminsa kasancewar ya tsallake kuri'ar rashin nuna kwarin guiwa da mulkinsa da aka kada, to amma dole jam'iyyarsa ta shiga damuwa saboda irin wannan kaye da take sha.