Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dakarun da Rasha ta jibge na iya afka wa Ukraine idan aka tanka musu - Amurka
Babban hafsan sojin Amurka Janar Mark Milley ya ce girke dakarun da rasha ta yi a kan iyakarta da Ukraine shine mafi girma tun bayan yakin cacar baka.
Janar Milley wanda shi ne shugaban hafsan hafsoshin sojojin Amurkar ya ce sojojin da Rashar ta jibge na iya haifar da mummunar hasarar rayuka da zarar an ce musu cas !.
Tun da farko dai rahotanni sun ce shugaban Rasha Vladimir Putin ya shaida wa takwaransa na Faransa Emmanuel Macron cewa ba shi da wani shiri na kai farmaki.
Sai dai ya ce Amurka da kungiyar tsaro ta NATO sun gaza magance manyan bukatunsa na dakatar da fadada kawancen da kuma kaucewa jibge makamai a kusa da Rasha.
Mece ce ƙungiyar Nato?
Nato - Kungiyar tsaro ce me hadakar sojojin kasashen yankin Arewacin Atalantika, wadda kasashe 12 da suka hada da Amurka da Kanada da Birtaniya da Faransa suka kirkiro a 1949.
Kasashen sun yi alkawarin kai wa duk daya daga cikinsu da ke fuskantar wata barazanar tsaro taimako.
Da farko manufarta ita ce ta kalubalanci duk wani yunkuri na mamaya ko fadadar da Rasha za ta nemi yi bayan yaki a Turai.
A 1955 Rasha ta lokacin Tarayyar Soviet ta mayar da martani ga kirkirar ta Nato, inda ita ma ta kirkiro hadakar soji ta kasashen kwaminishanci na Gabashin Turai, kawancen da ta sanya wa suna Warsaw Pact.
Sakamakon rushewar Tarayyar Soviet a 1991, wasu daga cikin kasashen da ke cikin kawancen na Rasha ( Warsaw Pact), sai suka koma kungiyar Nato inda ta zama da mambobi 30 yanzu.