Jamhuriyar Nijar: Ƴan bindiga sun sake kashe sojojin ƙasar 10 kwana guda bayan kashe aƙalla 70

Niger

Asalin hoton, AFP

Wasu 'yan bindiga dauke da muggan makamai sun halaka sojojin Jamhuriyar Nijar 10, yayin wani hari da suka kai wani sansanin soji.

Ana fargbar cewa karin wasu sojojin tara sun yi batan dabo yayin harin da yan bindigar da ake zargin masu ikirarin jihadi ne suka kai kauyen Anzourou.

Ma'aikatar Jamhuriyyar Nijar ta ce maharan sun isa ne a kan motoci da babura, kana suka bude wa sojojin da ke tsaron jama'ar garin wuta.

Wannan na faruwa ne yayin da ake zaman makokin akalla sojojin kasar 70 da masu ikirarin jihadi suka kashe a iyakar kasar da Mali da Burkina Faso.

Soja

Asalin hoton, Getty Images

Ranar Juma'ar da ta wuce ne Jamhuriyyar Nijar ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu daga yau Juma'a bayan da wasu da ake zargi masu ikirarin jihadi ne sun kashe kimanin mutum 70.

Harin ya faru ne a kudu maso yammacin ƙasar ta kan iyakar Nijar ɗin da Mali.

Cikin waɗanda harin ya rutsa da su har da wani magajin gari da kuma shugaban wata rundunar sa kai, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta bayyana.

Babu wata ƙungiya da ta fito ta ɗauki nauyin kai harin. Waɗanda suka kai harin sun tsere ta iyakar ƙasar da Mali inda rahotanni suka ce sun ɗauke gawargwakin ƴan uwansu da aka kashe.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta Jamhuriyyar Nijar ɗin ta kuma ce an yi wa wani ayari ƙarƙashin jagorancin Magajin Garin Banibangou kwantar ɓauna a wani ƙauye da ke da nisan kilomita 55 daga wurin da lamarin ya faru a Yammacin Tillaberi.