Matsalar Tsaro: Matakai bakwai da gwamnatin Kaduna ta dauka kan 'yan bindiga

Asalin hoton, KDSG
Gwamnatin Kaduna ta dau sabbin matakai masu tsauri domin murkushe 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane don karban kudin fansa.
Wata sanarwa da kwamishinan harkokin cikin gida ya fitar, Samuel Aruwa ta shaida cewa daga yau Alhamis 30 ga watan Satumba dokokin za su soma aiki.
Sanarwar ta ce gwamnatin Kaduna ta dau wadannan mataki ne la'akari da matsalolin tsaro da ke sake kamari a jihar da kuma 'yan bindiga da ke sake kutsa kai kauyukan jihar daga jihohi makwabta.
Gwamna Nasir El-Rufai ya ce kafin daukar matakan sai da ya tattauna da masu ruwa da tsaki a fanonin tsaro.
Sannan ya shaida cewa daukar wadannan matakai sun zama tilas domin taimakawa jami'an tsaro murkushe 'yan bindiga.
Tuni dai al'ummomin jihar Kaduna suka fara tofa albarkacin bakinsu game da matakan.
Ga jeren matakan da gwamnaya dauka
1. An haramta hawa babura ga kowa da kuma yin achaba, na tsawon wata uku.
2. An haramta mallaka ko gyaran makamai masu hadari.
3. An hana amfani da babura mai kafa uku daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe. Kuma dole su yaye mayafi ko labulen da ake sa wa a cikin baburan.
4. Dole a yi wa motocin haya fenti launin ruwan dorawa da baƙi a cikin kwanaki 30 mazu zuwa. Sannan motocin haya na musamman irinsu 'uber' dole su sanya fenti da ke nuna alamar motar haya.
5. An haramta sayer da man fetur a jarkoki ko mazubi a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kachia da Kagarko da Kajuru.
Sauran matakan da aka dauka a baya za su ci gaba da aiki. Sun hada da:
a. Haramci kan sare itatuwa da gadun daji a Birnin Gwari da Giwa Igabi da Chikun da Kachia da Kagarko da Kajuru.
b. An haramta fataucin itatuwa da gawayi.
c. Haramci shigowa ko fitar da dabobbi a jihar.
d. Haramta cin kasuwar mako-mako a kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da Chikun da Igabi da Kajuru da kasuwar mako ta Kawo da ke karamar hukumar arewacin Kaduna.

Karin haske
Gwamnatin Kaduna ta ce tana sane cewa ba lallai wadannan matakai su yiwa mutane dadi ba amma ya zama wajibi domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar.
Gwamnatin ta kuma nemi goyon-bayan al-ummarta da hadin-kai daga mazauna yankunan da wadannan dokoki suka shafa don ganin an dakile masu tada zaune tsaye.
Sanarwar ta ce wadannan matakai ne za su taimakawa jami'an tsaro wajen kakkabe 'yan bindiga da ke kashe-kashe da sace-sace domin neman kudin fansa.
Rashin tsaro a yankunan Kuduna ya yi sanadi rayukan mutane da dama da raba wasu da matsugunansu. Haka zalika ana sake samun karuwar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.











